*
*Page*
*56*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*"Tunda idanuwan ta suka sauka akan takardar da Umma ta jefeta dashi, Jikinta yashiga mugun yin rawa zuciyar ta yana tsantsan bugawa sosai, a hankali takai zuwa qasa tasa hannu ta ďauki takardar hannunta yana karkarwa ta warware shi a hankali take binsa da kallo tana karantawa, idanuwanta suka cika da kwalla batasan lokacin da hawaye mai zafin gaske ya soma bin kuncinta ba."
"Tsantsan firgita da abuda idanunta suka gani shi ya sanya ta durkushewa qasa a wajan tana qara maimaita abunda ke rubuce a takardar cikin kunar zuciyar ta soma faďin Innalillahi wainnailaiaihi, tana runtse idanunta taqara cewa, Abdulmalik meye nayi maka haka zakayi min irin wannan sakin walaqanci har saki uku"? meye nayi maka dan Allah bayan nafaďa maka gaskiya ta....
"Shiru tayi tana kuka sosai takasa qarasa maganar da take, Bata ankara ba taji an jefeta da abu ajikinta, Hakan shi ya sanya ta cikin mutuwar jiki ta ďago da jajayen idanuwan ta wanda suka soma kumbura dan kukan da tayi."
"Ido huďu sukayi da Umma wacce ke tsaye a kanta tana mata mugun kallon da ya sanya ta sauķar da nata idanun qasa."
"Cike da zafin nama Umma ta fisgi hannunta ta riqe gam ta soma janta daga ďakin suka fice Siyama na riqe da bagcon da suka tusa kayanta aciki tabi bayansu."
"A cikin parlou sukaci karo da Maraqishiya hannunta riqe da plate ďin abinci zata shiga kitchen da alamun yanzu ta kammala cin abincin" Ganin Umma riqe da humaira tana jan hannunta, ga Siyama na biye dasu riqe da bagco ya sanya ta ajiye plate ďin a qasa ta dawo zuwa garesu cike da mamaki tace, Umma lafiya dai naganki haka da yamman nan halan wani abun ne yafaru,?"
"Kawar da kai gefe tayi tanajan dogon tsaki ta daidaita tsayuwar ta kafin tace, kefa Maraqishiya wani lokacin kin cika tambayar rainin hankali wlh, kinaso kice min bakigane abunda zanyi bane ko meye,?" To idan ma ganewa ne bakiyi ba zan ganar dake, Abunda kika kasa yi tuntuni shi zanyi yanzu, Tana mata nuni da humaira wacce kanta ke qasa inbanda hawayen baķin ciki babu abunda take zubdawa, Umma taci gaba da cewa kinga wannan ja'iran matar ita zan kora yanzu tayi hanyar gidansu tasan inda dare yayi mata dan bazan iya cigaba da kallon wannan shegen muguwar baķin fuskan nan a matsayin surikata ba tazo daga baya muma ta ďauki adda ta kashemu ďaya bayan ďaya tunda har ta iya kashe jaririn da ko gama zama cikekken halitta baiyi ba...
"Dan haka abunda nakeso dake yanzu shine, maza babu bàta lokaci ki samu abun rubutu ki tsara gaskiya da karya ki rubuta kemadai kinsan sauran, kuma dan nace gaskiya bawai ina nufin ki rubuta mu muka koreta ba, a a ita ta kori kanta yanzu a tashar mota zamu sauketa daga nan sai mu koma gida idan kin gama tsara rubutun saiki ajiye a inda kika tabbata zai gani da kansa kuma idan ya tambaye ki ko kinsan inda take kice masa bakisani ba yanzu haka na aiki sani mai gadi kinga shima kenan baisan meke tafiya ba, kuma idan yakawo min saqona ki ajiye min ban yarda kiyi amfani dashi ba."
"Tana kaiwa nan taqara kallon Maraqishiya da kyau akaro na biyu taqarashe maganar da cewa ina fatan dai kingane menake nufi, kuma zaki kiyaye,?"
"Gizgiza mata kai tayi alamun Eh tagane komai, Umma ta girgiza kai tace yauwa yar nan haka nakeson ji yanzu abunda zamuyi shine samo min wani qalle ki rufe min idanuwan ta ruf sosai domin ko hanyar da mukabi da ita baniso tagani bare tayi gigin dawowa" Babu musu Maraqishiya tacire ďaurin ďan kwalin dake kanta tazo dafda su ta ďaure idon Humaira dashi gam dan mugunta zuciyar ta wasai har saida tasaki yar qara tana kama ďan kwalin, Bayan tagama ďaura mata ne Umma taja hannun humaira da karfin ta Siyama tabi bayan su suka fice daga parloun kai tsaye waje suka nufa inda motar take parke suka shiga Umma tashiga gidan baya tareda Humaira dan gudun karta kunce ďan kwalin basu sani ba."
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,