BABBAN GORO
NA
KHADEEJA CANDY
®
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*33*
Ganin yadda hankalin su duk ya karkata gurinta ya bata damar ci gaba tana kallon Momi,
“Nasan Minal tana son Yaya sosai so zata iya yin komai dan taga da dawo masa, maybe ba ki cin sa bane bamu da tabbatacin haka”
A fusace Nasir ya kalleta,
“Wannan wace irin magana ce haka Safiyyah.... -”
Momi ta tari numfashi sa
“Tana da gaskiya Nasir maganar ta abun dubawa ce”
“Idan ma har haka kuke jima tsoro ai zamu iya jiran har ta haihuwa sai a yi gwajin jini a gani ko, in yaso sai muyi da rainon ciki”
Hakan ma baiyi ma Safiyyah daɗi ba ta kalle Nasir cike da jin haushi,
“Yaya Nasir taya zamu rik'a rainon cikin da bamu da tabbatacin namu ne ko ba namu ba, cikin shege.... -”
Tasssss Saif ya wanke mata fuska da mari, jin ta anbace cikin da shege shi kanshi ba shi da tabbatacin nashi ne ko ba nashi bane amman zuciyar shi na bashi wani abun daban, kwakwalwalshi a yanzu rikece take daman ya daɗe da rasa natsuwar dake tare dashi,
Tsawa Momi ta katsa masa,
“Saif miye haka daga faɗan gaskiya maganar ta fa abun dubawa ce”
Tashi yayi rashin a ɓace yana faɗin
“Momi i need to think”
Ya fice, Nasir ma tashi yayi ya fice, cike da jindaɗin mari da Saif yayi ma Safiyyah,
“Duk abunda za'a faɗa masa ba yarda zai yi ba saboda kamar ba banza suka barshi ba”Safiyyah ta faɗa tana shafa gurin da ya mare ta ɗin, Lubna ta girgiza kai,
“A a anty ni gani nake kamar cikin na Yaya ne saboda... -”
“Saboda me ke baki da hankali ne Lubna yarinyar nan shi fa da kansa ya kamata da wani taya zamu tabbatar cikinsa ba wannan sam ba cikin Saif bane”
Safiyyah ta faɗa a fusace, ta tashi ta nufi ɗakinta
“Allah ya kyauta”
Momi ta faɗa tana janye tagumin dake fuskarta, Lubna ta amsa da ‘Amin’
*** *** ***Jingine da Mota Nasir ya tararda Saif ya kifa kai idonshi a rufe kamar marar lafiya,
Dafashi Nasir yayi cike da tausayawa,“Saif ka daina damun kanka da yawa you are too young for that bai kamata a'ce kana samun matsalan iyali a yanzu ba”
Juyowa yayi yana sauke ajiyar zuciya ya kalli Nasir
“Nasir na rasa meke faruwa da ni al a murran nan suna kokarin rikata ni”
“Saif kar maganar Safiyyah ta shiga kanka ni gaskiya ban yarda Minal ta aikata abunda kake zaton ta dashi ba wannan cikin naka ne Saif”
Fuskarsa ya shafa
“Nasir da ace ba ni na gani da kai na da zan iya yarda kazafi akayi mata, kuma da ace ba Deen bane nan ma zan iya mata uzuri amman kasan yadda take son Deen”
Nasir ya tattara girarsa,
“Ka yarda kenan ba kicin ka ba ne? Baka kusan ceta ba ko?”
Wata bazawarar dariya yayi yana gyara tsayuwarsa yace
![](https://img.wattpad.com/cover/114548868-288-k951883.jpg)
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...