🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M* *Page*

1.2K 57 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀

        *NA*

*HAFSAT_M*

*Page*

        *54*

Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*





"Yau lahadi ya kasance itace da karbàn girki, ganin irin yanda har izuwa wannan lokakin bayan faruwan wannan lamarin yana cikin fishi da ita bai daina ba baya sakar mata da fuska saima a duk lokacin da ta tun kareshi tamkar qara ingiza shi akeyi akanta sai ya haura  mata da bambami tamkar bashi ba idan ya soma mata faďa, dan haka yasa yau ta ďauki alwashin cewa saidai suyita taqare yau ko ita ko shi dan tagaji da zaman haquri irin wannan."

  "Tun safe bayan ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallan asuba ta shiga yin gyare gyaren ta da tasaba yi dan yanda takejin jikinta yanzu yagama warkewa wasai takejin kanta tamkar ba ita bace tayi kwanciyar kusan sati biyu a gadon asibiti ba."

    "Haka tayi ta aikin ta ita ďaya ba ruwan ta da shiga safgar Maraqishiya ko hanya bata bari sun haďa ba bare har wani yace ma wani qala." bayan ta kammala da duk abunda zatayi ne tasamu gado ta kwanta bayan tayi sallan azahar dan yanda taji bacci na rufe mata ido tamkar wacce ta kwana batayi bacci ba."

    "Kafin baccin ya ďauketa ne ta ďauki wayar ta dake ajiye kusa da ita, tashiga qiran Mummyn ta, baifi ringing biyu ba taji mummy ta amsa wayar" cikin murmushi ta qara wayar bisa kunnenta, suka shiga gaisawa."

     "Saida ta dauki tsawon lokacin tana hira ita da mummy Amman ko kaďan har yau batayi gigin sanar da mummy abunda yafaru da ita ba, dama tasan basusan tanada ciki ba tunda ita babu wanda tasanar wa inbanda Amina."
    "Bayan tayi sallama da mummy taqira Abbanta shima suka gaisa yana mai tambayar lfyr ta, ta amsa masa da lfy lau."
   "Suna gama gaisawa tayi mishi sallama kafin ta kashe wayar taqira na Yaa mahmud shima suka shiga gaisawa."
    "Baccin takeji  sosai Amman Haka tabi duk wayancin yan uwanta wanda suka kwana biyu basuyi waya ba ta gaggaisa dasu a qarshe taqira Ameena."

   "Bayan ta kammala da wayan ne ta ajiye shi a gefen ta tareda rufe idanunta cikin zuciyar ta tana haďe haďen yanda zata fuskance shi zuwa anjima idan ya dawo,"
   "Tana cikin zancen zuci bacci mai nauyi ya kwashe ta bata sani ba sai wajan karfe biyar ta farka tana miqa tareda karanto salati" kwalalo idanu waje tayi cikin firgici tamkar wacce taga baķin dodo sanadiyar ganin agogo da tayi har yamma tayi batayi sallah ba."
    "Cikin hanzari batare da bàta lokaci ba ta miqe tsaye ta shige toilet ta ďauro alwala ta tashar da sallah, bayan ta idar ne ta gyara zaman ta a wajan tana tasbihi ta shige cikin duniyar tunanin ta da baya qarewa dan ba abinci zata ďaura bats  ."

**

Da daddare wajan misalin karfe tara ya shigo cikin gidan a gajiye kai tsaye ďakin sa ya wuce, bai tsaya yin komai ba ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ďaure da towel a kunkumin sa" Yana cikin tsane ruwan dake jikinsa ta turo ķofar ďakin ta shigo baķinta dauke da sallama cikin shigar kayan bacci wanda ya mata kyau ajiki, daddaďan ķàmshin turare na tashi ajikinta, hannunta riqe da tray na shayi da samosa a gefen sa" cikin qasa da murya taji ya amsa mata sallaman yanaci gaba da goge ruwan dake jikinsa batare da ya kalle ta ba dama batayi zaton hakan daga garesa ba."
    "A hankali bayan ta ajiye abunda ke hannunta cikin sanďa ta tako da ķafafun ta zuwa garesa zuciyar ta na bugawa dum dum tasa hannayenta duk biyu ta rungume shi ta baya tsam ajikinta ta runtse idanunta gam."

    "Tsigar jikinsa ne yaji ya tashi yanda yaji ta matse shi tamkar wanda aka za'a kwace mata shi yanajin sauķar numfashin ta tabayan sa, ba makawa tabbas yayi kewar ta sosai yana begen ta cikin ransa saidai zuciyar sa yakasa yarda da ita, a duk lokacin da yafara saukowa yanaso ya manta da abunda yafaru sai abun ya faskara da zaran ya tuna da babynsa sai yaji yaqara shiga tsantsan baķin ciki marar misaltuwa, Allah yagani yanason  haifuwa Amman gashi bai samuba."

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now