BABI NA HANSI DA TAKWAS

3.8K 299 33
                                    


Kuka ta rika rusawa, jikinta har rawa yake, dukan su sai da idanunsu suka cika da kwallah, banda Saif da ya tafi wata duniyar ta tunani. Momy ta share hawayen idanunta ta kalli Safiyyah

"Ni na rai ne ki tun kina karama har kika girma ni nayi miki tarbiya na baki duk wata kulawa da kike bukata, amman ban nuna miki wannan hanyar ba baki tashi kika ga ina binta ba, miya kaiki aikata wannan mummunan aiki Safiyyah?"

Dagowa tayi ta kalleta

"Momy kin yi gaskiya baki nuna min irin wannan hanyar ba ban kuma ga kina binta ba, amman kece kika sani shiga wannan halin kika rufe ido kika kyale ɗanki yayi yadda yake so bayan kinsan ina sonsa kuma shi ne ya fara nuna min son tun farko,
. Nasan da ace nice bana sonsa da sai kin bi duk hanyar da kike ganin zata ɓulle ki aura masa ni amman da yake nice nake so sai kika rufe ido kika manta da halin da zan shiga"

Saukowa Momy tayi daga saman kujera zuwa kasa carpet, ta kama hannayen Safiyyah tana hawaye

"Ban taɓa jin banbanta ki da ɗan dana haifa ba, naso cillas ta Saif ya soki sai ya juya min baya Mahaifinsa kuma ta goya masa baya, kullum cikin ganin laifin sa nake, tun da kika kamu da wannan ciwon ban sake ganin farin Saif ba daga ni har mahaifinsa,
kuma saboda ke ne Safiyyah da ace ina da halin da zaki aure dana sa ya aure ki, ki daina zargina Safiyyah"

Lumshe ido tayi, tana wasu irin zafafan hawaye,

"Babu laifin Momy a ciki, ba kuma laifi na ko na wani wannan laifin kaddara ne, shin zaki iyaja da ita?"

Ba tare daya motsaa inda yake ba yayi mata wannan furucin, buɗe ido tayi ta kalleshi kamin tayi wata magana ya sauko saman kujera ya duka kasata yadda zata iya fuskantar shi,

"Ashe ke jahila ce Safiyyah, tunda kike ganin Momy zata iya yi miki abunda Allah baiyi miki ba, bayan nan kika tsallake kika je gurin wani boka yayi miki abunda Allah baiyi miki ba jin jahilci kaddara, kin kuma jahilci Allah, dan shine yadda ya so ga wanda ya so ga kuma wanda ya so tun lokacin da kika yi kulle kulle wa Minal bai isa ya nuna miki duk abunda ya samu mutun daga Allah bane, yanzu kuma sai kisa na aure ki dole jahila kawai"

A fusace yake mata maganar, har sai da taja baya tana sauke dogon numfashi, sannan ya kalli Momy yace

"Tashi muje Momy karki sake zubar da hawayen ki akan wannan"

Bai jira cewarta ba ko kuma tashin ta ba ya nufi kofar fita, Momy ta rik'a fuskar Safiyyah

"Miyasa kika faɗi wannan maganar Safiyyah? Miyasa baki rufa ma kanki asiri ba?"

"Saboda a yanzu na banbance tsakanin tsakuwa da hatsi, na kuma gane shayi ruwa ne, na gaji Momy lokacin kuka ya kare kunci da bakin cikin soyayya ya kare na shafe shafin Saif a zuciyata,
Na yarda da babu mai maka sai Allah Momy babu yadda banyi ba amman Saif yaki ya kula ni ma balle ya so ni, Momy na aikata abubuwa da yawa sanadin soyayyar Saif kuma gashi ban kai ga cin nasara ba, nayi sanadin shigar Minal cikin halin bak'in ciki, Soyayyar, kiyayyah, da kuma kishi abubuwa ne da suke rufa idon bawa, baya ji baya gani har sai ya aikata abunda zai aikata sannan ya gane kuskuren da yayi,
Na ɓata tsakanin ta da Saif, na ɓata tsakanin ta da Deen, kuma ta mutu ba tare da na nemi gafarar ta ba, na yaudari kai na da abubuwa da dama da zuciyata ta rika raya min kamar wani zai iya bani ba Allah ba, na cuci kaina na yi hasarar lokaci na ɓata tsakanin na da ubangiji na na kuma ɓata tsakani na da ku"

Kuka take sosai, Momy ma rungume ta tayi tana kukan, Gwaggo ma kukan take har da sarkewa.


*** *** ***
Kansa saman sitari yana sauke ajiyar zuciya, jin yake ya tsani Safiyyah sosai fiye da da, duk da wani ɓangare na zuciyarsa yana tuna masa da irin son da take masa, sai dai kuma abubuwan da ta bayyana masa yasa ya kara tsanarta tunawa da Minal ga kuma halin da Kairat take ciki yanzu. Ya dade cikin motar sannan ya fito jikinsa kamar a mace ya nufi cikin gidan, saman kujera ya zauna ya dafa kansa yana murzawa,
Sai da yayi awa uku da dawowa gidan sannan Momy da dawo fuskarta a kumbure alamar kuka tayi sosai, Lubna ce hankalinta ya tashi ganin Mahaifiyarta haka, gashi Saif ɗin ma tun da ya dawo baiyi ma kowa magana ba, kuma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa ta damu sosai, saɓanin Saif da tasan me ke faruwa, da kallo ya bi Momy har ta zauna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai yana cika ma bakinsa iska

"Ni Momy ban ga anfanin wannan damuwar da kike sa kanki ba, wannan yarinyar bata da tunani kuma wallahi duk abunda ya samu mata ta sai na raina mata hankali"

"Kai ma ka yarda tana iya yi mata abunda Allah bai yi mata ba kenan"

Kan Momy a kasa take masa maganar, Lubna na zaune kusa da ita cikin da rashin fahimta idan ta kalli Momy ta kalli Saif. Kai ya girgiza

"Aa Momy ni ban yarda da wannan ba, kawai dai ita ce sanadi tun har ta faɗa da kanta"

"Kamar yadda ka zamo mata sanadin shiga halin da ta shiga ko?"

"Oh Momy ki daina shigar mata, kina son shafi laifinta ba, bata gurbi abunda ta shuka ba sai nan gaba"

Tashi yayi yasa hannayensa aljihu, ya nufi kofa

"Karka fasa kwalɓar nan Saif karka sake jefata cikin wani hali"

Tsayawa yayi cak, ba tare da ya juyo ba yace

"Ban jefa ta ba Momy ba kuma zan jefa ta ba, ita dai ta jefa kanta"

"Tun lokacin dana fara haɗuwa da Minal Kairat ce ka fara labarta min, sai kuma gashi kazo min da maganar Minal har ka aure hankalin ka bai kwanta ba har sai da ka auri Kairat, yanzu kuma ta kamu da rashin lafiya duk kabi ka fita hayyacinka har kana kokarin ɓatawa da yar'uwarka,
Nasan Kairat tayi maka hallacin tun da ta shayar da lil Minal kuma yanzu tana ɗauke da wani cikin naka, amman ina son kasan wani abu guda ɗaya, Ana chanja mata ba'a chanja yar'uwa ba shin yanzu idan ka rasa Kairat yaya zaka ji?"

Juyowa yayi da sauri ya kalleta, kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya haɗiye maganar, tare da numfashin sa, sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi

"Haka zaka misalata yadda Safiyyah take ji a ranta baka da tausayi Saif ka canja kwatakwata kamar ba kai ba kana son kanka da yawa babu ruwanka da damuwar kowa sai taka zuciyarka ta mace! Tirr da irin son da kake yima Kairat tirr da son da xai rufe maka ido ka kasa ganin kowa sai ita kaji tsoron ranar da sonta zai wahalar da kai hakkin Safiyyah ya dawo kanka!"

Tunda ta soma maganar ya dinga jinta gan gan gan kamar ana sara masa gatari aka, sam bai zaci wannan maganar daga Mahaifiyarsa ba, tun tashin ta Momy bata taɓa faɗa masa wata magana makamanciyar wannan ba, amman a yau ta faɗa masa saboda Safiyyah, tsabbas ranta a ɓace yake yake dan har cikin makoshinta furucin ke fitowa,
Wani dogon Numfashi Lubna ta sauke zuciyarta na bugawa da karfi ta kalli Momy ta kalli Saif, Shima kallonta yayi ya kalli Momy sai ya ɗauke kai ya fice.
Wata tafiya ce yake mai kamar sauri-sauri kuma ba sauri ba, kallo ɗaya zaka yi ma fuskarsa ka fahimci tafiyar ɓacin rai ce yake, yadda ya bar gida sai da hankalin securities ɗin ya tashi, haka ya hau tt yana wani irin gudu kamar dansa kawai aka shinfiɗa titin, kamar wani ifiritu haka ya isa gidansa cikin kankanen lokaci. Har ya zauna maganar Momy ce take masa yawo a kai, tashi yayi ya nufi firjin ya bude ya ɗauki robar ruwa ya ɗaga kansa ya kafa kai, da wani irin karfi yake shan su, sai da ya kusa shaye wa sannan ya sauke kansa yana maida numfashi da karfi, ya jefar da kwalbar, saman kujera ya dawo ya ya zauna ya lumshe ido,har na kusan na mintuna talatin, can kuma ya buɗe ido da sauri kamar wanda ya tuna da wani abu ya tashi ya fito harabar gidan, ma'aikatan gidan ya fara kwalama kira, jiki na rawa suka iso cikin girmamawa, ɗaya daga cikin su ya kalla ya nuna masa gefen da itacen gidan suke

"Can nake son kuje kuyi ta binciko min wata kwalba, tana nan cikin kasa ku duba da kyau karku ce min baku ganta ba"

Da "Toh" suka amsa suka nufi gurin shi kuma ya juya ya dawo falon ya zauna, yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana matsa gashin.
Bayan kamar minti arba'in, aka kwankwaso kofar parlour, ya ɗan daɗe kamin ya bada izinin shiga

"Yes"

Turo kofar akayi aka shigo, hannunsa rike da kwalbar mai cike da hayaki, ya mika masa

"Ga abunda muka gani"

A hankali ya buɗe ido ya sauke su kan kwalbar, da ido yayi masa nuni daya aje ta saman tebur ɗin dake kusa dashi, yana ajewa ya juya ya fice.
Kwalbar ya tsura ma ido, yana taɓa hancinsa kamar mai tunani, zuwa can ya tashi daga gimciren da yake still yana kallon kwalbar, sai da yayi bismillah sannan ya kai hannu ya rik'a kwalbar ya ɗaga sama yana kare mata kallo, wani abu ne a ciki mai kamar hayaki kamar toka da wani abu kasanta ja kamar ruwa jini,
Bismillah ya sake yi ya cira kwalbar iya karfinsa ya buga kasa, a nan take kwalbar ta watse.

BABBAN GOROHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin