BABI NA ARBA IN DA TAKWAS

3.6K 340 20
                                    

Ja tayi baya da sauri ta dafe junco dan ba karamin mari yayi mata ba,

Lafiya mi tayi maka haka?”

Momy ta tambaya tana tashi tsaye, sai a lokacin ya lura da Momy, juyar da fuska yayi ya ɗan haɗe rai. A nan ya shiga neman dalilin marin nata da yayi ya rasa, shi kan shi bai san dalilin marin nata dayayi ba shi dai kawai ya samu kansa da jin haushin murmushin da tayi masa da magana.

“Momy parking tayi ba dai-dai ba gurin da nake aje mota na take ta aje

Ya faɗa yana kokarin kare kansa, tunawa da yau gurin da yake parking yaga motar ta fake,

Haba dan Allah dan Annabi sai kuma kayi mata wannan mari haka? Sai kace karamar yarinya, ai sai kaje kace ta ɗauke motar ko.? Ba ma ita ra fita da Mota ba Lubna ce

Shafa kansa yayi yana ɗan yatsinar fuska ya zauna saman kujera, kallonta yayi kamar yace tayi hakuri sai kuma yaji ba zai iya ba, ya kalli Momy data ranta ya ɓace ya ce

Na ɗauka ita ce sorry Momy”

Banza Momy tayi dashi tana kallon Safiyyah da ta rufe ido tana hawaye, juyawa tayi kamar kazar da kwai ya fashe ma ta nufi ɗakin.

Ni Wallahi halin naka ya fara isa ta bana son abunda kake yima yarinyar nan ko kaɗan

Momy ta faɗa tana jan tsaki cike da ɓacin rai. Kallonta ya sake yi

“Momy kiyi hakuri

“Wane irin nayi hakuri fusabilillahi abun da kake mata kyautawa ne? Ko kuma dan tana zama nan gidan sai ya baka damar yi mata duk wulakancin da kaga dama

BABBAN GOROHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin