Part ɗin Momy ya nufo, zuciyarsa cike da sake-sake saman kujera ya zauna yana shafa kansa, wani tunanin yazo masa, wayarsa ya duba ya shiga nema number Safiyyah, ya daɗe yana nazari kamin ya danna calling,
Dauke wayar yayi daga kunnensa bayan sun sanar masa da number tana kashe, Number Lubna ya kira ita kan ta shiga sai dai tayi ta ringing har ta kashe ba'a ɗauka ba, sai a kira na biyu ta ɗauka ta muryar bachi“Hello Yaya”
“Sauko gani nan parlour”
Yana faɗar hakan ya kashe wayar, yana mai cigaba da nazari, ta ɗaukar kamar minti biyar zuwa takwas sannan ta fito sanye da kayan bachi ta ɗora top sama, kusa dashi ta zauna tana hamma
“Yaya gani”
Kallonta yayi a natse
“Ya za'ayi naga Safiyyah yanzu? Kin san inda Gwaggo ta kai ta gurin magani?”
“A'a amman yanzu ai tana gidan Gwaggo kaje can zaka ganta”
“Sun dawo ne?”
“Eh sun dawo tun jiya ko shekaran jiya oh jiya, oh na dai mata amman taji sauki fa”
Gyara zamansa yayi cike da mamaki yace
“Taji sauki”
“Eh baka sani ba, maybe dan hankalin ka ba kwance ba yasa Momy bata faɗa maka ba amman taji sauki gaskiya”
Shiru yayi yana tunani,
“impossible”
Da karfi ya furta har Lubna ta kalleshi
“Lafiya yaya?”
Kallonta yayi
“Da gaske taji sauki kin ganta da idonki?”
Tashi yayi yana faɗin
“Lafiya kalau i need to see her”
A gaggauta ya fice daga parlour, da kallon mamaki Lubna ta bishi har ya fice sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, part ɗin sa ya koma ya ɗauki keys ɗin motarsa ya nufi parking space, yana shiga motarsa ya ɗauki hanyar da zata sada shi da gidan Gwaggon sa, a bakin gate ɗin gidan ya fara tsayawa yqna tunanin idan ya shiga me zai ce mata! Ka fara shiga ka fara gasgata zancen Luban tukuna, a nan ya danna horn, mai gadin ya buɗe masa, har kusa da kofar yayi parking, ya fito ya nufi kofar parlour, bell ɗin gidan ya tsaya bakin kofar yana kallon Windows ɗin parlour,
Sai da ya danna yafi a kirga sannan aka buɗe masa kofar, wata matashiyar yarinya ce sanye da uniform,“Ina kwana Yaya”
Bai tsaya amsa gaisuwar nata ba ya kunno kai cikin parlour yana faɗin
“Ina Gwaggo?”
“Tana ɗakinta bari na kira ta”
Ta faɗa bayan ta maida kofar ta rufe ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan tana karanta, kamin ta karasa Saif ya kirata
“No Farida zo ba sai kin kira ta ba”
Da wowa tayi tazo daidai shi ta tsaya,
“Gani Yaya”
Dukowa yayi tq yadda ita kaɗai zata iya jin mi yake faɗa yace
“Ina Safiyyah?”
“Tana ɗakin su Husna”
“Taji Sauki?”
“Eh taji sauki haukan ya cire”
Shiru yayi kamar mai nazari, sannan ya sake kallonta yace
“Samo min biro da Paper”
Da sauri ta juya nufi wani gurin da ina jin an tana deshi ne don aje bags dan bags ɗin suna da yawa, wata ja naga ta ɗauko ta nufo inda yake ta zauna ta bude ta fiddo littafi ta ɓalli paper ta ciro biro ya mika masa,
“Thanks”
Ya faɗa yana kokarin karɓa, a nan ya shiga rubutu a paper ya dunkule ya mika mata tare da bironta,
“Ga wannan ki ba Safiyyah idan ta tashi bachi kinji?”
“Toh tafiya zakayi?”
“Eh kice ma. Gwaggo ina gaida ta”
Yana kaiwa nan ya juya ya nufi kofar fita. Ya daɗe zaune cikin mota bayan ya isa gida, sai da lil Minal ta faɗo masa a rai sannan ya fita daga motar ya nufi Part ɗin sa, yadda ko yake tsammani haka ta tashi daga bachin sai kuka take tana kiran
“Mah mah mah”
Tana bursar da yawu, murmushin karfin hali yayi ya mika hannu ya ɗauke ta
“Yeee kin tashi yar mama”
Kara fashewa tayi da kuka, ya shiga jijjiga ta ya fito ya nufo part ɗin Momy, dinning ya nufa gurin da ya hango su Momy suna breakfast, Momy ta mika mata hannu
“Zo ki sha tea”
Juyar da fuskarta tayi ta kara fashewa da kuka, Saif ya ɗanyi Murmushi yaja kujera ya zauna yana faɗin
“Momy ina kwana”
Momy ta amsa cike da jindaɗin ganin yau ran nasa a sake ba kamar baya ba duk da idan ka kalleshi zaka gane yana cikin damuwa,
“Momy ai bata manta ɗorin da kika sa akayi mata ba”
Murmushi tayi, ta shiga haɗa ma Saif tea,
“Momy anjima Safiyyah zata zo ko da bana nan dan Allah a kira ni”
“Miya faru?”
Momy ta tambaya daidai lokacin da ta aje masa tea gabansa,
“Wai Safiyyah tana da hannu cikin rashin lafiyar Kairat shine nake son na tabbatar”
“Inji wa kuma wannnan wace irin magana ce haka”
“Nima haka tazo min sai dai ban tabbatar ba yanzu ne ake son na tabbatar”
Momy ta dafe kai
“Wannan abun har yaushe zai kare tsakanin ka da Safiyyah ne? Yarinyar nan daga samun lafiyar ta sai kuma ka ɓullon da wannan abun”
Bai ce komai ba ya kurɓa tea ya tashi yana faɗin
“Zanje Asibiti sai na dawo”
Momy bata ce masa komai ba har ya fice. Ba shi ya dawo gidan ba sai azahar duk da bai samu ganin Kairat ba dan basu barsu ya shiga ba ya window ya tsaya yana kallonta sannan ya dawo gida har lokacin lil minal na lake dake wanka ma daker ya samu ta sauka yayi, yana fitowa ta rarrafa ya ɗauke ta, ɗauke da ita ya saka tufafinsa mai ma bata barshi ya shafa ba turare kawai ya fesa ya fito ya nufo Part ɗin Momy, Mai aikin Momy ce ta karɓe ta da karfi wai za'ayi mata wanka, Saif ko yabi ya ɓata fuska dan baya son jin kukan lil minal ɗinsa, yana kokarin zama Lubna ya fito ɗaga ɗayan parlour tana leken ɗakin Momy har ta karaso kusa dashi ta zauna tana haki, shi dai kallonta yake har ta fara magana
“Yaya Safiyyah ta kira tace ba zata samu damar zuwa ba wai Gwaggo ta hana ta sai ta kara samun karfin jiki, amman Momy tace kar a faɗa maka”
Fuskar tunani yayi da mamaki, sai kuma ya shi da sauri Lubna ta rika hannunta
“Yaya karka ce nina faɗa maka Momy tace bata son tashin hankali, zata iya yi min faɗa”
“Ba zan bari taji ba”
“Toh ina zaka?”
“Gurin ta sai na tabbatar da abunda nake zargi ki kula min da Lil Minal please”
Bai tsaya jiran mi zata sake cewa ba ya fice.
VOUS LISEZ
BABBAN GORO
Roman d'amourNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...