Kai tsaye ya shigo cikin gidan, kana kallon fuskarsa kasan wani abun ne ke tafe dashi, Sama sama ya gaisa da Gwaggonsa yana tambayar ina Safiyyah
“Lafiya?”
Gwaggo ta tambaya ganin yanayinsa
“Lafiya kalau nazo gaishe ta ne naji ance taji sauki”
“Eh taji Sauki bari a kira maka ita”
Tashi tayi ta nufi ɗakinta ba ɗan ta bamsu ba komai ɗin ba, dan tasan Safiyyah bata da matsayin da Saif zaizo gaishe ta ɗan taji sauki duk da tana ganin yana tausayin halin da take ciki, amman kuma miyasa tun lokacin bai zo ba sai yau!
Da wannan sake-saken ta tura kofar ɗakin Safiyyah ta shiga. Kofar ɗakin ya tsura ma ido har sai da yaga fitowar Gwaggo,“Gata nan zuwa”
Kai kawai ya ɗaga mata ta shige ɗakinta, ya sake maida idonsa kan kofar ɗakin da yake saton Safiyyah na cikin dan ɗakin Gwaggo ta shiga, ta ɗan jima kamin ta fito har ya fara tunanin koya tashi ya shiga ɗakin ne, sai gata ta fito sanye da Abaya fara da farin gyale ta lulluɓe kanta, a hankali take tafiya har ta k'arasa kusa dashi, ko wannen su yana kallon ɗan'uwansa, ita tana masa kallon data saba masa sai dai yau ya ɗan babbanta dana kullum, shi kuma yana mata kallon ta iya zai fara! Shi fa har yanzu bai gama yarda ita ce da hannu a ciwon Kairat ba, tunawa da abunda tayi ma Minal yasa shi kawar da wacan tunanin nasa, ya ɗauke kai daga kallonta yana muna mata kujera
“Zauna mana kinyi min tsaye a ka”
Sai a lokacin ta samu damar yi masa magana, sai dai jikinta yana bata kamar wani abu zai faru, yadda gabanta yake faɗuwa ita kanta tasan ba lafiya ba duk da wata zuciyar nace mata na ganin Saif ne sai dai bata gama gasgata hakan ba,
“Ya jikin naki?”
Muryasa ta daki dodon kunnenta, kamar ta ɗago kai ta kalleshi sai kuma taji ba zata iya ba, kanta a kasa ta amsa mishi
“Naji sauki sosai”
Shiru ne y biyo baya, kamin ya cuta maganar data razana ta
“Kin warke Kairat ta kwanta, wani yace min warke warki ya haddasa ciwon Kairat”
A razane take kallonsa, ta kasa buɗe baki tace masa komai sai tunanin take wanda ya faɗa masa wannan maganar take. Shafa, no Shafa ba zata sona asirinta ba to wanene? Ita kaɗai fa tasan sirrinta, ina Saif yaji wannan maganar?
“Ba ki ce komai ba”
Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, zufa ce ta karyo mata ta gangaro tare da hawaye. Daga ita har shi kallon Kofa sukayi ganin shigowar Momy, Saif bai jidaɗin ganinta ba sam dan yasan ba zata barsa yayi abunda ya kawo shi ba, aiko ya canka a daidai dan tana karasowa kusa shi ta katsa masa tsawa
“Tashi ka wuce gida”
“Momy..”
“Rufe min baki ba zai yiyu ba Saif ba kai kaɗai muka haifa ba amman kullum kai ne da matsala cikin gida, karka manta mahaifinka yana da wasu yayan maza idan har ganin kake ni kaɗai na haifa namiji”
Yanayin ta ya nuna ranta a ɓace yake kuma yasan ya baza ta saurara masa ba, mafita ɗaya ce yabi abunda tace, tashi yayi ba ɗan yaso ba sai dan bashi da mafita sai wannan ya nufi kofa, har zai fice ya tsinkayo muryarta tana magana dashi
“Gaskiya ne Saif, lafiyar dana samu ya haddasa ciwon Kairat”
“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un”
Momy ta faɗa tana zauna, wannan furucin na Momy ya haddasa Gwaggo fitowa ɗaga ɗakinta daman can a tsawale take tana son tasan wainar da suke toyawa a falon,
CZYTASZ
BABBAN GORO
RomansNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...