Assalamu Alaikum readers of ™BG i want to use this opportunity to say something hope za ku ba ni aron hankalin ku! I know we are writing to entertaining, but we have to touch the reality, ina son duk mai karanta littafan KHADEEJA CANDY ya rik'a sawa a ransa kamar gaske ne yake faruwa saboda ina tafiyar da littafai na ne akan abunda hankali zai ɗauka.
Na samu messages ɗin readers wasu like karki kashe mana Minal please. wasu like idan kika kashe ta kin ɓata Novel ɗin ki. wasu like ni ban taɓa ganin inda aka kashe star a Novel ba. Wasu idan kika kashe ta me kika yi kenan. wasu like bai kamata Minal ta mutu ba. wasu like Please ki ce dogon suma tayi and list goes on and on and on and on and on......
Haba dears! Yanzu dan Minal tana star a Novel sai a ce ba za mutu ba? Ke yanzu dan ana sonki a gidan ku sai ace ba zaki mutu ba? Ki rika sawa a ran ki kamar ke ce ko kuma wata ce hakan yake faruwa da ita, wasu na cewa wai Minal bata ji daɗin rayuwa ba ya kamata ace taji daɗin rayuwa kamin ta mutu ina son ku koma baya ku karanta gurin da kuka manta, Minal tayi rayuwa mai kyau kuma ta jindaɗi Mummy ta nuna mata gata sosai har hakan yasa ta fara shaye-shaye babu wanda ya isa ya tsaya ya faɗa mata wata magana ta kyale shi remember? daga lokacin da ta fahimci bata da uba ta soma fuskantar bakin ciki a rayuwarta, masu cewa ya kamata ace ta gana da mahaifinta ba duka abunda mutun ke so yake samu ba, Nasan wata mata da iyayenta suka yi auren kasa da kasa babanta ɗan Najeriya mamanta yar Ghana sai suka rabu tana karama lokacin da ta girma ta mallaki hankalin kanta sai ta nemi ganin mahaifiyarta haka ta haɗa kuɗi motar ana sauran kwana uku ta tafi aka kira aka faɗa mata mamanta ta rasu kuma bata taɓa ganin mahaifiyar ta da ido ba, image idan Novel ne sai a ce bai yi kyau ba right? karku manta Mahaifin Minal shi ya wulakanta ta da kan shi, akwai masu cewa taya za ace Minal ta mutu ta bar Mummy bayan ita kaɗai ta mallaka a duniya da ace reality ne da nace mu ku haka Allah yake ikonsa idan yaga dama akwai wanda har ya gama rayuwar sa ba zai taɓa ganin jininsa ba akwai wata friend ɗita maybe wasu daga cikin kun sun santa ana ce mata Hannatu Ismail tana daf da kare karatun ta Allah ya karɓi abarsa kuma ita kaɗai iyayenta suka haifa sun ɗora mata buruka da yawa babu irin jindaɗi da bata yi a gidan su amman mutuwa ta kutsa ta ɗauke ta toh haka rayuwa take muna cikin sha'anin mu take ɗauke mu. ya kamata mu rik'a kula da irin wannan, na fahimci wasu suna karanta Novels ne kawai da nishaɗi kalilan ne ke karanta su fahimci sakon da abun ke son isarwa ko kuma darasin dake ciki.
Idan a reality ne kuna ganin mai ciwo irin na Minal zata rayu? No way duk da nasan rayuwa a hannun Allah take karku manta the Doctor said mai blood cancer leukemia in dai yayi Cronin they can't survive kun tuna? sannan ku koda yaushe ace dogon suma a Novels always in reality hakan yana yawan faruwa? No nasan ita ce ansar! To haka zaku rika sawa a zuciyarku idan kuna karantawa after that akwai Kairat, Huda, Safiya, Saif duk suna raye only Minal is gone and she has to, bari na tsaya a nan kar wasu suce na cika surutu i says a lot, anyway thank you for your time i really appreciate your efforts ina fatar za ku fahimci bayanin nawa zaku kuma tuna abunda kuka manta. I heart you all stay bless all the best one heart one love 😍 happy reading👌🏿
42
Kairat nayin Sign ya juya da sauri ya shiga ɗakin da take, tare da taimakon nurses da wasu likitoci aka shiga da ita ɗakin tiyata, a kofar ɗakin tiyatar Kairat ta tsaya tana safa da marwa hawaye na mata zuwa tana jiran a fito da ita kashe kunne tayi taa sauraro jin take kamar ace mata Minal ɗin tana raye.
Sun ɗauki awo uku a ɗakin suna yi mata tiyata, cikin nasara aka yi mata aikin suka fito baby girl sai dai bata da lafiya sosai dan duk a takure take numfashinta ma sai a hankali. suna fitowa da ita Kairat ta nufo su da sauri da nufin karɓar yarinyar jiki har karkarwa yake kamin ta mika hannu Doctor ya rike ta a nan ta kalleshi ta kalli baby,
“Sorry Kairat ba zaki iya taɓa ta yanzu ba bata da isassar lafiyar da za'ayi mata haka a yanzu zamu sata cikin kwalba ne zuwa wani lokaci saboda yar bakwai nin ce”
Ya faɗa yana kallon Baby dake hannun wata nurse, karasa tayi kusa da baby ta tsaya tana kallonta sannan ta risina ta manna mata kiss a goshi. a nan Dr ya ɗaga ma nurse ɗin kai ta wuce da ita, haka Kairat ta bita da kallo har ta ɓace mata da gani. kafaɗunta Dr ya dafa ya juyo da ita ta yadda zata fuskance shi ya soma mata magana a hankali
“Kairat dole ne ki zama mai hakuri you are the only person da Dr.Salamatu zata gani ta jidaɗi sai kuma baby da Minal ta bari,
Dr Salamatu da daɗe da sanin Minal ba zatayi rayuwa mai tsawo ba tana yawan bincika ta akan ciwon ta ni kuma ban taɓa ɓoye mata komai ba duk mai rai dole ne ya yarda da mutuwa ko da kuwa kafiri ne balle musulmi sai dai hanyar da zata zo maka ɗin zata girgiza ka,
Kairat kece zaki cire ma Dr Salamatu kewar Minal dan ke kike zama da ita bai kamata ace ke kika kuka ita tana yi ba mamaci baya son haka addu'ah ku take da bukata idan ke kika kuka waye zai lallaɓa ta ya nuna mata hanyar yin hakurin? you have to be strong nasan ke da Minal tare kuka tashi dan tun lokacin dana fara kula da Minal tare na ke ganin ku tun kuna kanana nasan zaki ji zafi sosai but dole ne ke ki ɓoye naki kukan ki haɗiye damuwarki for the sake of Mummy”
Hannu tasa ta share hawayenta tana kallonsa cike da fahimta, ganin hakan yasa shi cigaba
“Nasan yanzu ta farka dan alluran da nayi mata na awa biyu ne please stay with her wipe her tears”
Kai ta ɗaga masa tana sauke ajiyar zuciya, shi kuma ya sake ta ya nufi hanyar waje. Sai da tayi ta sauke ajiyar zuciya ya fi goma tana share hawaye ya fi a kirga sannan ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakin da Mummy take ciki.
Zaune ta tarar da ita tana murza wata munduwa dake hannunta hawaye na mata zuba, har Kairat ta zauna kusa da ita bata ɗago ta kalleta ba, a nan Kairat ta kai hannu ta ɗago Fuskarta, Mummy kamar mai jira sai ta fashe da kuka tana faɗin
“Lokacin da nayi birthday Minal ta bani wannan abun hannun tace min tana son na sashi a hannuna na rika tunawathat do you remember?”
“Yes i remember Mummy ta baki shine dan ki rika tunawa da ita kiyi mata addu'ah ba kiyi mata kuka ba please Mummy karki ce min baki shirya ma zuwan wannan ranar ba ke da kanki kike faɗa min wata rana Minal zata tafi ta barki har a gabanta kin faɗa ita ma ta sha faɗa miki haka,
ta kan ce miki ko da bata nan ni ina nan kuma nima nace miki haka Mummy ba Minal kawai kika haifa ba har da ni why you behaving like this ko da yaushe sai kice baki da kowa sai ita mi yasa kike min haka? mi yasa kike yi ma Minal kuka a lokacin da take da Bukatar addu'ar ki bata sha faɗa miki ba karki mata kuka idan ta rasu ko bata faɗa miki ba kuma bata tafi ba Mummy sai da ta bar miki copy ta”
Cike da natsuwa Mummy ta kalleta sai ta jata jikinta ta rumgume still tana hawaye
“Kuka shine yake yin kansa Kairat ba sai ana kirasa ba but I will try”
Kamkame ta Kairat tayi tana nata kukan a hankali yadda Mummy ba zata ji ba.
Silent readers run da ba Ku votes ban ya ban ya... 😹
Dear, Readers still a'ce dogon suma tayi? waiting for your comments
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...
