“Wanene wannan Huda..!?”
Ya tambaya cikin tsawa, fuskarsa na nuna ɓacin ransa karara dan har jijiyar wuyansa ta tashi,
Ba jikinta ba har hanjin cikinta zan iya cewa rawa suke, abunka da marar gaskiya sai kawai ta fashe da kuka, Fusata sosai ya karayi cikin ɓacin rai ya zaburo mata da gaggausar murya
“Ba magana nake miki ba ki ban amsa mana karamar yarinya ce ke da zaki tsaya kina min kuka!”
Hantar cikinta ce ta kara kaɗawa yayi mata tsawar da bai taɓa mata irinta ba, da sauri ta share hawayen idonta ta kalleshi da ido kamar zasu fito
“Ban sani ba Saif ban sanshi ba”
Yayi mata wani kallon rainin wayyo
“Baki sanshi ba na samu number shi a wayarki?”
Kukan ne ya sake dawo mata amman wannan karon marar sauti, saukowa tayi saman gadon ta zube kasa kamar mai neman gafara sai murzar hannayenta take tunani take yadda zata kare kanta amman bata da mafita, buɗe baki take sonyi tayi masa magana ta kasa, toh mi zata ce masa hakuri zata fara bashi ko kuma kare kanta zata yi duk tabi ta ɗimauce lokaci ɗaya sai zufa ke karyo mata.
“Tashi kije gida Huda karki yar da ki kwana a gidan nan”
Kamar saukar wahayi taji maganar, abunda bata taɓa zato ba ko da a mafarki ba, ne hakan yake nufi? sakinta yayi kenan ko me?
“Gi....gi...gida ..fa..ka..ce Saif..”
Ta faɗa muryarta ta rawa, shi kuma ya bata amsa a tsawa ce
“Gida nace ki tafi kinsan mi nake nufi ai karki yarda na dawo tarar dake a ɗakin nan”
Yana faɗa ya juya a fuce ya fice, lallai da sauran rina a kafa, dan ba wai ya hakura bane da sauran magana, ita kanta tasan asirinta ya tonu, bata da hanyar kare kanta fatan ta ɗaya kar ya rabu da ita.
* * *
A fusace ya isa asibitin da Safiyyah take, bai damu da dare ba dan goma ta gota shaɗaya ake batu, da wani irin karfi ya tura kofar ɗakin, sai da ganin Momi da Gwaggo ya katse masa hanzari,
“Saif Lafiya dai?”
Momi tayi masa tambayar cikin mamakin ganin shi yanzu da kuma jallabiya, tasan Saif baya son fita da jallabiya a ko ina idan ba gida ba.
Duk yadda yasa ya ɓoye damuwarsa a fuska kasawa yayi saboda ɓacin ran nashi yayi muni da yawa sai dai bai faɗa mata komai,
“Ba komai Momi gurin Safiyyah nazo”
Ya faɗa kamar baya son magana, sautin muryarsa da kuma yanayin fuskarsa ya karantar da Momi halin da ɗan ta yake ciki, lallai ba lafiya ba ganin mai ido da sanda,
Gashi kuma yazo da dare abunda bai taɓa ba tun da aƙka kawo Safiyyah,
“Momi ƙku ɗan bamu guri zamuyi magana”
Maganar ta bata mamaki wace irin magana ce da ba zai iya faɗi a gabanta ba? Gwaggo ce ta katse mata hanzari ta hanyar buɗe kofar fita tana faɗin,
“Bari mu fice tun da ba a son muji”
Ganin ta fice yasa Momi ita ta fice zuciyarta cike da rashin yarda.
Suna fita Safiyyah ta kalleshi fuskarta ba yabo ba fallasa, tasan waye Saif tun kamin tasan kanta ta kuma san irin tsanar da yake mata babu abinda zaisa ya taso cikin dare yazo duba ta daga ganin ma fuskarsa ka san ba lafiya ba, ga kuma guguwar harar da yake watsa mata,
Kofin dake hannunta na tea ta aje ganin yadda ya nufo ta kamar mai shirin ɗaukar ranta yau kan ita dashi sai Allah, gawa ta rike mai mata wanka duk da bata san meke tafe da shi ba amman tasan ba alheri bane,
“Mi Minal tayi miki kike cutar da ita? Mi yasa kike son kashe min ɗana jinina? yaushe zaki karantar da kanki ba zan taɓa son ki ba? wace irin mahaukaciya ce ke?”
A lokaci ɗaya yayi mata waɗannan tambayoyin yana ɗaga murya, hantar cikinta ta kaɗa cikinta ya ɗuri ruwa, yawun dake bakinta ya tsinke asirin ta zai tonu, fuskarsa take kallo idanunta a razane tana neman mafita,
Kura mai wayo abunku da yar bariki a nan take taso saye shi da murya kamar tayi kuka
“Subhanallahi wannan wace irin magana ce haka Yaya? me kake nufi ne? Kar dai a shafa min bakin fantin da aka shafa ma Minal a juyar da wannan lamarin a gare ni”
“Kinsan me nake nufi Safiyyah, kuma wallahi duk wani abu ya samu ɗa na ki kaddara ke ya sama”
Hawayen dake makalle a idonta suka zubo, jin yadda ya katsa mata tsawa
“Na san baka so na yaya maybe yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa aka min wannan sherin amman yaya ba zan aikata maka haka ba me zai sa na aikata maka haka waya yake kokarin haɗa ni da kai ne?”
Kuka take yi ta marairaice murya kamar gaske, bai saurara mata ba dan yanzu baya ganinta da kima balle yaga tausayinta, shi dai so yake ya kara tabbatar da gaskiyar abunda yaji da kuma wanda Dr Zainab ta faɗa masa, ita kuma taki bashi damar hakan dan ta marairaice ita sam ba ita bace haɗa su ake son ayi,
Akwai kamshi gaskiya a labarin da Zainab ta bashi tun da gashi ya kama Huda Safiyyah ce kawai ta rage masa so yake ta amsa da bakinta ta aikata ɗin ko kuma ta nuna masa alamun hakan dan yasan wannan kukan na munafurci ne wai ita yar duniya shi take son rai na ma hankali.
Jin yayi shiru yasa ta fara tunanin ko hakarta ta cin ma ruwa ne? Lallai ya fara yarda da ita tun da har ya tsaya sauraren kukan ta, ta kalleshi idonta rau-rau da hawaye,
“Wai Yaya waya faɗa maka wannan maganar ne?”
“Ubanki ne ya faɗa min”
Bata an karaba yayi mata ɓarin makauniya ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, har sai da taga wasu yan taurari nan take bakinta ya haɗe da jini da miyau, bai damu da ciwon dake kafarta ta ya ɗebeta kamar kayan wanki ya jefar ya hau shurinta kamar an aiko shi,
Razanannar karar da ta saki yasa Momi suka shigo da gudu, Yadda yake aika mata shurin sai da yaba Momi tsoro, duk yadda taso ta jashi baya kasawa tayi shi kuma yaki ma kallonta sai shurin Safiyyah yake,
Tassss-Tasss Momi ta watsa masa mari, bai ji zafin marin ba duk da marin ne yasa ya ɗan natsu ya kalleta,
“Ba kada Hankali baka da imani Saifullah mi yarinyar nan tayi maka haka? koma wani abun tayi maka aika duba halin da take ciki”
Cikin kuka Momi tayi masa wannan kalamin, dai-dai lokacin Nurses suka shigo tare da Gwaggo dan ita ce ya fita ta kirasu ganin Safiyyah ta suma,
. Kukan Momi yasa jin ba daɗi shiyasa shi bai ma jidaɗin da ya tararda ita a asibitin ba daman yasan hakan sai ya faru ko da bayan idonta balle a gabanta,
“Momi yarinyar nan ita ta kulla komai duk abinda ya faru da Minal ita ce ta kullah kuma a yanzu haka so take ta zubar da cikin Minal”
Yana kai aya Momi ta sake watsa masa wani mari, ta kalleshi rai a ɓace Cikin muryar kuka tace
“Ba kada hankali Saifullahi daga wani can yaje ya zugo ka sai ka ɗauka dan kawai ka raina yarinyar nan, nasan baka sonta amman ba zaka ɗauki karan tsana ka ɗora mata ba akan me yarinyar nan bata da Uwa ba uba amman kabi ka takura mata me ta tare maka ne? ba zan yarda kana ci mata zarafi ba kabar ganin kai ka ɗai na haifa namiji kana yi mata yadda kake so ina kyale ka, ba zan sake bari ka ci amarta ba ba zaka sake cutar ta ba”
“Momi ina da hujja akan hakan .....”
Ta katse shi,
“Rufe min baki fool wani ya isa ya kawo maka wata hujja ne bada idonka ka kama Minal ba yanzu ka dawo kace wai Safiyyah ce, ɓace min da gani fita kabar ɗakin nan”
Bai iya musu da Momi ba tun tasowarsa, hakan kuma bata taɓa bashi umarni yaki bi ba, yasan wacece uwa dan haka baya son ɓacin ranta, ganin hawayen dake zuba a idonta yasa shi saurin ficewa daga ɗakin,
A harabar asibitin ya fito yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗan samu sarari tun da ya bugi Safiyyah har ya sumar da ita duk da ba hakan kawai yaso ba, Huda ce kawai ba zai taɓa sama hannu ba dan yasan maganinta daya tabbatar da zarginsa zai yanka mata ticket.
Please ku na votes da comment shine abunda ke encouraging ɗin mutun yana update da wuri kar kubar aikina ya tafi a banza😢🙏
ŞİMDİ OKUDUĞUN
BABBAN GORO
RomantizmNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...
