NOT EDITED ⚠️
"Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan"
Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace
"Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...
A hankali ta ɗo ta kalli kwayar idonshi, suna haɗa ido gashin jikinta ya tashi, a hankali ta kawarda nata idon tace,
“Saif mi yasa kayi ma Minal haka? Mummy ta faďa min komai ita ma Minal ďin ta faďa min”
Yawu dake bakinsa ya haďe. ita kuma tayi masa kallon jiran amsa.
“Kaiyrat abunda Minal take yayi yawa abun ne ya dame ni shiyasa har nayi unkurin yi mata magana, abunda take ya tsa6a ma addini bata da wta rayuwa sai ta turawa ni kum sam bana jindaďin hakan”
“Saif ba kai kaďai ya dama ba dukan mu ya dame mu badan muna jindaďin abunda take muka saka mata ido ba,sai dan idan akan mata magana ko kuma kayi unkurin chanja mata rayuwa da karfin tuwo zai iya haifar mata da matsala, Saif da ba kai bane babu wadda ya isa ya tsaya gaban Mummy ya faďa ma Minal bakar magana. kai kaďai ka kai ka faďa ma Minal maganar da zata saka ta kuka ta kyale ka”
“Amman kinsan haramun ne a zuba mata ido tana yadda take so ko? kenan koda Sallah tace ba zatayi ba babu wadda zai iya yi mata magana ko?”
“Tana Sallah Saif Minal bata ta6a fashin sallah ba sai dai wani lokacin bata yinta a cikin lokaci duk wani aikin na ibada baya wuce Minal matsalar ta ďaya share share da kuma tufafin da take sakawa sai kuma rayuwar turawa da ta ďauka ta makalawa kanta kuma hkan ba zai rasa nasaba da zaman da tayi can kasashen turawan ba. Saif idan kana son ka chanja Minal dole ne ka fara nuna mata son duk abunda takeyi kamin ka nuna mata kin shi kai tsaye dole na ka jta jikinka ka nuna mata muhimmanci abunda kake so tayi kamin ka nuna mata illar wadda take yi a yanzu ki tsaye, zaka iya janta jikinka da kalamai masu daďi da kuma kulawa”
Wani murmushi yayi wadda ya fitar masa da beauty point.
“Taya kike ganin zan iya hawo kan Minal har ta daina abunda take bayan ke da kike da dangantaka da ita baki iya jan hankalinta ta daina?”
“Zata daina Saif just trust me and try zata iya canjawa a kanka bata bata canja a kaina ba saboda ni da kai a kwai babbanci kai Namiji ne ni kuma Mace ce zata iya daina akanka bata daina akaina ba”
“Ban fahimta ba toh miye banbanci n dake a gurinta.?”
“Zaka fahimta nan gaba. na gode da lokacinka da ka bani na barka lafiya”
Tana kaiwai nan ta tashi ta gyara yafin mafinta ta nufi kofa. Shima tashi yayi ya rufa mata baya suka fice tare. a bakin kofa ya tsaya yana kallonta har ta buďe motarta tana kokarin shiga ya kira ta,
“Kaiyrat”
A hankalin ta juyo ta kalleshi. Wani kyakkyawan Murmushi ya sakar mata,
“Thank you”
Itama murmushin ta mayar masa tana kaďa kai,
“Welcom.”
KAIRAT
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
ido ya tsura mata har ta zauna cikin motar, ta saka mata key tayi ribas tabar gidan. sai da mai gadi ya rufe gate ďin sannan ya juyo ya dawo cikin falon. Huda na ganinsa ta tashi ta nufi Upstairs, shikan bai ma kula da da kishi take ko wani abun ba dan hankalinshi baya gurinta. Kairat yake tunani da kalamanta, shi kan ta burge shi. _Gaskiya tana da hankali da tunani tunda har ta iya yin wannan maganar da wannan tunanin ai ita ma yar mai kuďin ce amman bata hali irin na minal kuma tayi karatun a waje itama, amman bata ďauki halinsu ba da yake tana da hankali kalli ko shigarta shigar musulmai koda yaushe zaka ganta cikin kamala gata black beauty_
Yana kokarin Zama yake wannan tunanin. (Ni kan nace Saif kodai an kamu🤔)
Huda kan tunda ta shiga ďaki ta kasa zaune ta kasa tsaye, sam hankalinta yake ya kwanta da ganin Kairat ďin da tayi. _toh miye tsakaninsu ? ina yasanta? miyasa yaje da sauri ya tarbeta ? miyasa ya koma can gefe suna magana ? ta lura da irin kallon da yake mata da kuma wadda ita ďin take masa kardai ace sonshi take! shin mima suka tattauna? _ Goshinta take bugu da karfi tana safa da marwa. daker ta samu ta zauna gefen gado still tana tunani. Kardai ace Saif sonta yake! kai bazai ta6a yiyuwa ba sai dai idan ita ďince take son jan hankalinsa dan ita bata yarda a kwai mace da mijinta zai iya so ba. toh mima ta rasa da har mijinta xai iya hango wata ? amman da yake mata yan iska ne aun iya jan ra'ayin mutun zasu iya bin ko wace hanya ganin sunja hankalin mijin ko dan mulki da kuďi da yake tattare dashi uwa uba kuma ga kyau. kai dole na ta gano abunda yake tsakaninsu dan daga ganin idon wannan Kairat ďin irin gogaggin karuwan nan ne na turai kai zama ba gannin ba dole ne nayi musu tsakani. tun kar tafiya tayi girma.
Tashi tayi zuciyar ta na bugawa da karfi ta nufi hanyar falo.