🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻 *Page*

1.6K 67 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀



         *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻


*Page*
      
       *44*


Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃



*ZUWA GAREKI QAWATA AMINIYATA, TA ASALI, AISHA IBRAHIM GENTLE LADY, MARUBUCIYAR  SO KO ZURFIN CIKI DA LITTAFIN WIYA BATA KISA (SAI KWANA TAQARE) AKODA YAUSHE INA ALFARI DAKE, KE ĎIN DABAN KIKE AGARENI MUTUMIYATA INA SO KISAN CEWA WANNAN LITTAFIN RAYUWAR AURENA DUNGURUGUN NAKINE MALLAKAN KINE KEĎA YABA TAREDA WANI BA, INA FARIN CIKIN SADAUKAR MIN DA LITTAFIN SO KO ZURFIN CIKI DA KIKAYI, THANK U MY DEAR ALLAH YABAR ZAMAN TARE DA AMANA, IYA WIYA ANA MUGUN TARE AISHU NA, KINA HASKAWA AKO DA YAUSHE LITTAFEN KI AKWAI FAĎAKAR WA*😘






Baccin ta take sosai me nisa hankalin ta kwance bata farka ba har aka qira sallan magariba aka idar tana bacci, tamkar wacce ake binta bashin bacci." batula ce ta turo ķofar ďakin ta shigo dan duba ko lfy take haka har zuwa yanzu bata fito ba gashi duk kowa yayi sallah an zuba abincin za'a aci kowa yana wajan banda ita."

    "A hankali ta qarasa shiga cikin ďakin, tare da zama a gabanta tasa hannu a kafaďar ta kafin ta soma tashin ta a hankali tana qiran sunan ta." kamar a mafarki taji ana qiran sunan ta, cikin magagin bacci ta buďe idanunta ya sauka kan fuska batula, ganin itace ke tashin ta ya sanya ta tashi zaune tana hamma tayi miqa tare dayin salati." tana sakar mata da murmushi tace Aunty tashi kiyi sallah lokaci tayi idan kin idar sai ki same mu a parlou zamuci abincin ke ake tambaya, kinata bacci tun ďazu."

     "Batayi magana ba illah kai kawai da ta gyaďa mata alaman to, ta miqe tsaye ta shige cikin toilet ďin su dake cikin dakin, batula kuma ta fice ta dawo parlou inda suke har sun soma cin abincin, Abdulmalik ya tambaye ta yace ina humaira har yanzu baccin take,?" A a tabasa amsa da cewa yanzu na tasheta, tayi sallah zata fito idan ta idar." bai kuma faďin komai ba yaci gaba da cin abincin sa, najeeb dake gefen sa yana kaiwan loman abinci bakinsa, bayan ya gama haďiyewa yace, nikam meke damun Amaryar tamu ne haka, naga tunda kukazo bata cikin kuzari saima bacci da tafaďa yi, ina fatan dai lfy take,?" ya qarashe maganar yana duban Abdulmalik wanda ya miqa hankalin sa ga abincin da yakeci."

     "Zaiyi magana batula ta tari baķin sa da cewa, yaa najeeb kana ina muka samu wannan babban rabon baka saniba, na ďauka ma wlh dan tsaban farin ciki shine zai soma baka lbr ashe ba hakaba da alama nice me rabo." tana dariya tare da gyara zama ta qara cewa, yanzu dai Allah yasa nice zanyi maka albishir dan haka yarjejeniya zamuyi, idan nafaďa maka to tabbas ba makawa zaka cika min alqawarin da kayi min na sabon waya, basai har nagama school ba, ka amince da haka,?" tana kallon sa tayi masa tambayar, wanda shi kuma hakan da yaji tana faďa ya sanya shi dawo da hankalin sa gareta da yake ya kammala da cin nashi abincin ya kawar da plate ďin gefe kafin yace."

     "Naji na yarda saidai kuma kiyi sauri ki sanar dani, tun kafin in gane da kaina, dan idan na canki albishir ďin da kaina, shikenan kinga kinyi asaran sabon waya, Ina ai baza'ayi hakaba, tafaďa tana ci gaba da dariya tace to bari kaji amaryar yaya dai aunty humaira ciki ne ďauke da ita, aqalla yau wata uku kenan muke ciki..

     "Zataci gaba da magana ya katseta da cewa, tsaya batula daga nan ya isa haka, bama irin wannan wasan dake, kifaďa min gaskiya, wlh tallahi yaa najeeb kasan dai baka bina bashin rantsuwa wlh ciki ne ďauke da ita, kuma idan ma yarda ne bakayi ba ga yaya nan ka tambaye shi, zakaji daga bakinsa ko su Umma zaka iya tambaya duk zasu faďa maka." bai kuma bi ta kanta ba ya kai dubansa ga Umma gameda tambayar ta ko maganar ta gaskiya ne," banza tayi masa tamkar wacce ba da ita yakeba illahma kawar dakan ta gafe da tayi."ganin taqi kula sa saikace batasan me suke magana akai ba, hakan yasa ya rabu da ita yadawo da duban sa ga Abdulmalik wanda yaja gefe daga wajan abincin da yake shima ya kammala da cin abincin yace, Abdullah dan Allah wai haka zancen yake,?"." kai ya gyaďa masa alaman eh hakane batare da ya kalle sa ba."

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now