BABBAN GORO...!
NA
KHADEEJA CANDY
WATTPAD @khadeeja_candy
BABI NA GOMA SHA BAKWAI___17
Shiru Mummy ta ďanyi, sannan tace “Saif Minal tana da cutar sikila da ita aka haife ta shiyasa kullum cikin rashin lafiya take, idan ka lura haka jikinta yake bata kiba kuma abu kaďan ya isa yasa ciwon ta ya tashi.
Saif duk mai cutar Sikila in har sun rayu sun girma basa wuce shekara 25, Shekarun Minal 23 a duniya, Saif bansan ta rai ba amman Minal tausayi take bani gashi ita kaďai na haifa bani da kowa sai ita idan ban barta tayi yadda take so ba sai naga kamar na cutar da ita .zuwa zuwa nasan wata rana za'a wayi gari ba ita....- ”Kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasawa, Lumshe ido Saif yayi cike da tsumayi, can kasa kasa ya sinkayo muyar Dr.Salamatu tana cewa,
“Ba a nan kawai a abun ya tsaya ba Minal tana da blood cancer Kuma kasan blood cancer bazai ta6a fita ba har sai an chanja jini, gurin chanjin jini kuma mutun zai iya rasa ransa dan babu tabbas ko zai rayu.Saif bazanbiya hana minal abunda take so ba koda raina take so ba zan iya hana ta ba matukar yana sata farinciki ina fatar ka fahimce ni”
Bai ce da Mummy komai ba dan baya jin akwai abunda zai iya furta mata a yanzu, tshi yayi tsaye tare da saka hannayensa aljihu, ya nufi kofar fita,
Jinginawa Mummy tayi jikin kujera tana kallon Saif har ya fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayen da suka zubo mata,**********
Har ya isa gida tunanin maganar da Mummy ta faďa masa ta Minal yake, Tabbas Minal abar tausayi ce amman wannan ba zai zama dalilin da xai sa mummy ta rika kyaleta tana yadda take so ba.
“Sannu da zuwa Dear”Cike da fa'ah ta tar6eshi dai-dai lokacin daya kawo baki qafar falo. Da murmushi ya amsa,
“Yauwa sannu wannan kwaliyar fa?”
Fari tayi da ido, ta kar6i makulin motar dake hannunshi
“Kai akayi ma. Muje kayi wanka muci abinci”
Ba musu suka nufi Upstairs tare, har ďakinsa ta rakashi ta taya shi cire kayan jikinsa ya ďaura tawul ya shiga wanka,
Ita kuma ta buďe waduraf ďinsa ta ďauko masa janabiya da guntun wando ta ďora masa saman gado sannan ta fice ta nufi dining tana shirya kwanukan abincin.****** ****** *****
Zaune suke falo, tana kwance saman jikinsa yana wasa da yatsun hannunta. Kallo ɗaya zakayi mashi kasan hankalinshi baya gurin, dan idonsa ma ba akan tv suke ba.
Bugun kofar da akayi ne, ya ďago hankalinsa zuwa gurin kofar. Huda kan yin tayi kamar ba taji ba daman can haka halinta yake indai akan bugun kofa ne. Sai tayi banza da mutun sai yayi ya gaji sannan ta buɗe. irin matan nan ne masu wulakanci da kyaluwa, (Iri Mrs J Mood 😜).Yunkurin tashi yayi da nufin zuwa gurin kofar, da sauri ta rike masa hannu
“Ina zaka.?”
“Ba kiji ana buga kofa ba?”
“Naji mana ka kyale ko wanene har sai munga damar tashi mana”
“A'a idan ba zaki ba ni bari na duba”
“Zauna bari na duba ďin”
Tashi tayi ba dan taso ba, ta nufi kofar. A fusace ta buďe da nufin yima ko wanene masifa, sai kawai taga Budurwa tsaye cikin doguwar rigar atamfa da gyale.
“Sannu”
Kairat tace da ita.
Wani kallo Huda ta watsa mata tun daga saman ta har kasa, bata ga alamun talauci ko makamancin hka a tattare da ita ba, tun daga kan tufafinta Juwa halittar jikinta hakan yasa batayi gaggancin faďa mata wata banzar magana ba. Tun da batasan ko wacece ba sai kawai ta ďauke kai tace.“Wa kike nema.?”
“Saif. yana ciki?”
“Wacece ke.?”
“Sunana Kairat Ibrahim Ahlam”
_Ibrahim Ahlam_ a zuciyarta ta maimaita sunan. tasan waye Ubanta koda bata san wacece ita ba. fitattacen mai kuďi kuma sanannen ďan siyasa mai faďa a ji cikin najeriya,
“Saif nake nema nace yana ciki.?”
Ganin yadda ta tsaya kallonta yasa Kairat, maimaita mata tambayar. Juyowa Huda tayi gurin Saif,
“Dear. kasan Kairat.?”
“Kairat.?”
Da karfi ya zaburo, jin ta ambaci Kairat, ya nufi kofar.
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya kar6a sunan ya kuma nufo kofar jiki na rawa.
Yana isa, ya kara buďe kofar yana faďin,“Kairat shigo mana”
Sai a lokacin ta ďanyi murmushi, ta tako kafarta ta shigo cikin falon, wani 6angare na falon ya nufa da ita, ya nuna mata kujera
“Zauna ina zuwa”
Zaunawa tayi tana karewa hotunan su dake manne kallo. Wani gurin yana rik'e da Huda wani gurin kuma suna manne da juna, har ma da inda yayi mata kiss.
Haka nan sai taji wani irin, duk bata jidaďin ganin hotunnan nasu ba. _Ko miye dalili oho!_
Da kansa ya ďauko mata abun sha da cup, ya dire mata, sannan ya zauna a kujerar dake fuskantar, ta ya sakar mata manyan idanunsa dake kwance da wasu ruwa saboda fari.
Tsif falon yayi Huda na can daga zaune can gefen tana satar kallonsu. Kairat kuma tun lokacin data zuba drins ďin ta maida kanta kasa,
Saif kuma jiran yake ta fara masa magana dan yasan bazai wuce abunda ya faru tsakanin su da Minal ba daman hankalinsa ya kasa kwanciya tun lokacin da ya baro gidan, ganin ya saka Minal da mahaifiyarta kuka.Kairat. Sai da tasha lemun sannan ta kalleshi cike da nauyin ido,
“Saif. Naje gidanku akace nazo nan, na tararda kai tare da iyalanka kayi hakuri da takurawar da nayi maku”
Murmusawa ya ďanyi ya shafi dogon hancinsa,
“Ba komai what is important now you are here”
“Saif. I want to talk to you about what you say to Minal earlier”
Gyara zamansa yayi, ya tattara hankalinsa ya mika mata, yana kallonta cike da natsuwa.
“All my ears Pretty Kaiyrat”
Har cikin jijiyar jinin zuciyar ta taji kiran sunan nata da yayi, wata rahama ce ta rufe mata jiki sai taji kamar babu wadda ya iya kiran sunan nata daďi irinshi.
'''Don't forget to Vote Comment and share.
#KhadijaAbubakarAlkali
#OneheartOnelove'''
ESTÁS LEYENDO
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...