BABBAN GORO
NA
KHADEEJA CANDY
_Ga barka da Sallah na baku, ni kuma ku aje min nama zanzo na karɓa😊_
*30*
“Miyasa baki faɗa min kina sonshi ba? Miyasa kika bari na aureshi bayan kinsan ke yake so?”
Sune tambayoyin da Minal ta riƙa yima Kairat tana hawaye,
Itama hawayen take sai motsi take ta baki, kamar mai son yin magana ta kasa,
Girgiza ta Minal ta shigayi da ƙarfi tana kuka.“Ki bani amsa mana Kairat miyasa kika sadaukarda soyayyarki ga wace farin cikinta kaɗan ne?
Miyasa kika bari na auri Saif bayan kinsan ba nice mace da yake so ba kinsan ban dace da rayuwarsa?
Miyasa zaki cutar da kanki kuma nima ki cutar da akan abunda zaki iya juyashi ya zame miki farin ciki?”Kuka Kairat take yi sosai kukan da bazata iya furta mata koda ‘A’ ba balle ta amsa mata tambayoyinta.
Ganin hakan yasa Minal ta saketa tayi baya-baya har ta jingina da bango, ta sulale ƙasa tana matsar gashin kanta,“Allah na tuba idan wani abun na maka Ya Ubangijina na tuba ka yafe ni, Allah karka kama ni da laifin da bansan na aikata ba Allah karka ɗora min abunda bazan iya ɗauka ba”
A hankali taji an shafa tsakiyar gashin kanta zuwa bayan ta sannan aka duƙo dai-dai tsawonta an sa hannu a anshafi gefen fuskarta,
Wani sanyi taji ya ratsata, ta lumshe ido tana ƙara saita fuskarta ga Mummy,“Ko wane Bawa da irin jarrabawar da ake jarrabarsa da ita Minal, kowa da adadin Allah ya ɗibar masa na rayuwarsa da jidaɗinsa da farinciki da kuma mutuwarsa,
Ba'a taɓa dauwama a abu ɗaya Minal jindaɗi bai taɓa ɗaurewa ba,
Dole ne ka mutu ka barshi ko kuma shi ya ƙare ya barka, kamar haka ne wahala bata ɗaurewa, dukan abunda yake fararre toh ƙararrene wannan abun, Ɗan Adam baya taɓa samun abunda yake so 100%,
Allah yana jarraba bayinsa badan baya sonsu ba sai dan ya gwada imaninsu da irin juriyarsu, wani yana can yana neman irin rayuwarki bai samu ba, yana neman farinciki koda ma wadda bai kai naki ba bai samu ba,
Kiyi haƙuri Minal ki kasance kicin bayin da haƙuri yake zame musu riba, kiyi haƙuri dan Allah kar lokaci yazo wanda haƙurin zai zame miki dole kuma a lokacin baki da lada, kiyi haƙuri Ƴata kici jarrabawa ki yarda da ƙaddara baki san abunda mahaliccinki ya tanadar miki ba”Kai ta girgiza ma Mummy alamar gamsuwa ta rumgumeta suna kuka,
Kairat ma tana tsaye a gun da take tana nata kukan, aka sara mai ba wani haƙuri.
Sun daɗe a haka sannan Mummy ta rika ta suka tashi tsaye tare ta nufi hanyar ɗakin.
Wanka mummy tasa tayi sannan ta kwanta taja bargo ta lulluɓe, zaune mummy tayi kusa da ita tana kallonta har bachi ya ɗauke ta,*** *** ***
Bata farka sai bayan la'asar, tana tashi ta sake yin wanka tayi sallah, sannan ta nufo downstairs, Babu kowa falon sai tv dake ta aikinsa, windon falon ta nufa tayi tsaye tana kallon Parking space, wani yanayi take ji mai wuyar fassara, bata jin kuka a yanzu sai dai na zuci ta take, fuskarta tayi wani fari kamar marar jini, lumshe ido tayi ta sauke ajiyar zuciya.
“Minal...-”
Buɗe ido tayi ta juyo tana kallon Kairat ba tare da ta amsa ba,
Karasowa tayi kusa da ita idonta cike da hawaye tace“Kina jin haushi na ko?”
Ko dai bata ɗaga mata ba balle tayi mata magana sai kallon fuskarta take,
![](https://img.wattpad.com/cover/114548868-288-k951883.jpg)
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...