Ya daɗe a haka sannan ya buɗe ya ɗago yana share hawaye,. Har lokacin Lubna na tsaye tana kallonsu tada ita yayi tsaye ya rik'a hannunta suka nufi cikin parlour, saman kujera ya zaunar da ita sannan shima ya zauna yana kallonta yana murmushi. Lubna ma zaunawa tayi a kujerar dake fuskantar tasu ta kura musu ido kamar tv.“Ta ci abinci?”
Ya tambaya yana kallon Lubna, Kai ta girgiza masa, yana ganin haka ya tashi da kansa ya nufi dinning ya zubo abincin a plate, ya dawo kusa da ita ya zauna ya rik'a bata a hankali tana ci,
“Lafiya?”
Ya tambayi Lubna ba tare daya kalleta ba ganin yaddata sakar masu ido ko kyaftawa bata yi, tashi tayi tana faɗin
“Bari na kira maka Momy”
“Ban saki ba”
Ya tari numfashinta, a nan ta koma ta zauna still bata daina kallon nasu ba. Sai da ya tabbatar da ta koshi, ya bata ruwa ta sha. Sannan ya tashi ya nufi ɗakinta Momy.
Goma saura kwata Saif ya shigo gida, kana ganin yanayinsa kasan baya cikin walwalah, kai tsaye ɗakinsa yana tunani, sam bai lurada Kairat dake falo ba har sai da tayi masa magana
“Sannu da zuwa”
Da sauri ya juyo, sai a lokacin ya lura da ita, a maimakon ya amsa sai kawai ya zagayo ya zauna kusa da ita yana murmushi ya kai hannu ya taɓa sakar wuyan ta
“Wannan kwaliyar fa”
“Uhm”
Kawai tace ta ɗauke kai ta tashi, da kallon Saif ya bita har ta shige ɗakinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya shiga ɗakinsa, wanka yayi ya shirya ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya fara da gajeren wando ya fesa body spray, ya hau saman gado ya kwanta yana shafa cikinsa. Babu wanda yake tunani a yanzu sai Minal maganar ta da akayi ɗazun ya dawo masa da tunanin ta a ɗayan ɓangaren kuma ga maganar da Momy tayi masa wai shine silar shigar Safiyyah wannan halin.
Kairat ce ta faɗo masa a rai cikin hanzari ya tashi ya nufi ɗakinta, tana kwance taji an turo kofar ɗakin, Lil Minal na gabanta ta zuba mata ido sai kallon ta take. zuciyarta ta nasalta mata Saif ne ya shigo ga kuma kanshim turarensa da fara kai ma hancinta ziyara tun kamin gayar ya iso, har ya mai da kofar ya rufe bata motsa a daga inda take ba tana jin ya kusa karasowa kusa da ita ta lumshe ido kamar mai bachi. Leka ta ya fara yi yana idonta a rufe, sai ya zauna gefen gadon yana kare mata kallo kamin ya kai hannu ya mirgino ta ta juyo gefensa ya rungume ta tsamtsam a kirjinsa“I'm so sorry Momy ce ta kira ni shiyasa ban dawo ba, kuma hankalina ya ɗauku ban je na ɗauko ku ba”
Har yayi surutansa ya gama bata motsa ba balle ma tayi masa magana, ganin bata da niyar maganar yasa ya tashe ta zaune ya ɗora bakinsa daidai kunneta ya soma mata magana kamar mai raɗa
“Haba yar gidan Mummy kiyi hakuri mana nasan nayi laifi amman a yafe min dan Allah”
Sai a lokacin ta buɗe idon ta, ta kalleshi
“Amman kuma shine baka dawo ba sai yanzu”
Fuskarta ya rik'a yana rufe ido da buɗewa yace
“Kin san Safiyyah ba lafiya shine na.........”
Sai kuma yayi shiru kamar wanda ya tuna abu, basar da maganar tayi sai ta kalli cikin kwayar idonsa
“Ka ci abinci?”
“A'a tun abincin Safe”
“Miyasa.?”
Bai bata amsa ba, ita ma kuma bata kara tambaya ba sai kawai ta sauka saman gadon ta rika hannunsa for the first time
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...