🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀 🥀 *NA* *HAFSAT_M_S* ✍🏻 *7*~ *

4.7K 172 2
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀 🥀


       *NA*

*HAFSAT_M_S*  ✍🏻
(Preety_hammud)

*7*~ *8*

Dedicated to my besty
AISHA GENTLY LADY


A hankali suke  bibiyar motar batare da mai shi ya fahimci binsa ake ba, kasancewar cikin dabara yake taka masa baya haka nan suketa ratsa kyawawan gidaje dake jere a cikin unguwar, A wani babban gida sukaga tsayawar motar mai gadi ya buďe masa ya shiga,"

Ganin haka yasa shi jan nashi motar zuwa gefen kwaltan dake layin yayi parkin ďin motar nasa , kafin ya, kwantar da kan sa ajikin kujeran yayi matashi da hannayen sa duka biyu ya lumshe idon sa murmushi sauķe a fuskan sa yana hango ta cikin kwakwalwar sa sanda take masa tsiwa da ďan madaidaicin bakin ta, qara gyara zaman nasa yayi akaro na biyu murmushi ta ķubùce masa da hango Kyakkyawar gashin kanta mai sheqi baki siďik da yayi ,"kallo ďaya tak zaka masa ka fahimci cewa yana cikin nishaďi," muryan haisam yaji kamar daga sama shi dayawo dashi daga duniyar da ya wula,"

Kutuma ķur'anin Allah Abdulmalik kamayar dani ďan iska, sanin kanka ne inada inda zanje Amma ka kama ka ďauko mu inda ba'a san da ķurar ka ba, to billahil azim wannan gadaran ta isheni nabar ka lfy zan qarasa gida da taxi, idan kagama banzan tunanin da ya kawo ka kasame ni a gida, yana kaiwa nan ya buďe motar yayi ficewar sa, ran sa in yayi dubu ya bàci dan tun suna bibiyar motar yake masa mita Amma yayi banza dashi shiyasa yaga idan ya biyesa sai ayi magariba basu bar unguwar ba,

Ajiyan zuciya ya sauķe tare da shafo sajen fuskar sa, bayan yagama sauraron ķorafin haisam, Murmushi yasaki tare da girgiza kai ya tada motar yabi bayan shi,,""" Hango sa yayi ya tsaida taxi zai shiga hakan ya sanya yayi gaggawar isa gareshi..glss ďin motar ya sauķe, ya ďago kai ya kalle shi,yace,"

Haba abokina miye na zuciya akan wani abu qalilan kamar ba dangin mazaje ba hakan na nuna ragwanci nefa Abdulmalik yace da haisam ta fuskan zolaya tare da kinne masa ido ďaya yana masa  dariya dan yanda yaga ya takura fuska,"

Tsaki yaja tare da buďe motar ya shiga kafin yace ai kai zan cewa ragon namiji wlh Abdulmalik kabani kunya wlh mace guda ďaya tilo  ta susutaka harda biyo ta unguwar su saikace asirce ka tayi duk kabi ka ďaga hankalin ka akanta wlh ko Maraqishiya ni banga kayi wannan ruwan ķafa haka akan ta ba,,ai ko mayya ce ta kamaka iya kaci kenan,"cikin bàcin rai yake maganar,,"

Ganin mitar nasa bana qarewa bane, hakan yasa Abdulmalik girgiza kai baice dashi uffan ba dan yaga alama ransa ya matukar bàci sosai tada motar yayi  sukabar unguwar

*************

Zaune take a parlou ita ďaya kasancewar yau gidan nasu ba kowa Abba ya fita office yau tun safe  mahmud kuma yaje gun aikin sa mumy ma fita tayi bayan gari yagama waye wa gidan aminiyarta  hajiya fatema, kan maganar walimar auran ďanta sufiyan wanda za'a gabatar gobe, tayi tayi da  humaira ta rakata dan ta gaishe da hajiya fateman da yake kullum idan sun haďu saita tambaye ta, Amman fur taqi,

Ita kuwa ba qaramin tsanan zuwa gidan tayi ba sakamakon maganganun da sufiyan ďin ke  mata tun wani lokaci da mumy ta aike gidan da yake unguwa ďayasuke ," tun a nesa ya ķallara ido akan yaji gaba ďaya ta tafi da nutsuwar shi,"tunda daga lokacin yaji bazai iya rayuwa ba ita ba shidai yasan yana ganin ýan mata iri iri Amman wannan daban take, hakan yasa yabi diddigi ya gano cewa ashe ma ýar gidan aminiyar mahaifiyar shi ce,"
Daga nan yasamu ya sanar da mahaifiyar tashi, ranan yaga murna a gunta zai iya cewa rabon da yaga farin ciki haka qarara a furkan ta ya manta,,"

Batare da bàta lokaci ba ta nasar da qawar tata itama mumy taji daďin zancan ta amince bayan ta sanar da Abba yace mata shifa baison abunda zai kawo masa bàcin rai dan haka sai ya tabbata idan yarinya tana so tukun zai amince, mumy kuwa batace mishi ķala ba, ta sanar da hajiya fatema abinda Abban ya faďa,"" hakan yasa ta samu ďan ta sufiyan tagaya masa,"

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now