BABI NA TALATIN DA TARA

3.6K 371 6
                                    

BABBAN GORO

         NA

KHADEEJA CANDY

®
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

*39*

Shigowar masu mopping ne yasa shi farkawa, A hankali ya raba jikinsa da nata ya sauka saman gadon ba tare da ta farka ba, A masallacin dake asibitin yayi sallah, ba shi ya dawo ɗakin ba dai bakwai da rabi.
   Zaune ya tarar da Minal tana shan tea, Mummy na gefen ta zaune Kairat kuma na tsaye tana matsa mata kafafunta, ganin shi yasa Kairat haɗe fuska kamar taga mala'ikan mutuwa, Minal kuma kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai. Mummy ce kawai ta ɗan sakar masa Fuska,

“Saif....”

Yaji daɗi sosai hakan yasa shi risinawa har kasa ya gaishe ta

“Na'am Mummy an tashi lafiya?”

“Lafiya Kalau Mun gode sosai Dr ta faɗa mana Ka bada jini”

“Mummy miye abun godiya, Minal nayi ma fa ba wata ba”

Wani wawan kallo Kairat ta watsa masa,

“Ai dole ayi naka godiya tun da kasan Minal ba dolen ka bace yanzu .....”

Ya tari numfashinta

“Dole na ce Kairat idan banyi mata ba wa zanyi ma? Ni Allah ya ɗorawa hakkin yi mata komai matata ce idan ba ki san da wannan ba ki sani yanzu”

Zata sake cewa wani abun Mummy ta ɗaga mata hannu, hakan yasa ta jifa da kafar Minal ta fice a fusace,
 
“Kayi hakuri Saif kasan halin yara”

“Ba komai Mummy ni ya kamata na baku hakuri akan abunda nayi dan Allah ku yafe min”

Kamar mummy zata dake ce masa wani abun sai kuma ta tashi tsaye tana murmushi ta fice, a hankali ya ɗago ya kai dubansa gurin Minal dake kallonsa ya tashi yaje kuda da ita ya zauna har lokacin kallon shi take kamar mai jin tsoro ko kuma wanda bata yarda dashi ba, hakan yasa shi jin ba ɗaɗi hannu ya kai zai riko hannunta, da saurin ta janye hannun ta har tea dake a ɗayan hannunta ya zube, bai damu ba ya sake kai hannu ya riko hannun nata yana murzawa a hankali

“You hate me Minal right?”

Sai kuma ya ba kansa amsa

“Yes you hate me Minal a know”

Ita dai kallonshi kawai take bata ce masa uffan ba idonta na kwance da wani farin ruwa mai kamar hawaye kuma ba hawaye ba,

“Dan Allah Minal ki yafe min wallahi na gane kuskure na kuma yafiyar ki nake nema Minal na cutar da ke  na sani Minal na-”

Shigowar Nasir yasa shi katse maganar yasa hannu yana share hawayen da suka zubo masa,

“am sorry”

Ya juya zai fita, Saif yayi saurin dakatar da shi

“No Nasir shigo kawai”

Juyowa yayi yana murmushi

“Naji daɗin ganin ku haka Saif ina fatar ka gane kuskuren ka”

Shiru yayi kamar ba zaiyi magana ba, sai kallon Minal yake dake kallon Nasir tana motsa baki,

“Saif Dad yana son ganin ka”

Nan shiru yayi ya kai hannu yana shafa kan Minal, yasan matsalan ba zata wuce akan Huda ba ko kuma dukan da yayi ms Safiyyah shi kuma a yanzu ko ɗaya baya shakka dan yasan yana da gaskiya,

“Nasir kaje gani nan zuwa”

Ya faɗa ba tare daya kalleshi ba, Nasir bai tsaya jiran komai ba ya juya ya fice. Kallon kallo suke shi da Minal kowane da abunda yake karanta a idon ɗan'uwansa, Wani kalar yanayin yake ji kanta a ciki yanayin da ita kaɗai tasan me yake nufi, kasa ɗauke ido yayi daga kallon kwayar idon nata da yake tausayinta yake ji da kaunarta da begensa na kara kamashi, ganin hawaye sun zubo mata yasa shi saurin matsawa da faffaɗan kirjinsa ya rumgume ta yana sauke ajiyar zuciya, lumshe ido tayi hawayen suka cigaba da zubo mata tana kokarin raba jikinta da nashi kara kankanme ta yayi,

BABBAN GORODonde viven las historias. Descúbrelo ahora