BABBAN GORO.
NA
KHADEEJA CANDY
Candynovels.wordpress.com
WATTPAD @khadeeja_candy
BABI NA ASHIRIN DA BIYU___22
Cike da ɓacin rai ya isa gida. Mamakin kansa yake wai Namiji kamar shi Kairat zata tsaya tana yimai yadda taga dama, wani gurin kuma laifin kansa yake gani tunda shi ya sake mata fuska har taga damarsa.
Da wannan tunanin ya shiga ɗakinsa, Kwance ya hango Huda ta baje saman gadon tana sharar bachi, matsawa yayi kusa da ita ya kura mata ido hannayensa zube cikin aljihu. Zuwa can ya ɗauke kai ya nufi wadurof ya canja kayan jikinsa zuwa na bachi, bayan ya gama shirinsa na bachi ya kashe wutar ɗakin yazo bayan Huda ya kwanta.* * *
“Mtwssss”
Yaja tsaki, Nasir ya kallesa,
“Wai dan na yi maka sammako kake wannan tsaki.? idan mitin ɗin ne baka son zuwa sai ka na koma na sauke ka”
“No ba haka bane mitin ai ko baka zo ba dole ne naje, kawai wani abun ne yake ɓata min rai”
“Name.? ko san yan jarida sun yaɗaka”
Kallon rashin fahimta Saif yayi masa,
“Sun yaɗani kamar ya wani abun na aikata ne.?”
“Kar dai kace min baka san komai ba!”
“Allah ban sani ba, meke faruwa ne?”
“Aiko kusan jarida nawa ta buga wai kana soyayyah da ya Dr. Salamatu”
Hannu yasa ya dafe kansa, yada soma sara masa yanzu,
“Kai wai yan jaridar nan basu da hankali ne! Su abu kaɗan ya zama na labari Mtwss”
“Wai kana nufin bada gaske bane.?”
“Babu abunda ke tsakanin mu, ni ba sonta nake ba beside ni Qawarta nake so kuma ita ma ta fara bani haushi”
“Baka sonta amman kake kula ta.? Haba Saif nifa ba mutun bane da zaka ɓoye ma sirrinka”
“Allah da gaske nake ni babu abunda ke tsakanin mu, ina kula ta ne kawai dan tana bani tausayi saboda kazantacciyar rayuwar da take, amman ni ba sonta nake”
Murmushi Nasir yayi ya bugu sitarin motarsa,
“Karka ce min baka sonta Saif, baka sonta kake kokarin ɗorata a hanya? Wannan ai kai ba zai ɗauka ba”
Saif ya ɗan fusata,“Ai sai kayi tayi tunda baza yarda ba”
“Ka yarda kana sonta Saif Tausayi silar so da baka sonta da bazaka iya zama da ita ba koda na minti ɗaya ne, and Saif abunda kake kokarin yi ba xai taɓa yiyu ba Kairat bazata taɓa sonka ba koda tana son ka bazata nuna maka ba,
Saboda taraiyarsu da Minal ta zamo kamar yan'uwa, toh faɗa mi taya Kairat zata so abunda Minal take so?”Saif ya kalleshi,
“Ce maka akayi tana sona?”
“Tana sonka Saif kuma kaine ka ɗasa mata son a zuciyata, da bata sonka bazaka mata abu ta kyale ka ba, An faɗa min babu wadda ya isa yasa Minal tayi abunda bata tashi ba amman kai kana sata kuma ta daina,
Kai da bakinka kake faɗa min minal tana shaye-shaye tana zuwa club tana mu'a mala da maza yadda kai hakan baya yi maka daɗi, kasan abunda yasa baka jindaɗi! saboda kana sonta, Kairat ta fita hankali da hali mai kyau hakan yasa taja hankalinka har ka fara sonta, Bari na faɗa maka wani abu da har yanzu ka kasa ganewa Saif, Minal ce kake so ba Kairat ba Kairat halinta kake so Minal kuma zatinta kake so da ace Minal zata canja hali, Halinta ya dawo kamar na Kairat, da bazaka sota ba, Toh kaga Minal ce ainihin mace da kake so”
![](https://img.wattpad.com/cover/114548868-288-k951883.jpg)
ESTÁS LEYENDO
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...