🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M* ✍🏻 *Page

2.4K 103 11
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀


           *NA*

*HAFSAT_M* ✍🏻

*Page*

       *22*

*Sadaukarwa ga qawata Aminiya  ta  Aisha  gentle   lady abar kauna  ta*😘

Assalama alaikum yan uwa  kuyi haquri da rashin jina da kukayi jiya wlh saida nagama editing kafin nayi posting ina kunna data nayi losing wanda nayi editing shiyasa kukaji shiru jiya ga aiki ya min yawa bare nayi wani😭😭😭

Dan Allah ina neman tayin Addu'ar ku wlh my lovely brother bashida lfy sosai yanzu haka an riqe shi a asbiti wannan shine dalilin da yasa bansamu damar yin posting da wuri plss I need ur du'ah thanks 🙏🏿🙏🏿


_Tunatarwa ce_👌🏿

*An karbò daga Abdullahi ďan abbas Allah yaqara musu yarda yace: Manzon Allah tsirada amincin Allah sut abbata agareshi yace: duk mai komawa kyautar sa kamar kare ne yayi amai sannan yakoma ya lashe aman sa*

*Bukhari da Musulim ne suka rawaito,,, Allah yasa mudace Amen* 🙏🏿🙏🏿

Cikin kiďimewa take binta da ido tana kallon ta tare da kakkare jikin ta tana dukunkunewa  cikin bargo tana neman hanyar tashi tasa kaya Amma babu hali, haka ta maqale inda take tana cigaba da binta da ido gabaki ďaya kanta ya kulle zuciyar ta yakasa tantance mata wanda take gani"" binta da kallo yake zuciyar sa na raya masa abubuwa iri iri shin wai wannan matar shi da yasani ne tafara hauka?,,,can yanisa yana ci gaba da binta da ido ya buďe baki yace, ke meye haka lfy kike me ya shige miki  kwakwalwa zaki ballawa mutane ķofa ki shigo kamar mahaukaciya??

qarasa shigowa tayi tana binsu da mugun kallo,"" ita ko sai qara jan bargon take tana rufuwa da yake ba riga a jikin ta,"" kallon shi da kyau tayi cikin ďaga murya ta qira shi da sunan shi tana kaďa jiki, tace Abdul malik kenan ai idan haukane na ďade da haukacewa, Amman bazaka gane ba a yanzu,," tabàryan dake hannunta ta ďaga tayi setin Humaira dashi, tana zare ido, ke kuma karuwar banza karuwar wofi, yar iska muje ni dake, zakisan ba'a shiga gona ta, karki yaudari kanki kice kinyi nasaran auran mijina, to ķur'anin Allah zakiyi kuka da kanki duk wani mai hali irin naki saiya shafawa kansa ruwa,, kibar tunanin ina numfashi a doron qasa zan iya bari  karuwancinki da kisisinar ki yayi tasiri akan mijina, Sam wlh tun wuri ki canza shawara yanda kikasan ake zaman makabarta to shi zakiyi a gidan nan dan kanki idan kinji azaba zaki nemi inda dare ya miki,, zungurin goshinta tayi da tabàryan,, shegiya baķar aljana yar isk....kunnunwansa kasa iya jure kalaman ta yayi, taji ya kame mata bakin ta da hannun sa, ransa a bàce,, cikin zafin rai, yace wlh idan kika kuskura kika qara buďe bakin ki da niyar zagin ta to ina mai tabbatar miki bazaki gane kamannin ki ba,idan kin musa kuma bisimillah, tabàryan ya warce daga hannu ta ya cilla shi gefe tare da yi mata nuni da yatsan hannun sa alamun ta baçè masa da gani ,"

dariya ta kwashe dashi kamar ta bàbbiya tana shewa yanda ya nuna zagewar sa,, tace inaga saidai ka bàtar min da kammanni na, Amman indai akan wannan shegiyar nan ne bazanyi shiru wata yar iska karuwan layi taci galaba a kaina ba saidai idan na mutu,,,harzuqashi kalaman ta suka qarayi cikin zafin nama yaja hannun ta ya fitar da ita a ďakin," kwace hannun takeyi daga riqon da yayi mata, cikin masifa take  tana dirdirjewa, yayi banza da ita, kai tsaye ďakin ta ya wuce da ita kafin ya sake ta ransa a bàce ya juya ya fice a ďakin baice mata qala ba,,,zage zage take tana surutai marasa daďi billahillazi  la'ilaha'illahuwa zakaga tashin hankalin da baka tabà gani ba wai har ni zakayi ma walaqanci kan wata yar iska karuwan...shiru tayi cikin kunar rai tayi zaman dirshem a filin ďakin,,,ji take kamar tayi hauka ko kuka,hala taji sauķin bakin cikin da take a yanzu, hannun ta ta murza akanta tana yamutsa gashin, ta ta rasa ta ina zata bòllowa lamarin nan duk abinda tasoyi gani take baya mata aiki,,""

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now