🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻 *Page*

1.5K 69 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀



         *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻


*Page*
      
       *38*

Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare






"Zama shiwari ta gyara dakyau, a karo na biyu ta kuma kaiwan dubanta gareta, tace, meke faruwa ne, kin sakani a duhu sam ni bansan me kike nufi da haka ba, cikin waye kike iqirarin zaki zubar har kike irin wannan rantsuwar a kansa,?"

       "Sauķe hannunta tayi daga tagumin  da tayi gameda da sauķar nauyayan ajiyan zuciya, ta dawo da dubanta kan shiwari, damuwa qarara kwance bisa fuskanta, cikin iriyar murya, tace."

      "Humaira" tana ďauke da ciki shiwari ya zanyi da raina, komai nawa rugujewa zaiyi."Ya salam shiwari tafaďa nan take ta zaro idanu waje  tamkar wacce aka aiko mata da zancen muta, ta dafe kirji, bakinta yana ambaton salati, tace wanne ďan tashan ne yayi miki wannan mummunar zancen wanda ko daďin ji babu kodai mafarki kike.?"

      "Da idanun na, da kunnuwa na, shiwari dani akaje asibiti, a gabana Nurse ta tabbatar mana da wannan zancen, yanzu haka, dalilin da yakawo ni gidan ki kenan, yanzu yakawo mata result ďin tabbatacin cikin ne ďauke da ita, inajin sa ya sanar da ita, wlh ba mafarki nake ba, ba kuma faďa min akayi ba, da idanuna wlh shiwari." cikin dashewar murya take maganar, gameda jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune, tana fitar da numfashi."

      "Wanda hakan ya sanya shiwari qara gyara zama, batare da ta qara wata maganar  ba, har na tsawon wasu mintuna kaďan, kafin daga bisani, ta sauķar da ajiyan zuciya, a hankali cikin sassauta murya, tace, qawata matso kusa, inaso ki tattaro min da hankalin ki waje ďaya kiji abunda zan faďa miki."

      "Inajinki shiwari, wlh na tattara miki hankali na, faďi inji ko wacce irin shawara ce zan ďauka idan har zai fitar dani daga cikin damuwar da nakeji yana cin cikin zuciya ta."

     "To saurare ni kiji dakyau, shiwari tace da ita, a hankali zamu fara tafiya tamkar tafiyar maciji, har mu samu mu aiwatar da aikin mu." taci gaba da cewa, kamar yanda kike barazanar babu makawa sai kin zubar mata da ciki, to shawarar ta itace, ba'a yanzu zaki zubar dashi ba, idan har kinaso taji raďaďin zubewar cikin, to yazama dole ne mubata lokaci koda kuwa kaďan ne, dan yaron cikin nata yafara tsira, idan yaso kafin wannan lokakin kinga wannan saurayin naki da kika samo shi, sai ki nemo masa phone number ta na tabbata baki da ita, sauran abunda zai biyo baya kuma nasan kun gane ko me nake nufi basai nayi bayani ba."

      "Ya salam shiwari" kin ceci rayuwata da faďawa mummunar hali,  wlh ke abokiyar tafiya ce, tunda nake ban tabà irin wannan tunanin ba, nagane komai abunda kike nufi, shima nasan babu shakka ya tafi gana, yanzu ina komawa gida, zan san yanda zanyi in ďauki phone number ta, sai in tura masa, kinga shikenan farin cikin da narasa zai dawo gareni, in koma yanda nake a da, ya kake da suna tashi mutafi,  bukata na tabiya,  shiwari sai kinji ni, zan qiraki duk yanda akayi zakiji."

      "Cike da wani irin farin ciki take maganar, tana washe haqora, tamkar wacce akayi mata kyautar wasu maqudan kuďi, jinta take kamar tayi tsuntsuwa a yanzu taga kanta a gida." tana gama gyaran mayafin dake kanta,  ta zari jakanta, gameda yin hanyar fita, har zuwa lokacin bata daina dariya ba, ita kaďai tasan irin mugun farin cikin da takeji yana ziyartar cikin zuciyarta." A yayin da wannan saurayin ya miqe tsaye, cikin nuna rashin fahimtar abunda suke shirin aikatawa, yana kallon ko wanne su yafara magana, wanda hakan shi ya dakatar da ita daga fitan da zatayi, gameda da kawo duban ta zuwa gareshi, yace."

     "Da farko dai kafin nafaďi abunda nakeso nace muku zan fara gaya muku koni waye, ni sunana zaid, ni haifaffan ďañ garin nan ne, dalilin da yasa na amince da maganar da kika kawo min shine, dan insamu hanyar da zan rama rashin mutuncin da ya rinyar nan ta min ne, saidai kuma wani abu guda ďaya da nakasa fahimta shine, wannan maganganun da kukeyi, idan kuma na fahimta, so kuke kuce min ya rinyar da kuke magana akai itace wacce nakeso, ma'ana tanada aure kenan har take ďauke da ciki,?"

     "Zauna a wajan shanye tamkar kayan wanki, wacce kakeso tayi maka rashin mutunci, to da ita muke, itace ke ďauke da ciki, kuma sai na zubar dashi babu makawa."

      " Tana nuna kanta da hannunta, taci gaba da cewa,     Karkace, a banza da wofi nake wannan maganar, sam babu ko ďaya inada dalili, ni wannan da kake gani kishiyar tace, ina zaman zamana ni ďaya a gidana ta shigo ta aure min miji, kuma bazan tabà yin kaffara ba kamar yanda nake ni ďaya da mijina haka zata fita tabar min gida ni ďaya, ina fatan yanzu ka fahimci magana ta, kuma zaka bani goyon baya har nacima burira kaima kaci ma naka,?"

        "Jin maganganun tane ya sanya shi saukar da ajiyan zuciya, yana mamaki,  gameda yin wata iriyar murmushi, na wanda zai tabbatar maka da cewa shi cikekken ďan duniya ne, kafin yace, yanzu nagane komai idan hakane kuwa kun sameni a daidai." yana shirin fita daga parlon, ya qara cewa muje ki mayar dani inda kika ďauko ni, inada abunyi,  kina komawa gida sai ki turo min phone number ta ďin, sauran kuma ni nasan abunda zanyi."

       "Fita sukayi gabaki ďayan su daga parlonu suna qara tattaunawa, kafin sukai ga fita daga cikin gidan, mijin Shiwari ya turo ķofa ya shigo, ya tsaya yanabin ko wanne su da wani irin kallo, musamman zaid wanda yake neman hanyar fita Amman baiga hanya ba, wanda cikin rauwan jiki da tsoro duk ya gama cikata ta matso kusa dashi tana qiqiro murmushin dole, tace, dear sannu da zuwa ya kadawo da wuri haka bayan kace min sai dare zaka dawo,?"

     "Dan nace miki sai dare zan dawo shine kika samu lasisin kawo min wannan qawar taki ko, banda hakama harda kawo min katon gardi cikin gida, yazo ya ďauke ku fice kenan, duk irin gargaďin da nake miki bakyaji sai kinci gaba ko,?" to shikenan kici gaba dayi ďin muna nan tare dake." bai tsaya ya saurareta ba ya wuce cikin gidan ransa a bàce, bayan yabisu da wani irin kallo."

      "A sannan Maraqishiya ta matso kusa da ita, cikin damuwa da tsoro tace, shiwari meye haka nake gani, bake bace kikace min baya nan ba, ya akayi kuma na ganshi yanzu bayan kinsan bason ganin mu a tare yake ba,?" ai dama ba tafiya nace miki yayi ba, ya dai fita ne kawai, kuma saida ya tabbatar min da cewa sai dare zai dawo shiyasa, ni kaina banyi tsammanin zai dawo gida a yanzu ba."

      "Himm shikenan nidai mun tafi sai anjima, idan munyi waya, tace da ita gameda ficewa daga gidan, zaid yana biye da ita sukayi sallama da shiwari kafin suka shige cikin motar sukabar gidan, ita kuma ta koma cikin gida, zuciyar ta yana dukan uku uku, tana fargaban yanda zata shiga ta tarar dashi, dan tasan babu makawa dole ne ya tuhumeta akan wannan saurayin da yagani, tunda dama kullum yana cikin mata ja mata kunne da irin yawon da suke ita da Maraqishiya."

      "Koda suka kama hanya, saida ta jiye shi a unguwar da ta ďauke shi, kafin ta dawo gida wanda a wannan lokakin har yamma tayi rana tagama faďawa, ana neman magariba, bayan mai gadi ya buďe mata get ta shiga tayi parkin motar ta a  parkin space, kafin ta fito daga cikin motar ta nufi ciki, zuciyar ta wasai batajin ko wanne irin damuwa."

   
     "Tasa hannu ta tura ķofar parloun ta shiga, idanuwanta suka sauka a kansa zaune qasan filin parloun, yana cin abinci, Humaira na kusa dashi tana masa hira cikin kwanciyar hankali, ga dukkan alamu idan ka kalle su hakan zai tabbatar maka da cewa ta saukar dashi daga fishin da yake da ita."

     "Wanda ganin su hakan da tayi a tare ba qaramin baķin ciki ya kuma shigar da ita ba, duk wani walwalan da take ciki ya gusar mata dashi." cikin haďe fuska, tayi hanyar dakinta zata shige batare da ta qara kai dubanta garesu ba, taji muryan sa ya tambaye ta, yace."

  
     "Daga ina kike,?"

     "Daga gidan shiwari, tabashi amsa a takaice, bayan ya maido da dubansa gareta ya qara cewa waye kika tambaya da zaki fita, banda hakama, ban hanaki wannan shegen fitan da kikeyi ba, kina nuna min ni ban isa dake ba kenan, duk lokacin da kike da ra'ayin fita zaki ďauki qafa kifita kai tsaye da yake zaman kanki kike ko,?"

     "Jiyowa yayi da kansa ya ďibi abincin sa da yake ci zai kai bakinsa ya qara cewa, kije kici gaba da abunda kikeyi tunda hakan shine kikega yafi miki daidai a rayuwarki." yana gama faďin hakan yaci gaba da cin abincin sa, hankali kwance yana santi, a iyayin da itama batare da tace masa qala ba ta shige cikin dakinta tana zancen zuci ta faďa kan gado tana fitar da numfashi qasa qasa."










*HaneeSat*✍🏻📚📚📚

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now