BABI NA ARBA IN DA BIYAR

4.6K 394 23
                                    

Sululu ta fito ɗakin, fuskarta ba yabo ba fallasa, tana tafe tana murza yatsun hannunta har ta shiga parlour, idonta a kasa ta risina

“Hajiya zan tafi kar Mummy ta tashi bata gan ni ba

“Me kika je yi gurin Abbah ko Mummy ce ta aike ki?”

Kamin Hajiya tayi magana Zainab ta aika mata tambayar tana mata kallon kul. Daga duken da take ta amsa mata

Abunda Ya take zuwa yi gurin Mahaifinta

Zainab ta tsire baki

“Au rashin kunya zaki yi min daga tambaya Allah Mama idan baki tasar ma yarinyar nan ba irin tarbiyar Minal zata koya tunda uwar rikon su ɗaya, kinga ysrinya na kokarin min rashin kunya

Ta karasa faɗa yana kallon Hajiya Suwaiba, ɗagowa Kairat tayi ta kalli Zainab cike da ɓacin rai

Minal.dai bata duniyar Mummy kuma ba abokiyar wasar ki bace

“Au iskanci zaki min tunda na taɓo uwarki ko?”

Hajiya Suwaiba ta kalleta

Wai miyasa kike haka ne, Salamatu warin ki ce? ko da kika buɗe ido kin ganta a cikin gidan nan amman baki da marainiya sai ita!”

A tsawace take mata maganar tana hararar ta, tsire baki tayi

Ni wallahi bana son ta kwata-kwata tun tashi na ni rayuwarta bata min sam

Hajiya ta watsa mata harara

Tunda baki sonta ai sai ki kashe ta marar kunya kawai

BABBAN GOROWhere stories live. Discover now