BABBAN GORO
NA
KHADEEJA CANDY
®
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*36*
Kasa Saif yayi da kanshi ya ƙlumshe ido yana sauke ajiyar zuciya,
“Ka yarda da ni Saif zan maka duk yadda kake so amman idan nima kayi min yadda nake so”
Buɗe ido yayi ys kalleta,
“Wa nene wanda kike son a sako miki.?”
“Mijin Mahaifiyata ne bayan rasuwar Mahaifin mu mahaifiyata ta aure shi ni kaɗai ce ta haifa da Babana sauran duk nashi ne tun da aka kamashi ita da sauran yan uwana sun kasa samu natsuwa ni kaina na kasa samun natsuwa saboda rashin natsuwar nata”
“Mi yayi aka kamashi?”
“Yan danfara suka danfare shi ya ranta musu kuɗi sai suka gudu shine su kuma suka kamshi”
“I hope gaskiya kika faɗa min!”
“Ko da yana da wani aibin toh ban sanshi ba, dan ni haka mahaifiyata ya faɗan min kenan”
“Fine Miye sunan shi?”
“Sunanshi Alhasan Muhammand Yola”
Wayarsa ya ciro daga aljihu ya dannan kira, bata daɗe tana ringing ba aka ɗauka,
“Ka bincika min wani da aka kama mai suna Alhasan Muhammad yola”
Yana faɗa ya kashe wayar, ya kalleta
“Make sure gaskiya kika faɗa min akan Huda dan duk na gani karya kike sai na sa an wulakan ta ki”
“Gaskiya ce mana Saif how do think mace kamar ni can lie to someone like you!
idan zaka yarda zan fara baka evidence yanzu”Bata tsaya jiran abinda zai ce ba ta ɗauko wayarta, ta shiga danne-danne, daga bisani ta ɗago ta kalleshi
“Ka buɗe Bluetooth ɗin ka zan turo maka wani abun yanzu sannan ka bani number wayar ka zan turo maka wasu abubuwan ta whatsapp”
Bai mata musu ba ya mika mata wayar ta tura masa abubuwan, ta mika masa wayar tana faɗin,
“Ina son ka kunna wannan Audio ka ji a cikin Audio akwai wanda zaka ji yadda suka shirya komai tsakanin ta da Safiyya na abunda akayi ma Minal kuma nasa maka wata number mai sunan Faruk inason kasa number a wayan Huda jaga ya sunan zai fito sauran abubuwan sai ka cika alkwari nima zan cika maka”
Hannu yasa ya karɓa bai ce da ita komai ba kwakwalwarshi a tushe take, shi har yanzu bai yarda ba sai ya samu hujojin akan hakan, yana zuyawa ta kira shi
“Saif.... Kayi kuskuren auren Huda ka aureta ba tare daka bincika wacece ita ba baka bincika tarbiyarta ba Huda tana tare da abokin karatun ka ko kuma nace abokin ka tun bata aure ka ba sanadiyar sa ta sanka ka ganta kace kana sonta”
Bai juyo ba kuma har lokacin bai ce mata komai ba ya fice.
Har ya isa parking space bai san ya isa ba saboda tunani.da yake magangun Dr.Zainab ne suke masa yawo kai ya daɗe tsaye gurin motarsa kamin ya buɗe ya shiga, koda ya isa gida har wani ciwon kai yake ji a cikin motar ma ya daɗe zaune kana ya fito ya nufi cikin gidan.
Yana tura kofar falon Huda dake zaune sanan kujera ta taso da gudu ta tarbeshi tana faɗin,“Oyoyo Habibi sannu da zuwa”
Kallo ɗaya tayi masa ta ganshi abnormal, sai dai ba zata iya tantance halin da yake ciki ba, saboda yayi kamar marar lafiya kamar kuma mai damuwa.
“Dear lafiya na ganka haka?”
Ta tambaya cike da damuwa, Kallon fuskarta yake sai yanzu yake tuna wasu abubuwan nata, maida ta yayi gefe ya nufi upstairs hanyar ɗakinsa yana shiga ya maida kofa ya rufe ya zauna gefen gado ɗafe da kai,
daker ya samu ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya fito, ya saka jallabiya da gajeren wando, Sai a ƙlokacin natsuwa ta ɗan shige shi, yana shirin zama Huda ta shigo ɗauke ta turen drinks fuskarta ba far'ah, kusa dashi ta zauna ta zuba masa drinks ɗin tana masa magana,“Dear ga Drinks ɗin ka kasha nasan rayuwar ka zatayi sanyi sai ka faɗa min abinda yake damunka”
Ko ɗago wa baiyi ya kalleta ba balle ya bata amsa, sosai hankali ta ya tashi rabon da taga ɓacin rai shi irin wannan har ta manta, toh mi yake damunshi ko wani abun akayi ne?
“Saif kayi min magana mana ko nayi maka wani laifin ne?”
Ta faɗa cikin muryar kuka, sai a lokacin ya kalleta ya ɗan murmusa kamar babu komai,
“Wani ne ya ɓata min rai a office amman karki damu ya wuce”
Drinks ɗin ta karɓa ya sha yana janta da fira dan ya kawar mata da zagin dake ranta,
Ita kuma hankalinta ya kwanta ganin ya dawo dai-dai.DARE.....................
Tare sukayi hira a ɗakinta sai da ya tabbatar da bachi ya ɗauke ta sannan ya ɗauki wayarta ya saci kafa ya fice ɗaga cikin gidan ya nufi gurin motarsa ƴa buɗe ya shiga bayan ya rufe ya kunna Audio da Zainab ta tura masa,
Ba karamin mamaki yayi ba jin abunda Audios ɗin ya kumsa jikinsa ya mutu sosai da abunda kunnuwansa suka ji masa, tabbas muryar Huda ce kuma duk maganganun da yaji akan sa ne sai kuma Minal wani gefen da saurayin nata, Duk wasu tambayoyin da yake son sani ya samu amsar su a Audios. jufa ce ta shiga karyo masa a nan take yaji kansa na tsarawa, wayarta ya ɗauka ya saka number da Zainab tasa masa, Ga mamakinsa sai ga number ta fito amman ɗauke da sunan _FAIRUZA_ a nan take ya danna ma number kira da wayarta, Bai kara katsewa ba sai da yaji muryar namiji muryar abokinsa ƴa ɗauka,“Hello Sweetheart baki yi bachi ba?”
Bai amsa ba sai kawai ya kashe wayar, ya fito cikin motar a fusace ya nufi ɗakinta, yana isa mai number ya kara kira, wani mugun bugu Saif ya kai mata ta farka a firguce tana haki, wayar ta mika mata ba tare da yayi mata magana ba daman already yayi picking yasa hands-free,
Karɓa tayi amman bata kara wayar a kunne ba sai kallon Saif take jikinta na rawa,
“Hello Sweetheart naji kiran ya katse ne kp network ne?”
Jin muryar mutunen yasa ta kalli gaban wayar number da taga hankalinta yayi matsifar tashi, kamar wanda ya ruɗe sai tace
“Wanene?”
Tana kallon Saif,
“Wanene kuma Faruk ne ba Huda bace?”
Shiru tayi batayi magana ba sai kallon Saif take abunda ka marar gaskiya nan da nan idonta ya faɗa wani zafi ya rufeta baki buɗe tana numfashi kamar marar lafiya, jin hakan yasa mai kiran ya kashe.
ME KUKE TUNANI GABA.....?
DON'T FORGET TO VOTE
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...