🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M* ✍🏻
*Page*
*15**Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace.. duk mutumin dakafi so aduniya ,to dashi za'a tashe ka ranar gobe kiyama ,ya Allah ka tashe mu tareda Annabinka da iyalen gidan sa tsarkaka Allah ka karemu da son yahudawa Amin*🙏🏿🙏🏿
*Qawata Maryem Abdool karki sa rai cikin wannan shafin dan ba mallaka miki zanyi ba*😜😜
Sannu da shigowa ya mahmud tafaďa batare da ta kalle shi ba,"" yauwa yabata amsa yana mata kallon tuhuma, tare da miqawa Abdulmalik hannu suka gaisa kamar an sashi dole,""
Wani irin mayun kallo taga abokin mahmud ďin yana yi mata, hakan yasa tafara tsarguwa da kanta tana duba shigar da tayi, tace to shi kuma wannan wani irin mayene sai kallo na yake kamar yasamu TV,""muje ko? taji muryan Abdulmalik yana shirin fita bayan yagama gaisawa dasu mahmud," bayan shi tabi suka fita har zuwa gun motar sa ta rako sa, tace to Yaya Abdool sai anjima Allah ya tsare,""
kallon ta yayi bayan ya buďe motar ya shiga yace,"""bangane ba wannan sunan fa daga ina kika samo shi?,"
Murmushi tayi tace daga ruhinka mana,"
A a kidai canza dan bazan dauka ba ina mijinki Amman kina qirana da sunana kai tsaye, babu ko sirki banda hakama ai Abdool daban Abdulmalik daban,"
To ni shi yafi min daďi kuma dashi zan ina qiranka tace da shi tare da rufe mishi ķofar,"
kunna motar, yayi yana shirin ficewa, yace kidai gyara "
Tana dariya tace to yaya Abdool zanyi kokarin gyarawa tunda baso kakeba,
Au qarawa ma kike, ya miki kyau ni na wuce yace mata yana ďaga mata hannu,""" itama hannun ta ďaga masa tare da juyawa ta koma cikin gida zuciyar ta fal murnan zuwan shi da yayi,"
Faisal ne keta safa da marwa cikin parlon yana magana shi ďaya ya kasa zaune ya kasa tsaye,"""gajiya mahmud yayi da kallon sa yace wai meyake damunka ne faisal naga tunda muka shigo ka kasa zaune ka kasa tsaye wani abun ne yafaru?" ya tambaye shi yana duban sa"
kujera yasamu ya zauna tare da dafe kansa yace abokina dan Allah, ka taimaka min wlh nayi sake,"
kallon sa mahmud yayi da kyau yace bangane maganar ka bafa , kayi min bayani yanda zan fahimta,"
Shiru faisal yayi na ďan dakiku kafin yace qanwar ka humaira, da alama ta kubùce min,"
Ajiyan zuciya mahmud ya sauķe yace dama akan humaira ne kabi ka ďaga hankalin ka ? waima tsaya tukun kana nufin har yau ka kasa sanar da ita kana son ta?"
kai ya girgiza masa alaman Eh yace wlh lokacin da ka turo min ita kasa faďa mata nayi shiyasa nadamu ka faďa mata da kan ka tunda qanwar kace,"
To ka hutawa rayuwar ka ai dan ni babu abinda zan iya maka a yanzu,"
Haba mana abokina karka min haka dan Allah ka shige min gaba cikin wannan maganar, faisal yace da mahmud tare da tasowa yazo kujeran da yake,"
Shikenan ba matsala zanyi mata maga ya bashi amsa tare da cewa kazo mu shiga wajan Abba daga nan sai nayi mishi maganar,""""yauwa abokina kokai fa yanzu naji dama dama a zuciya ta da saura kaďan ta buga wlh,""" ai da ya buga ďin da mun huta kuwa, Mahmud yace masa bayan sun fita a parloun suka nufi wajan Abba,"
Shida mummy suka tarar zaune suna hira, sukayi musu sallama tare da qarasawa cikin girmamawa faisal ya gaishe dasu suka amsa masa cikin sakin fuska kafin ya fice yabar mahmud a gun dan ya gabatar musu da bukatar sa,"
gyara zama mahmud yayi tare da yi maya Abba bayanin son da abokin sa faisal yake ma humaira,"" yace to ai ya makara mai yasa tuntuni bai fito ya faďa ba sai yanzu da yarinya ta kawo wanda takeso kuma har magabatan sa sunzo angama magana saidai yayi haquri Abba yafaďa,"
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
ActionLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,