BABI NA ARBA IN DA BAKWAI

4.6K 353 30
                                        


Sun daɗe suna kallon juna shi da Nasir kamin ya ɗauke kai ya kalli Mummy sai kuma ya saci kallon Kairat da ido sannan ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

“Samu guri ki zauna mummy”

Ya faɗa ba tare da ya sake kallonta ba, Kairat tayi musu kallon rashim fashimta

“Ta zauna kamar ya? ni ban gane nufin wannan abun da kuke kokarin yin ba ni dai na riga na aminta zan shayar da ita dan haka duk wata magana ku ajeta gefe”

Saif ya kalletaƙkamar a fusa ce

“Ki bamu guri Kairat ba dake zanyi magana ba wannan tsakanin ni da mummy ne”

Zatayi magana Mummy ta tari numfashinta

“Jeki ɗakin ki Kairat”

“Mummy...”

Sai kuma tayi shiru, tsaye tayi kamar ba zata ba sai dai kuma ba zata iya yin musu da Mummy ba, ba dan taso ba ta juya ta nufi hanyar ɗakinta. Bayan Mummy ta zauna Saif ya kalleta a natse ya soma magana

“Mummy kina da gaskiya na hana Kairat ta shayar da Lil Minal. ni kaina sai da nayi tunani na gano hakan dan haka nima ban bada goyon bayan ta shayar da ita ba.

   Sai dai kuma Mummy ba zan iya ba wata wanda ba Kairat ba ta shayar da Lil Minal saboda ban san halinta ba ban san ya addininta yake ba, kuma kinga ba wai zata shayar da ita kawai bane zata raine ta ne ta nuna mata tarbiya har na ɗan wani lokacin.
   Babu matar da na yarda da ita irin Kairat a yanzu, kuma ba zai yiyu ta shayar da ita tana budurwa ɓa dole sai tayi aure.

in kuwa haka ne toh ni nafi kowa cancantar na aureta tun da yata zata shayar sannan kuma ina son na rika ganin su karkashin kulawata kuma ta haka ne kawai zan iya cika wasiyar Minal hakan kuma ba zai taɓa samuwa ba sai da haɗin kanki da kuma amincewar Kairat ”

Tun da ya ɗauko magana Mummy tayi natsu tana saurarensa, shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗan daɗe kamin ta ɗago kai ta kalleshi

“Kayi tunani mai kyau Saif zan kuma goya maka baya ɗari bisa ɗari in har da zuciya ɗaya zaka yi. sai dai kuma ba zan cillas ta yin abunda bata so ba ba kuma zan hana ta abunda take so ba ina fatar ka fahimta”

Kai ya ɗaga mata

“Bana nufi hakan Mummy, ko kaɗan babu hakan cikin rai na kawai ina son kiyi shawara ne ke da ita ki kuma nuna mata abunda ya dace”

Yana kawai nan ya tashi tare da zuba hannayensa cikin Aljihu

“Na barki Lafiya Mummy sai naji daga gare ki”

Nasir da tun ɗazu mamaki ya kashe shi ya tashi shima yayi mata sallama ya fice.

    A Mota Nasir yayi ta yima Saif magana yaki ya amsa masa sai tukinsa yake har suka isa gida sai da yayi parking sannan ya kallesa

“Dan mi zakayi min haka Nasir? wannan ba shine karo na farko da kake min irin wannan katsa ƙandan ɗin ba ban san miyasa kake min haka ba!”

Tuntsurewa yayi da dariya

“Ba gashi ka faɗin abunda yake ran ka da kanka ba ni ai soso maka gurin da yake kaikayi ne kawai nayi. Kuma Saif in bakayi auren nan yanzu ba yaushe kake tunanin zakayi shi? kai fa ba yaro bane kasan abunda ya dace”

Saif dai bai sake ce masa komai ba ya buɗe Motar ya fice.
ganin haka yasa shima ya buɗe motar ya fita. a tare suka shiga parlour Nasir na ta jan Saif da maganar shi kuma ya masa shiru kamar ba dashi yake ba.
  Guri ya samu ya zauna yana kallon Momy dake kallonsu ya gaishe

“Momy an wuni lafiya?”

“Lafiya kalau ina kuka fito haka? tun ɗazu na aika a kira min kai akace ƙa fita”

BABBAN GOROWhere stories live. Discover now