🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M* *Page*

1.5K 59 1
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀


        *NA*

*HAFSAT_M*



*Page*

       *45*


Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃🏻









Ya mutsa fuska yayi tare da tsuke baki alamun jin irin  kalar abincin yayi masa jagwalgwalo, yana kallon ta yace tayaya zaki iya cin miyar kuka da cous couse ana zaman lfy,?" zan iya ci mana, tafaďa tana dariya, taci gaba da cewa, kaga nifa ko a gidan mu bamusan cin  wani tuwo da miyar kuka ba saida cous couse kasamu ka haďa shi da gashashshen kifi karfasa da man shano, duk family mu hakane, musamman Abban shi kam bashida wani abinci wanda ya wuce wannan,  indai har kanaso kaga yaci wani kalan abinci, to kada ka tambaye sa me zaka dafa masa, dan idan ka kuskura ka tambaye sa wanne irin abinci zaici, to miyar kuka da cous couse zaice maka kullum baya gajiya da ci, so all gidan mu gaskiya munaso..

    "Sai yayana mahmud shine kaďai daban a cikin mu wanda bayaci a duk lokacin da yadawo gida daga wajan aiki yaga nadafa wannan abincin, to a ranar babu makawa akaina zai sauke duk wata bala'in shi da masifar sa sai idan Abba yana nan yake raga min, har gargaďi yake min cewa wai idan har nasan wannan shegen abincin zan dafa to in tabbata nayi masa wani abincin daban Amman ba wannan ba."

     "Tana haďe fuska ta qara cewa, kaji fa dan Allah saikace wani ubana ko yasamu wata yar aikin sa harda jera min qa'ida."

      "Sosai maganar nata yabashi dariya, yana dariyar yace to ai idan ba uban ki bane kinsan dai cewa is ur brother yanada right a akan, dan haka ko nima ina bayan sa wlh inaji ina gani bazan zauna inci wannan jagwalgwalon abincin naku ba."

     "Ci gaba da duba takardun sa yayi bayan ya ajiye cup ďin shayin dake hannunsa, ya qara cewa, kinga malama nifa wannan surutun naki ya isheni haka inada aiki agaba na dayawa, daga tambaya shikenan sai kikafaďa zuba min lbr saikace BBC hausa, babu ko full stop."

     "Haďe fuska tayi jin abunda yafaďa kamar yar yarinya ta cura masa baki kafin tace, au hakama zakace ko, to shikenan ai gashi kayi ma kanka buqulu dama gobe nake da niyar dafawa in haďa shi da kifi na da man shano." tsuke bakin ta taqarayi tareda haďiyan yawu, kafin tace, kaga kuwa inaci kana kallo na ko tayi bazanyi maka ba kwalelen ka."

     "Ai baki isa ba, yace da ita yana murmushi ya qara cewa kinsan idan nayi niyyan ci inaso basai kinyi min tayi ba zanci, Amman dole kiyi wannan kifin da rabona, kin ma tuna min insha Allahu gobe zan tafi abuja akwai aikin da zanje inyi, bazan wuce sati ďaya ba, pls sai ki kula da kanki banda fita, nasan ma ba fita kikeba but ki kiyaye."

   "Zan kiyaye tafaďa tana kallon sa, cikin qara qasa da murya tace pls mutafi tare mana, inaso in koma school ďin nan zaman gidan da nake ya isa haka, , dan Allah karkace a a idan mukaje abujan ko Abba zai shirya min komi wlh ga Ameena qawata tare muke zata kula dani pls."

   "Zaki tafi Maman baby Amman ki qara haquri idan nadawo da kaina zan shirya miki komi sai kitafi, idan yasoma in rakaki da kaina muje tare kinsan yanzu a qarqashin kulawa ta kike dole nine wanda zan biya kitafi ba Abban ki ba."

    "Runtse idanunta tayi, tanajin wani irin zugi cikin zuciyar ta, sam bataji daďin maganar tasa ba na cewa bazai tafi da ita ba, a halin shi da kansa yasan yakamata ace ta koma makaranta yanzu, Amman yana mata waine waine, akan tana ďauke da ciki saikace akansa aka soma ďaukan ciki, dalilin da yasa bataso ace ta ďauki ciki a yanzu ba har sai bayan ta kammala karatun ta, kash tafaďa cikin ranta shiyasa batayi murnan sa ba a lokacin da taji wannan lbrn cikin, dukda kyauta ce ta ubangiji bataqi sa ba..

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now