Ya daɗe a harabar asibitin kamin ya nufo gida,
Ko da ya shigo sha-ɗaya saura kwata, ganin kofar Parlour a buɗe ya tabbatar masa da Huda bata gidan,
Kai tsaye ɗakin sa ya wuce, ringing ɗin wayarsa ne ya amsa masa sallamar da bai yi dan karar wayar ce ta tarbe shi, kamin ya karasa ya ɗauka kiran ya yanke, ɗaukar wayar yayi yana dubawa kusan twenty something miss calls ya tarar, Abban Huda ne da Umma ta sai kuma Nasir da wasu two numbers da bai sani ba, tsaki yaja ta wurgar da wayar yasan duk maganar Huda ce zasu masa shi, kuma a yanzu bata gabansa wani haushin ta ma yake ji, yana kokarin cire jallabiyar dake jikinsa aka kara kiran a nan ya ɗauki wayar yasa ta silent, ya ɗaura tawul ya shiga bathroom ya sakar ma jikinsa ruwa.Ya daɗe a banɗakin daga bisani ya fito rayuwarsa a jagule ya rasa inda zai sa kansa yaji sanyi, Shi tun da yayi aure baya iya cewa ga ɗauraren lokacin da ya kasance cikin farin ciki, duk da auren so sukayi da Huda amman kullun cikin samun matsala suke, idan wannsan ta kare wannan ta taso, ya kara da Minal ita kuma aka zo aka mata wannan sherin, shin sai yaushe zai san jindaɗin rayuwar aure ?
Gashin kansa ya shafa a dai-dai lokacin da ya zauna gefen gado,
“Mi yasa irin waɗannan abubuwan suke faruwa da ni ne? Komai na duniya Allah ya ban amman banda wannan oh god!”A fili ya faɗa yana matsar gashin kansa, zuwa can ya tashi ya saka kayan bachi ya kwanta saman gadon a rairan yana kallon sili,
Tunanin Huda yake gani yake kamar ba gaske ba ne baza ta iya yi masa haka ba, a nan take zuciyarsa ta soma karanto masa wasu abubuwan da take ɓoye masa da kuma waɗanda ya gani yake kuma zarginta,“Innalillahi wainna illaihi raji'un”
Wannan shi ake kira da ana zaton wuta a makera sai aka same ta a masaka,
Miyasa bai yi ma Minal uzuri ba? Miyasa bai saurareta ba? Miyasa bai yi bincike akan hakan ba?, Sai a lokacin ya soma tunanin irin kuka da Minal ta rika yi da kuma yanayin fuskarta,“Miyasa kika amsa kin aikata Minal? Bayan baki aika ta ba? Miyasa?”
_Saboda ba zaka yarda ba,_
Wata zuciyar ta bashi amsa,
Da a'ce tun farko kayi mata uzuri ka saurareta ka kuma yi bincike da duk hakan bai faru ba, da yanzu ka gano gaskiya an wuce gurin, yau gashi har tana asibiti da cikin ka cikin da ka daɗe kana nema cikin da family ka suke so cikin da za'a haifa naka magaji ka samu ɗa ka zama mutun kamar kowa amman aka saka maka shakku a akansa ka kasa bashi kulawar da ta dace,“Noooooooo!”
Da wani irin karfi ya faɗa ya kai ma katifar gadon wani mugun bugu, wanda na tabbatar da mutum ne sai ya suma,
Fillo yaja ya rumgume yana kuka,“Oh Minal oh Minal”
Kwakwalwarsa ta cushe tunaninsa ya bushe, wani kara tsana ya ɗorawa kansa da kansa a yanzu, shi kansa yasan bai kyautawa Minal ba sai a yanzu yake ganin laifin kansa. Tashi yayi zaune jin yayi babu wanda yake son gani idan ba Minal ba, A gogon ɗakin ya kallah,
Karfe ɗaya da minti talatin da bakwai ns dare haka a gogon ya nuna, bai damu ba ya tashi ya canja kayan dake jikinsa daga na bachi zuwa kananan kaya, ya ɗauki makullin motarsa ya fice.*** *** ***
Ko shakku babu kai tsaye ya nufo asibitin, duk da yana tsamanin tayi bachi, amman shi dai ko fuskarta ya kalla ya samu sauki dan jin yake yau idan bai sata Minal a ido ba ba zai iya bachi ba.
Abunda bai yi zato ba ya hanga kamin ya karasa bakin kofar Emargency, Deen ne a jingine da kofar ya rumtse ido fuskarsa a takure,
Toh mi yazo yi asibitin? Kar dai ace gurin Minal ya zo?
Ita ce tambayar da Saif ya rika yima kansa har ya isa kusa dashi Fuskarsa a murtuke kamar bakin kumurci,“Mi kazo yi asibitin nan ɗan iska matar mutunci”
Ba shakka wannan muryar Saif ce hakan yasa shi buɗe ido ya kalleshi, kamar bakin hadarin gabas haka yaga fuskar Saif babu annuri yana mashi wani kallo irin zan iya ɗaukar ranka,
CZYTASZ
BABBAN GORO
RomansNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...