BABI NA ARBA IN DA D'AYA

3.3K 338 21
                                    


Faɗuwa Mummy tayi zaune tana wani irin numfashin tana kallon tiles, da sauri likita ya nufe shi da Kairat, Kairat ta dafa ta,

"Mummy Mummy"

A nan ta ɗago ta kalli Kairat idonta a raunene kamar mai jin tsoro, ta jata jiki na rawa ta rumgume

"Minal my child....."

Fashewa Kairat tayi da kuka hakan yasa Mummy tayi saurin sakin ta, ta matsa can ta dafe kai ta rumse ido,
Ta ɗan daɗe kamin ta buɗe idon ta kalli kofar ɗakin da Minal take ciki, a nan ta tashi tsaye ta nufin tafiya sai kafafun ta suka kasa ɗaukarta ta faɗi, da sauri likitan ya rika ta yana kiran wasu nurses,
Unkurin ta sake yi a karo na biyu da nufin sake tashi a nan ma faɗuwan tayi dan jikinta yayi ma kafafunta nauyi basa iya ɗaukar ta,
A nan ta soma jin wani kalar abu na daban, zuciyarta tayi mata nauyi kanta ya sara sai ta rika jin kamar mafarki take kalmar Dr ta rika dawo mata _Duk mai rai mamaci ne_ sai a lokacin idonta ya cika da hawaye alamun rashin ya fara fisgarta, kamin ka ce kwabo sai gata tana kuka mai haɗe da dariya,

"You know what? Minal she's always asking me Mummy idan bana nan ya zaki ji! Minal ina ma zaki zo yanzu kiji yadda nake ji...."

Kairat ta matso kusa da ita ta kama hannunta tana kuka mai tsuma zuciya,

"Mummy kiyi hakuri haka Allah yaso"

Fashewa Mummy tayi da kuka

"Mutuwa baki kyauta min ba, Minal ita kaɗai ce farin ciki na ita ce family na ita kaɗai na mallaka a duniyar nan miyasa zaki ɗauke ta ki bar ni bayan ni nafi dacewa dake haba mutuwa haba mutuwa...."

Rufe mata baki Kairat tayi tana girgiza mata kai,
A nan ta mai dubanta gurin Kairat

"Kin ga Minal ta tafi ta bar ni ko!......"

Shiru tayi tana kallon tafin hannunta, zuwa can ta sake kallon Kairat tace

"But never mind i will take good care of her clothed and her room so that I can be with her again I will always....... "

Sai kuma tayi shiru tana kallon yatsun hannunta hawaye masu zafi na mata zuba,

"She's will come back to me very soon"

Ta faďa tana fisgar gyalenta tana kuka.
Yanayin kalamanta da kuma abunda take ya tabbatar ma da likitan tana kokarin barin hankalinta ne, A nan yasa wasu Nurse suka ɗauke ta aka ɗora ta saman kujera suka nufi wani ɗakin da ita sai surutai take...

*** *** ***

Kamar mahaukaci Saif ya shiga ɗakin, ya nufe ta da sauri ya shiga girgiza ta

"Minal Minal Minal Minal wake up!"

Da wani irin karfi yake girgiza fuskarta, zafafan hawayen dake masa zuba na ɗiga a saman kumatun ta, ganin bata motsa ba ya hannunshi ya matse mata baki

"Talk to me Minal Saif ɗin ki ne please Minal please"

Ya faɗa yana taɓa lips ɗinta da wani irin karfi. A nan wata nurse ta nufo shi ta ɗafa tana janshi baya

"Kayi hakuri ta riga ta rasu iya......."

Bata karasa maganar ba ya kai mata wani mugun haushi nan take bakin nata ya fashe da jini, ba shiri ta fasa ihu tayi waje da gudu.
Hannu yasa ya tallafo kan Minal ya rumgume ta tsam-tsam a kirginsa kamar mai rai yana kuka

BABBAN GORODove le storie prendono vita. Scoprilo ora