BABI NA ASIRIN DA BIYAR

3.4K 289 1
                                    

BABBAN GORO

      NA

KHADEEJA CANDY

Candynovels.wordpress.com

WATTPAD @khadeeja_candy

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*25*

Numbar Momi ta kira, Bugu biyu aka ɗauka. jikina na rawa tace

“Hello Momi ina wuni”

“Ba momi bace Safiya ce momi tana part ďin Dad lafiya naji muyarki haka.?”

“Ba lafiya ba Safiyya wai kina da labarin Saif aure zaiyi.?”

“Allah sarki kardai kice min sai yanzu kika sani bayan saura sati ďaya a ďaura musu aure”

“Naji amman ban tabbatar ba sai yanzu dan ni a tunani na bada gaske bane sai yanzu da ya kawo min kayan faďar lefe wai saura sati biyu a ďaura masa aure”

“Toh ya rage miki ne saboda kiga kishiya ba zata wallahi anty da ba Yayana bane da nace azzalumin ace duk zaman da kukayi ya rasa da me zai saka miki sai kishiya, kishiya kuma irin wannan yar shaye shaye karuwa kuma shegiya hmmm namiji kenan”

Fashewa Huda tayi da kuka,

“Wallahi Safiya da ace a mafarki ne aka ce min Saif zaiyi aure bazan yarda ba amman yanzu wai har shi da kansa yake faďa min”

“Kuma kinsan wani abun haushi su Momi da Dad suka goya masa baya sam ni hakan bai min daďi ba dan ni tun lokacin da aka ce yarinyar nan tayi unkurin hallaka kanta naji na tsaneta, shiyasa naje har gidansu nayi mata wankin babban bargo data faďa masa yazo gida dukanane kawai baiyi ba amman sai kinga yadda yake tada jijiyar wuya akanta ita kuma Momi ta goya masa baya”

Cikin muryar kuka Huda tace,

“Wallahi Safiya ban yi zaton Momi zata goya masa baya ba ya aureta mace haka”

“Hmm ai duk goya masa baya sukayi nice kawai nayi masa magana ina nuna masa illolinta sai yace min wai shima tausayinta yake gani kuma idan bai aureta ba hankalinsa bazai kwanta ba wai yaci amanar ta jifa ke har Nasir goya masa baya yayi gurin aurenta wannan yarinyar ta tsafe kowa nice kawai bata samu sa'ah kuma nafi karfinta”

Kasa magana Huda tayi sai kuka take, tana murje murje kasan karfin, hankalinta ne ya kara tashin jin ance kowa ya goya masa bayan yayi wannan auren,

“Oh ji min Anty Huda wai kuka kike ne! Allah sarki ni ina ganin laifin mata masu kuka akan kishiya name a a wallahi bazan wahalar da rayuwa taba”

Daker ta iya furta,

“Safiya hankalin Saif ya riga ya gama tafiya gurin yarinyar nan kwata kwata yanzu baya kulani gashi sai zagin iyayena yake yana cimin mutunci shiyasa ma na kira na faďawa Momi ina cikin matsala Safiyyah”

“Ke ďan Allah ki daina zubarda hawayenki akan wata yar iska, ai akan wannan yarinyar komai sai iya yi miki dan ta riga tayi masa magani amman kinsan wani abun ba ai idan tasan wata bata san wata ba indai magani ne tayi ni kuma zanyi mata makirci wadda yafi magani”

Tashi Huda tayi zaune, tasa hannu tana share hawayenta

“Me kike nufi Safiyyah zaki taimake ni ne?”

“Ae taimako kan zanyi miki zan yima kaina da duk family mu dan wannan da kika gani da kowa zata iya raba shi kuma tunda nace bana sonta bana sonta sai na hana auren ta da Yaya”

Wani sanyi sanyi Huda ta fara ji, cikin zuciyarta wadda bai gama hawa saman fuskarta taba,

“Mi zakiyi Safiyyah.? wallahi da kin taimaka min daman nasan duk cikin family ku babu mai sona irinki”

“Yanzu ne zan nuna miki so Huda sai na hana ta zama gidan Yaya kota halin yaya keda yaya kuma mutu kan raba, ai daman ance mai laya kiyayi mai zamani kuma BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,in dai ita takamarta magani ni kuma zan nuna mata zamani da boko da kuma kalar barinki da bata sanshi ba”

Wannan karon Dariya Huda tayi,

“Amman wallahi da kin faranta min rai kin cire min damuwata”

“Hmmm kawai kisa ido kiyi kallo, ke dai daga yanzu ki daina nuna masa kishi da haukar nan ta mata ki bishi kar kuma ki sake kiran Momi da sunan yi mata sheidair wani wani sau da kafa sauran bayani sai gobe idan nazo.”

Tana kaiwa nan ta katse kiran, da sauri Huda ta kalli wayar tana buďar baki da fuskar mamaki,

“Ikon Allah daman ance duniya mai faďi abunda ka sani shi ka sani wadda baka sani ba baka sanshi ba ashe Safiyya mace ce”

Abunda ta faďa kenan tana kokarin tashi tsaye,da nufin komawa saman gado ta zauna.

                    ******        ******       ****

MINAL.................
  Safa da marwa kawai take cikin falon, tana busar da iskar baki. Tun kairat na kallonta har ta gaji tayi mata magana,

“Wai lafiyarki Sis kike wannan yawon haka.?”

Da sauri tazo kusa da ita ta zauna, fuskarta cike da tsananin damuwa tace

“Sis Deen ne nayi da kiran wayrsa bai ďauka ba daga karshe ma sai kashewa yayi har yanzu fushi yake dani ya kasa fahimta ta”

Wani dogon tsaki Kairat taja,

“Deen! Deen!! Deen!!! haba Minal miyasa ba zaki aje shi a inda ya aje ki ba har yashe zaki fita harkar sa ne aure fa zakiyi kuma ke da kanki kike faďa min Saif yace kiyi masa alkawarin ba zaki kara kula sa ba  yanxu Deen ďin nan ya fita harkar ki ai kodan haka yaci ace kema kin kyale shi”

Tashi tayi tsaye a fusace, ta nufi hanyar Upstairs tana faďin,

“Ai daman nasan ke ba fahimta zakiyi ba, shekarar mu nawa tare yanzu yana fushi dani ace bazan bashi hakuri ba, ko an faďa miki abota karya ce shashasha kawai”

Da ido kawai Kairat ta bita tana kaďa kai,

“She kenan kije yi ta yin abunda kike ganin yafi miki wadda bai ji bari ba yaji hoho”


                     **********************

“Amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan natsattsen matashi”

A hankali ya ďago kai ya kalleta. a nan ta cire katon bakin gilashin dake makalle idonta cikin tattausan lafazi tace,

“Sarki ya tabbata ga Ubangijin wannan halittar,
Hakika kana da kyau, da kwagiji kana da cikar kamala da sanya zuciyar yan mata faďuwa, babu wata mace zaka ce kana sonta ta kika sai idan tana da wata manufar ne da daban,
   Mutum ne kai mai rikon amana wadda har hakan yasa Minal ta aminta da kai kai kuma ka bata kanka ka zamo mata raqumi tana jan akalar daga karshe tace amanar ka, wadda ko kwankwanto babau nasan zaman da kayi a wannan gurin ita kake tunani”

Kallon natsuwa yayi mata, shidai bai ta6a ganinta ba sai dai fuskarta tayi masa kamada fuskar wadda da yasani,

“Wacece ke.?”

Ya tambaya yana mata wani kallo, idonsa a jawur kamar wadda yayi shaye-shaye, murmushi ta sakar mashi sannan tace,

“Sunana SAFIYYAH BASHIR BATURE kanwa gurin SAIF BASHIR BATURE zan iya zama.?”

_Safiyyah Bashir Bature_  cikin zuciyarsa ya maimaita sunanan yana kallon mutanen dake zaune gurin shakatarwa kamar mai neman wani.

VOTE

BABBAN GOROWo Geschichten leben. Entdecke jetzt