🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*
*Page*
*74*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*A falo suka yada zango, inda TV keta faman aikinsa shi kad'ai, a lokacin ana neman k'arfe taran dare. Yana zaune bisa doguwar kujera, tayi matashi da cinyarsa, ko wan-nansu yana cikin shirinsa na kayan bacci, hannunsa dake kan gashinta yana shafawa a hankali.
"Matar, ni kam yaushe za'a d'an min dakon babynah ne?". Cikin sigar zolaya ya yi mata tambayar, bayan ya d'auki wayarsa yana latsawa.
"Himm! Me kake ci nabaka na zuba? Ai Kada ka damu indai wannan zancen ne, ko gobe ma zan iy d'auka, ai ba abu mai bak'ar wahala bane"."Haba! Da gaske?".
"Da gaske mana, tunda nice zan bawa kaina". Ta mayar masa da amsar tambayansa, game da jefa masa harara ta sigar wasa.
"Ya dai kamata ki hanzarta, dan gaskiya ina k'aunar ganin yarona"."Ai fa! Kai kam ka bar damuwa, kawai zuwa gobe kasa tsammani, zaka ji..." Ta kashe masa idanunta d'aya, had'e da d'age gashin saman giranta.
"To shi ke nan, Allah yasa hakan, duk da dai nasan kina fa fad'a min ne cikin sigar wasa, domin ban mance da bayanin Doctor Ibrahim ba, na cewa mahaifarki ta samu matsala, haifuwa yanzu dakyar ne, sai in kuma wani ikon Allah".
Maganar tasa tayi matuk'ar sosa mata rai, amman gudun jan wata magana yasa ta basar, kasancewar tasan silar faruwar hakan, ba zata musa masa ba, dan ba k'aramin rauni suka ji mata a ciki ba.
"Yoo kuma kasan da wannan zancen amman kake irin tambayar nan?" Ta fad'a tana mai kallonsa. "Eh, amman ai Allah yana amfani ne da abinda ke aiki a cikin zukatarmu, so kinga ko gobe kamar yanda kika ce, ko hala yau ma, zaki iya d'auka".
"To na ji, yanzu dai a bar zancen, ni bacci ma nake ji, sai da safe". Ta k'arashe maganar a ya yinda take mik'ewa tsaye.
Tashi ya yi shima yace baccin zaiyi, su shiga su kwanta, bayan su kashe komai na falon, sannan suka wuce d'akinsu na bacci.
Washe gari da safe, suna zaune a dining table suna karin kumullo cikin raha.
Shi ne ya soma gama cin abincin sannan ita, kafin ta kwashe wajan ya wuce d'akinsa ya yi shirin fita."Fita zaka yi ne?". Ta tambayesa. "Eh wallahi akwai wani abunda zanje inyi a office ne, amman ba zan jima ba zan dawo, dan kinsan yau Lahadi rana ce ta hutu".
"Hakane kam ranka shi dad'e a dawo cikin k'oshin lafiya".
"Amen-Amen ya Rabb". Ya amsa mata yana mai shirin ficewa, yana daf da bakin k'ofar falon da zai sada shi da haraban gidan, ya dawo da baya zuwa gareta, a hankali taga yasa hannunsa bisa kan idonta na gefen dama, ya wangale shi yana duba cikinsa, ba tace da shi k'ala ba ya kai hannunsa kan d'ayan idon, shima ya wangale yana duba cikinsa, sannan ya dawo kan tafukan hannunta yana dubawa, kai ta kad'a cike da mamakinsa tace
"Haba! Meye shi haka kake ta min dube-dube a jikina? Sai kace wani sabon likita".
"Dubawa nake inga ko yau kin d'auki cikin, ko hakan da na yi nada lefi?".
"A-a babu, ba ka da lefi Doctor Abdool, tunda ce maka akayi ina d'auke da ciki".
"Shi ke nan, wannan sunan da kika sa min ta yi". Ya fad'a yana dariya."Dan Allah ka tafi haka-nan, ya isa wannan was..." Ba ta iya ta k'arashe maganar ba, ta ji wani irin hajijiya ya d'ibeta, kad'an ta fad'i k'asa yayi gaggawar cafketa, cikin damuwa ya shiga jijjigata yana tambayarta meke damunta, ganin ta gagara basa amsa, hakan yasa ya fita da ita harabar gidan ya shigarta cikin Mota, sannan ya dawo d'aki ya d'auka mata hijabi ya kulle k'ofar falon, kafin ya dawo Motar ya sameta tana sauk'ar da numfashi.
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,