*🥀🥀🥀RAYUWAR AURENA🥀🥀🥀* *NA* *HAFSAT_M_S* ✍🏻 *page*

2.2K 118 0
                                    

*🥀🥀🥀RAYUWAR AURENA🥀🥀🥀*


        *NA*

*HAFSAT_M_S* ✍🏻

*page*
       *13*

*ASSALAMA ALAIKUM Yaku yan uwa musulmai bari nayi amfani da wannan damar wajan tunatar daku falala mai girma ta salatin Annabi (saw) Watarana mala'iku guda huďu sukazo wajan manzon Allah (saw), mala'ika JIBIRILU yacewa Annabi duk wanda yayi maka salati goma 10 to ni zan kama hannun sa na ketare dashi akan siraďi ranar tashin Alķiyama,mala'ika MIKA'ILU yace ni kuma zan shayar dashi ruwan Alkausar, mala'ika ISRA'FILU yace ni kuma zanyi sujjada gaban Alllah bazan tasoba har sai Allah yagafarta masa mala'ika AZARA'ILU yace ni kuma zan zare masa ransa cikin sauki kamar yanda nake zare na Annabawa ,Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar ya Allah ka ķarawa Annabi daraja da ďaukaka da matsayi a ranar tashin Alķiyama Allahumma salli wasallim ala khatimil Anbiya'i wa imamul mursalina.*🙏🏿🙏🏿🙏🏿


Zuciyar sane yafara dukan uku uku dama kamar yasan za'ayi haka,"

"Nace auran gidan uban ka zaka qara? Umma taqara maimaitawa bayan ta iso inda suke,"""
shiru yayi ya rasa amsar daa zai bata,"

badakai nake magana ka min shiru,"

Kansa ya ďago ya kalle ta yace "Haba Umma kefa kike cewa in qara aure kullum bakida wata magana sai na in qara aure yanzu kuma nace zanyi auran kuma kinaso ki nuna bakisan da zancan ba,"

kallon banza tayi mishi tace Eh nasan nice mai ce maka ka qara aure Amman yanzu na fasa, tunda ba wacce nakeso zaka aura ba,

Abba ne yayi gyaran murya yace ke bara'atu wannan wani irin sakarci kikeson nunawa?,"" dole ne sai ya auri wanda kikeso?," ko kece zaki zauna masa da ita?"" to buďe kunnen ki ki saurareni tun wuri kibar yaron nan ya auri wacce yakeso tunda ba'a kanki zasu zauna ba, kinji nagaya miki,"

Haba alhaji ya zakace haka indai wacce yakeso ne ai nabar shi ya aura, in banda walaqanci irin nashi ga mace kamila tana son shi Amman ya tsaya yana ruwan ķafa akan wasu yan iska,"

Idan ma rashin karatu ne ai gashi tanayi yanzu," to nidai harga Allah bazan laminta wannan karon ma ya watsa min qasa a ido ba, ko ya auri suwaiba ko kuma na hanashi auran wata, nayi haquri a wancan lokacin Amman yanzu haquri na ya qare dole ne ya auri suwaiba ko afasa auran gaba ďaya,"""tana gama faďin haka ta juyar da kanta gefe tana girgiza ķafa ďaya alaman ranta yabàci,"

Abba yace to shikenan bara'au kiyita jayayya dani, yayi miki kyau," kafin ya juya gun Abdulmalik yace babana faďa min yar gidan wanene kuma daga ina take,"

Ajiyan zuciya ya sauķe tare da kai kanshi qasa yace Abba sunan ta Aisha humaira mahaifin ta  alhaji Ali girema ďan siyasa ne a maiduguri Amman dai abuja suke zama,"

Umma ta jiyo da kai tace Amman Abdulmalik bakada hankali, yanzu ace duk yan matan nan da suke cikin faďin garin katsina karasa wacce idon ka zai kalla yaso sai yar maiduguri?",

Hannu ta ďaga ta nuna shi da yatsa tace to bari kaji wlh wlh kaji dai na rantse maka auran yar maiduguri ba'a cikin dangin nan ba, kuma bazanyi kaffara ba," tana kaiwa nan ta kabè zanin ta tabar parlon tana bambami ita ďaya har ta isa bàngaran ta,"

Nauyayyan numfashi Abba sauķe yana mamakin masifa irin nata," dakewa yayi yace da Abdulmalik, babana karka samu damuwa akan maganganun mahaifiyar ka barni da ita, insha Allahu da kaina zan tafi abuja na nema maka auran ta in har na yaba da halin ta, tashi katafi abunka,"

Tashi yayi jikin sa babu ķwari yana ma Abban nashi godiya yabar parloun, yau kam ko ďakin inna bai leqa ba dan ji yake gaba ďaya maganganu umma ta ruďashi, meyasa takeso tayi mishi wannan hukuncin tana nufin kenan har mata uku zaiyi, kai inaa da sake daga humaira sai humaira babu wani mahaluķin da zai mallake min gurbin ta a zuciya na, haka yaci gaba da surutan sa shi ďaya har ya fice a gidan zuciyar sa tunkushe da abubuwa iri iri,"

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now