🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT M* *Page*

1.3K 61 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀

        *NA*

*HAFSAT M*

*Page*

        *64*

Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*






Innalillahi wainnailaiaihi raji'un, Umma keta maimaitawa a cikin zuciyar ta a yayinda Batula ta tabar abunda takeyi ta maido da hankalin ta garesu a ranta tana Allah gwandama munafuka kaďan ma kikagani."

   A hankali ta ďago da kanta tana kallon cikin kwayar idanunta ta soma share mata hawayen da ya cika mata fuska kacakaca tace,
  "Suwaiba ďiyata, ko zaki iya sanar dani irin lefin da yayi miki har kike irin wannan maganar"?

  "Umma, Abdulmalik baya sona baya kaunata kokaďan a ransa bazan iya ci gaba da zama dashi a matsayin dole yana nuna min tsana da walaqanci ba, dan haka nikam nahaqura da zaman auaran sa wlh dan Allah ki raba mu Umma tunda dama kece kika haďa mu wannan auran."

  "Ya salam, Umma, Tafaďa tareda da dafe kanta cike takaici bayan tasake ta ta soma magana tace, Wai ke wannan wani irin iskanci ne ke damunki, ko so kike kiyi wasa da hankali na,

  "Tuntuni naketa faman tambayar ki meye yayi miki dukan ki yayi ko meye Amman kinyi banza dani sai qara tashar min da hankali kike kina faďin in rabaki da shi  kingaji da zaman auaran sa, to bari kiji ni kina lalata min lokaci na idan har ba sanar dani zaki ba to gwara ki koma inda kika baro ki rabu dani inyi aikin dake gabana banason shashencin tsiya da asara."

  "Cikin faďa take mata maganar bayan tazo qarshe a zancen nata ta juya ta maida hankali kan aikin da takeyi tana jan qaramar tsaki dan yanda abun yabata mugun haushi."

  "Jikin Suwaiba ne yayi sanyi matuqa a hankali ta matsa gafda jikin Umma tasa hannu a kafaďar ta tadafe ta kafin ta soma magana cikin muryan kuka tace."

  "Dan Allah Umma na kiyi haquri kar ranki yabàci akaina, bakomai yayi min ba face tun lokacin da kuka kaini gidan sa amatsayin matar sa Umma har ila yau bansan meye daďin aure ba domin hatta daran farko na a cikin baķin ciki da kunar zuciya na kwana dan ko dawowar sa gidan banji ba bare har inga kwayar idanunsa harma nayi tsammanin tarairayan da amarya take samu a daran farkon ta,

  "Umma hatta jiya da natare shi da maganar bani hakkina da bayayi kawai sai yashiga zagina wai ni karuwace yar iska idan maza nakeso infita kan titi zan samu duk wanda yayi min, Waiyyo Allah na wlh yaci min zuciya da wannan munanan maganar Umma kinga ai gwara ya sakeni in mutum akan son sa bawai inyita zama yanaci min rai da tsanar sa agareni ba....

   "Kambu Shi Abdulmalik ďin ne yayi miki irin wannan tijaran"?
  "Kai suwaiba ta gyaďa mata alaman Eh tana qara faďin, Umma nice amaryar sa Amman sai ganin sa nayi da Maraqishiya suna nunawa junan su soyayya dan rashin adalci ni kuma ko ohho."

  "Ran Umma ne ya kuma sosuwa da jin wannan lbrn, cike da takaici da zafin rai tabar aikin da takeyi ta ďauki hijabin ta dake rataye jikin ķofar shiga kitchen ta zura shi ajikin ta tareda kamo hannun Suwaiba tace biyo ni muje in nuna masa shi bai isa yaci zarafi naba yayi kaďan wlh."

   "Tana maganar ne tareda ďaukan hanyar ficewa ganin hakan ya sanya Batula dake tsaye har izuwa lokacin faďin, Umma ina kike nufin zakije da safiyar Allah akan wannan maķaryaciyar yarinyar tazo tazuba miki karya da gaskiya tasaki zaki ďibi ķafa da safen nan kije ki ďagawa ďanki hankali."

  "Qaniyar ki Batula, Cewar Umma fuska a murtuke tana mata daķuwa da hannu tace, Gidan Ubanki zanje shegiya munafukar yarinya ai nasan dama duk bakin ku ďaya kawai dai shiru nayi naqyale, kuma  wlh idan nadawo naji lbrn kin kai gulma gun Abbn ki cewa ga inda najeba,  Himm zakici gidanku sai na tabbatar da nacire miki labèn baķin ki ďaya."

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now