BABBAN GORO.
NA
KHADEEJA CANDY
Candynovels.wordpress.com
WATTPAD @khadeeja_candy
_Masu cewa idan ba zan karasa ba na faďa da masu cewa sai an manta page nake typing da masu cewa yanga nake kuma bana yi da yawa duk kuyi hakuri dani bana da time ne sosai shiyasa, LOVE YOU ALL._
BABI NA ASHIRIN__20
Sai ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ya ďago ta yana faďin,
“Kar fa kiyi bachi nasan halinki Yar baby”
Dariya tayi ta kallesa,
“thanks for your caring”
Murmushi yayi mata,
“It's my pleasure”
Ya sake ďaga kai ya kalli windo sannan ya juya yana faďin,
“Tunda kin hakura bari naje gida ki gaida min da Dr.Salamatu”
“Ai da ka shiga ka gaishe ta”
“A a wannan zuwana naki ne bana kowa ba sai dai wani lokacin Ki gaida min da Kairat”
Dariya ta sake yi cike da jindaďi ta mika hannu ta riko hannunsa,
Bai yi unkurin hana ta ba har ya kai gurin da ya faka motarsa. Sai da taga zai shiga sannan ta sakeshi fuskarta shimfiďe da murmushi.Tsaye tayi tana kallonsa har ya fice sannan ta juyo ta shiga falo cike da nishaďi,
Kai tsaye upstairs, ta nufa hannunta a baki kamar irin yarinya,“Kairat”
Ta kira sunan ta tana kokarin buďe kofar ďakin.
Da sauri Kairat ta share hawayen dake idonta ta kalleta tana murmushi,“Na'am sister”
Kusa da ita ta zauna, tana murza ďan hannunta.
“Yanzu ya tafi ya bani hakuri kuma yace na gaishe ki”
Murmushi tayi ta rika fuskar Minal,
“Yanxu kin hakura ko komai ya wuce?”
“Eh man tunda ya bani hakuri ai na hakura”
“Uhmmm amman ni da Mummy babu yadda ba muyi dake ba kika ki hakura”
“Ai toh ai shine ya 6ata min rai kuma yaban hakuri kinsan shi na daban ne”
Kairat ta haďe yawun dake bakinta, ta sake mata hannaye
“Toh yanxu hankali ya kwanta”
“Yes Sis”
A nan ta tashi tana murmushi ta nufi hanyar ďakinta.
Ajiyar zuciya Kairat ta sauke ta kwantar da kanta saman filo ta lumshe ido, tana numfashi a hankali.Minal tana shiga ďakinta ta faďi zaune saman kujera tana murmushin da ta kasa dainawa tun ďazu,
Kalma ďaya zuwa biyu ta hana mata sukuni. _Ina kinshinki ina bacin ciki wani namiji wadda ba muharraminki ba ya kalli surar jikinki_ me yake nufi ne.? Miyasa yake kishi na ? Mi yasa ya damu dani sosai.? Dubu yadda yazo yake bani hakuri kamar bashi ya 6ata min rai ba,
Dora kafafunta tayi saman hannun kujerar tana lumshe ido.****************
K'ARFE TAKWAS DA RABI......
8:30pm.
Juye juye take tayi saman carpet ranta a jagule jikinta kuma a mace, kamar marar lafiya.
Tashi tayi ta ďauki wayarta ta kunna wakar Rihanna _work work work_ ta saka iyafis ta faďa kife saman gadon ta rumtse ido. Bata samu yadda take so ba, sauran ďan sukunin daya rage mata sai ya kara fita ba shiri ta tashi zaune ta cire iyafes ďin ta kunna kira'ar Shuraim, ta kai bolon đin karshe.
Ahankali take bin suratul Baqara ďin suna karantawa tare. Can ta janyo Laptop, ďinta ta shiga facebook. Notifications ta fara dubawa kamin ta kai gurin massages, sama-sama tayi reply ďin wasu massages wasu kuma ta kyale su, ta koma newsfeed. Posts ta ďinga dubawa wadda ya dace ta dabnawa like ta danna. Daf da zata sauka online ta duba friendsrequest.
Saif Bashir Bature ta gani, first friendsrequest. Da sauri ta duba profile ďinshi, information ďin data gani about him ya tabbatar mata da shi ďinne na gaske, ga kuma pictures ďinsa dake kai, da wasu family members.
Dawowa tayi baya ta danna accept sannan ta cigaba da duba profile ďinsa,Tana Haka massage ya shigo mata,
''' Thanks for accepting my request Kaiyrat'''
Yanayin yadda ya rubuta sunanta nata ya kara tabbatar mata da lallai shi ďinne.
'''Your welcome'''
Ta rubuta masa as reply, tana taunar hakoranta,
Nan take taga Video call. Ya kirata. Tsayawa tayi tana tunani miyasa ya danno mata videocall.? Oh maybe yana son ya tabbatar da idan ita ďince, hakan yasa ta amsa masa kiran.Dimm! gabanta ya faďi saboda kwarjinin, murmushinsa da kuma yadda kyakkayawar fuskarsa ta cika mata screen ďin computer.
“Kece ko gumkinki.?”Ganin yadda ta ke kallonsa ba ko motsi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ďan saki murmushi,
“Nice mana kai ma kai ne ko gunkin ka.?”
Dariya yayi,
“Rama wa kikayi.? Ykike ya gida?”
“Lafiya kalau na gode da zuwan da kayi ka bawa Minal hakuri”
Tsoke fuska yayi ya ďan turo hanci gwanin sha'awa,
“Oh never mind Dear it's my pleasure”
“Thanks too”
Ta faďa tana murmushi. Da tunanin abunda zata ce,dan duk ya ďaure mata jiki da sarka da bazan iya cewa ga kalar ta ba!
Shima idon ya tsura mata yana kallon beautifull face nata, da kuma yadda take kunnar kallonsa, duk sai yaji ta kara burgeshi. Wani zillo zuciyarsa take akansa duk da har yanzu bai gama tabbatar da sonta yake ba,
Saidai kuma jinta yake duk ta make ko ina na ilahirin zuciyarsa, dan ta tara komai da yake so a mace. Suturce jiki, tunani, sanin ya kamata ga kuma uwa uba kunya.“Hy are you still there!”
Ido ya kara sakar mata da murmushin da ke kayar mata da gaba,
“Yes pretty anything for me.?”
Dariya abun ya bata daga ita har shi, basu da wani abun cewa sai magana suke kamar wayanďa aka saka dole,
“Laugh huh? What is funny.?”
“Nothing naga kawai kaki kashe laptop ďin bayan baka da wani abun cewa”
“So glad to know that you’re having fun, especially With me”
“Lol Saif I...-”
Bata karasa maganar ba ta rufe loptop ďin da sauri. Tana kallon Minal data shigo yanzu, tana kallon laptop ďin.
VOTE FOR ME
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...