BABBAN GORO...!
NA
KHADEEJA CANDY
_Gun zance ka iyawa halshenka wani guri kuma karda ka kai kanka sannan ka zamo mai kare mutunci ka_👌🏿
_NURA M INUWA_BABI NA GOMA SHA D'AYA___11
Kuka Mommy tayi sosai kamin ta cigaba,
_“Bakin cikin kan iyayena sun yi shi sukace sai na faɗa musu wadda yayi min cikin nace Alhasan ne, nan take suka je suka same shi da batun nan ya karya tani yace shikan ko hannu na bai taɓa rikawa ba kazafi nayi mashi har da cewa sai yayi karata daker iyayena suka samu ya hak'ura Abbah na ya sani gaba sai na faɗa mishi cikin waye na rantse mishi yaki ya yarda ni_
_Tun daga lokacin na soma fuskantar wulakanci ɗaki ɗaya aka ware min kullum ciki nake rayuwa bana zuwa ko ina har cikin ki ya kai sata tara, Ranar wata Laraba naqudarki ta taso min da taimakon mahaifiya na haife ki”_
Dagowa tayi ta kalli Minal idonta na zubar da hawaye tace “Tun da na haife Tausayinki ya kamani na rayuwar da zaki shiga da kuma zuwan wannan ranar da zaki tambaye ni waye ke”
Wata irin ajiyar zuciya Minal ta sauke ta jinginar da kanta jikin Saif. Tana kallon Mummy da ya cigaba da zancen,
_“Duk wace ta haihu tana bukatar kulawa amman ni ban samu ba sai ma lokacin na gane bana da gata abinci yara ake bani ruwan nono na ya soma kafewa a haka na wata biyu ni da ke muka koma kamar masu ciyon kanjamau saboda rama ban taɓa tausayin kaina ba kullum ke nake tausayi, wata rana Abbah na ya fitar dani cikin ɗakin da nake Mamana na kuka ya sani a mota mukayi ta tafiya mai nisa sai da ya kai hanyar dake tsakanin Abuja da Kaduna ya sauke ni ya kuma yi min gargaɗin karna kuskura waiwaiya su da duk dangin su dan na riga na ja musu abun faɗi_
_A gurin ya barni naci kuka sosai na saɓaki a baya ina tafiya idan na gaji sai na tsaya na huta haka na rik'ayi har na kai wani kauye dake kusa da gurin, mutanen kauyen saun tarɓeni sosai ni kuma nayi musu karya nace yan fashi suka tare ni nayi gudu har na kawo kauyen nace musu mijina yana cikin garin Abuja, sun nuna min so sosai suka haɗa min kuɗin mota da rakiyar wasunsu aka kaini tashar garin na hau mota Abuja,_
_Dana shiga cikin Abuja sai na shiga gidajen masu kuɗi bara idan dare yayi sai naje wani tsohon shago na kwana, Wata rana ina halin baran na faɗa gidan Alhaji Mamman, yanayin halin da nake ciki ya bashi tausayi gani da kuruciyata hakan yasa ya sani gaba yana yi min tambaya dalilin baran nawa, ban ɓoye mushi komai ba na faɗa mushi labarina sosai ya tausaya min shi da iyalinshi_
_Daga lokacin ya maidani gidanshi ya rik'e ni yana nuna min gata ni dake cikin yan kwanaki mukayi bulbul bayan na yayeki yace zai maidani makaranta sosai naji daɗi kuma na Amince dan daman abunda nake jira kenan, a matarshi ya sani tare da Matarshi da yar shi Kairat muka je har yola gurin Abbah na ɗauko takarduna nan sosai ya so ya shirya ni da Abbah amman sam yak'i yarda sai ma cewa da yayi wai karuwanci zanje yi da gaggan nayi wannan cikin,_
_Ban damu da duk wani furuci nasu ba tunda ba albarka suka cire min ba kuma daman ni ke nake yima tanadi, yana dawowa ya nema min admission na shiga yin mastas ke kuma ya samo mai rainonki, ina gama mastas ya sake nema min admission na koma University nayi degree a ɓangaren Economics, ke kuma ya saki a Primary school,_
_Bayan na kare karatun ya nema min aiki a kanfanin da yaki aiki, da sannu sannu har aka bani karamar manajan kanfanin, Kina kare Secondary School, na name miki Chartere By act of Congress The American University, Maza da dama sun yita neman Aurena amman naki yarda nayi Auren dan kawai nayi miki tanadi_
_A lokacin Alhaji Mamman ya soma sani a harkokin Siyasa ni kuma na shiga gadan gadan har na samu karamar Minister man fetur, ban tsaya nan ba na shiga siyen hannayen jari ba ɗaya ba duk dan ki samu jindaɗi yadda kowa yake ji,_
_Daf da zaki gama Secondary school na koma gurin dangina ba dan komai ba sai dan nasan duk kika girma sai kinso ganin family ki, sunyi na'am dani a lokacin sai dai kece suka ce ba zasu karɓa ba dansu a dangin su babu shegen dan haka karna na kuskura nuna masu ke_
_Nayi mamakin yadda dangina suke da riko wata kila ko dan suna yare ba hausawa ba, ni kuma tun daga lokacin na yanke shawarar kin haɗa ki dasu dan karsu wulakanta ki,_
_Kina gama Secondary School kika dawo Nijeriya, ni kuma lokacin na sauka daga muka mina sanadiyar chanjin gobnati da aka samu nan ne ke kuma kikace kina son na nema miki makaranta a faransa_
_Bayan tafiyarki karatun ne wannan gobnati ta hau akamin babbar ministen man fetur_
Ajiyar zuciya ta sauke tace,
_Da kika dawo sai kika kika fitar da wannan saurayin naki wadda ya chanja miki tunani har kika rik'a k'ina a kanshi_.
K'asa Minal tayi da kanta tana haɗiyar yawu, idonta cike da hawaye,
Tashi Mummy tayi ta shiga bedroom, bayan kamar minti goma ta fito rike da wani littafi mai kamada Diary daga gani tsohuwar ajiya ce dan duk tayi kura, ta mika ma Minal tana faɗin,
“Wannan littafin na aje shi ne danki duk gurin da wani family members naku yake address ɗin shi yana nan ciki wannan shine tarihin ki Minal ina fatar zaki sami natsuwa”
Hannu Minal tasa ta karɓa tana kallon fuskar Mummy dake kokarin maida kukan dake son fito mata,
Juyawa tayi ta koma ɗakin hawaye na mata zuba, Hannu Minal ta mika zata rik'o hannun Mummy, da sauri Saif ya rik'e mata hannun tana kallonshi ya girgiza mata kai, alamar a'a.
Nan itama ta fashe da wani irin matsanai cin kuka ta chusa kanta cikin kirginshi, rumtse idon yayi da suka yi mishi jawur kamar wadda yayi kuka,Kukan tayi sosai sai da ya tabbatar da ta samu sukuni sannan ya ciro handkerchief ɗinshi ya share mata hawaye ya rik'a hannunta suka fice,
Gurin da yayi parking ɗin motarshi ya nufa sai ya saka ta sannan ya shiga ya fara Driving,
Har suka isa babu wadda yace da wani uffan ita dai sai kuka take yi, shi kuma ya kasa bata hak'uri.
“Minal miye haka kuma tun ɗazu kuka kike kodai baki yarda da abunda Mummy tace miki bane?”
Bayan ya kashe motar yayi mata maganar yana ɗan buga sitarin motar,
“Na yarda Saif ina dai jin ban kyautawa Mummy ba ina ma ban aikata abunda na aikata ba miyasa idona suka rufe na kasa fahimtar Mummy mi yasa banyi mata uzuri ba? Ji nake yi ba daɗi bansan miye abun yi ba”
Kallonta yayi,
“Minal in dai har kinyi nadama to kije ki bata hak'uri ki nuna mata kinyi nadama kuma ki roki gafarar ta kinji?”
Kai ta ɗaga mishi tana share hawaye, sannan ta buɗe motar da niyar fita, sai kuma ta juyo ta kalleshi.
Murmushi ya sakar mata wadda ya faɗar mata da gaba ya wani lumshe sleeping eyes ɗinshi ya buɗe still yana murmushi,
Ta daɗe tana kallonshi kamar ba zata ɗauke idon ba, sai kuma ta k'arasa fitar ta rufe mishi motar.
Bai bar gurin ba sai da yaga ta shige cikin gidan sannan ya sauke ajiyar zuciya ya sama motar shi key,
Kai tsaye gidanshi ya nufa yana yin parking ya dubi a gogon hannunshi, 10:41pm ya gani kai ya ɗan girgiza ya buɗe motar ya fita,
Da sallama ya shiga yana kallon gurin da Huda ta saba zama, cikin sa'a kuwa ya hangota zaune ta tsaɓa ado tana kallon tv kamar bata san da shigowar shi ba, duk da yasan taji sallamar maybe tayi hakan ne dan yayi dare,
Kusa da ita ya k'arasa ya ɗan lek'i fuskarta
“Dear kina jina kika ki amsa sallama ko?”
K'ara ɓata fuska tayi,
“Sai da nace maka karka daɗe zamuyi zaɓen cake amman kaje ka zauna har yanzu”
Sai a lokacin ya tuna da maganar Birthday ɗinta, da sauri ya zauna kusa da ita,
“Ayyah Wallahi kwata-kwata na manta.. -”
Ganin yadda ta kalleshi yasa ya chanja maganar,
“I mean wani abun nayi important ba wai mantawa nayi ba”
Taɓe baki tayi “Ba wani nan daman dai baka ɗauki abun da muhimmanci bane har akwai wani abun important da yafi nawa?”
Bayan ta ya shafa cikin daɗadɗiyar murya da yasan zata kashe mata jiki ya soma bata hak'uri kamar mai raɗa,
“Am so sorry Dear tuba nake muje yanzu mu zaɓa”
Kallon shi tayi kamar ta musa masa sai kuma taji ba zata iya ba, ganin hakan yasa ya rik'a hannunta suka nufi bedroom.
![](https://img.wattpad.com/cover/114548868-288-k951883.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
BABBAN GORO
RomansaNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...