🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M* *Page*

1.3K 57 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀

        *NA*

*HAFSAT_M*

*Page*

        *53*

Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*





"Abba ma haka yakan zuwa dubata akai akai dan yaga yaya jikin nata yake, kullum idan zai zo asibitin sai ya tabbatar da yayi mata siyayyar kayan ciye ciye dasu fruits"" Umma kam dama ba'a maganar ta domin tunda hakan yafaru inbanda tura saqon tsinuwa babu abunda take aikawa humaira domin kuwa a wannan lokakin ne taji tsantsan tsanar ta yaqara dasuwa cikin zuciyar ta wanda bata tabà yima wani mahaluqin ďan adam mutum irin hakaba, ji take yanda abun ke ci mata a rai idan ba samu tayi ta amayar dashi ba zai iya haddasa mata ciwon zuciya dukda hakan ma wani rana saida taje gidan Abdulmalik ďin ta tarar da Maraqishiya ita ďaya a gidan tamkar mayya, dukda itama dai ba sonta take ba cikin zuciyar ta Amman gani take tafi mata akan humaira."

    "Abun nema yasamu matar driver ta haifi taya dubun su goma ya huta, haka shine yafaru da Maraqishiya a lokacin da taga umma acikin yanda taga yanayin fuskan ta tagane cewa ba lfy, cikin makirci irin nata kuwa tasamu kan Umma ta zazzaga mata karya da gaskiya akan zubewar cikin humaira, babu abunda ke fita a bakinta tamkar tsinuwa da ďaukan alwashin cewa kota halin qaqa sai tayi mata korar kare a cikin gidan tareda cusa tsanar ta a cikin zuciyar Abdulmalik, hakan da Maraqishiya taji Ummar tafaďa ba qaramin farin ciki yaqara jefata ba, bayan Umma tabar gidan ta ďauki wayar ta gameda qiran shiwari ta zazzaga mata yanda sukayi da Umma a yanzu."

     "Hankalin ta sam yakasa kwanciya saida tabi tana ta yaďa abunda shegiyar matar ďanta tayi,  tasamu qanwarta hajiya zulai ta bata lbrn abunda yafaru, hajiya zulai tayi baķin cikin jin hakan matuqa, hakan ba qaramin ingiza mata rai yayi ba" koda najeeb da matar sa Zaliha sukaji lbrn hakan sunyi matuqar tausayawa Abdulmalik domin sun san yanda yakeson haifuwa shima yaga yaron sa wanda ya haifa Amman gashi hakan bai iyuba, dukda suna mamakin jin cewa wai humaira da gangan ta zubar da cikin, hakan bai hana najeeb zuwa asibitin yaga ya takeba dukda bawai shaquwa sukayi da ita ba amatsayin matar yayan shi Amman ya yaba da halinta zuciyar sa takasa aminta da hakan" Zaliha kam a dole take binshi suje asibitin badan ranta yaso ba dan dama jininta sam bai ďauki na humaira ba dan aqalla zata iya cewa duk lokacin da suka haďu a gidan umma hira bata shiga tsakanin su, dan haka yanzu ma da taji hakan baki ta cura cikin zuciyar ta tace dama zata aikata ance idan kaga mutum ďan adam to kabarshi a yanda yake dan da zakaji abunda za'ace maka gashi ya aikata wani abu ko kuma yana aikatawa,  zaka iya musawa."

     "Koda doctor ya tabbatar da cewa tasamu lfy sosai kuma zazzabìn da ya rufeta shima yabarta a yanzu ta ware ba wani waje nata dake ciwo, hakan ya sanya shi rubuta musu takardar sallama yabasu" a lokacin da aka sallameta Batula ce tareda da ita yauma kamar kullum sai Abdulmalik" cikin hanzari batula duk ta harhaďa musu kayan su, suka fice a ďakin, suka iso zuwa haraban asibitin inda yayi parking motar."

    "Mazaunin bayan motar Humaira ta buďe ta shiga batula kuma ta shige mazaunin gaba Amman badan ranta yaso hakan ba, dan ita anata taso humaira ta zauna a gidan gaba dan yanda taga tsakanin su  babu sakin fuska har yanzu  musamman shi Abdulmalik da bakasafai ma yake mata magana ba, idan yayi maganar ma takama sane Amman badan yanada niyar yi ba, aqalla idan ta duba zata iya irga iya maganar da tashiga tsakanin su."

    "Koda suka shige cikin motar Abdulmalik ya figi motar yayi hanyar gida dasu" suna isa bayan mai gadi ya buďe masa get ya shiga, yasamu waje yayi parking kafin suka fito daga cikin motar, Humaira jiki a sanyaye batayi magana ba ta qarasa zuwa cikin parloun tana riqe da wasu kayan a hannunta, Batula  ma ta tsaya ta kwashi sauran kayan da sukazo dashi kafin tabi bayan ta."

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now