🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*68*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*"Bayan na samu na kub'uta daga hannunsu ina cikin tafiya ba tareda nasan inda na dosa ba na hango wani shagon masu waya na shiga na sayar da wayar, ina fitowa na samu mai adai-dai ta sahu nace ya kaini tashar mota.
Bayan ya kaini ya nuna min motar da ake lodin 'yan Abuja, kasancewar wajan mutum d'aya ne ya rage, hakan yasa ina shiga muka kamo hanya har muka iso cikin Abuja na samu mai taxxi ya kawo ni har k'ofar gida".
"Runtse iduwanta tayi a karo na biyu wasu zafafan hawaye suna k'ara zubo mata, a hankali ta d'ago da jajan idanunta da suka yi jazir sosai dan kuka ta dubi Mummy da Abba kafin tace
"Yanzu a duk irin wannan mawiyancin halin da na shiga idan nace zan koma wancan garin zaku yarda in koma?""A'a". Mummy ta fad'a tana girgiza kanta hawaye na gangaro mata a fuskanta tace
"Humaira! kinyi babban kuskure da rashin k'iran mu da bakiyi ba, yanzu da sun lalata miki rayuwa daga k'arshe sun kashe ki waye da a sara?"
Mune ba kowa ba, dan Allah ki daina irin wannan halin ba'a b'oye mummunar abu idan ana cikin neman taimako".Jikinta ta shiga dubawa tana k'ara fad'in
"Ina fatan dai basu samu damar cin galaba a kanki ba har Allah ya kub'utar dake?""Mummy lafiyata lau na dawo, ki kwantar da hankalinki ai babu wanda yayi na saran biyan buk'atarsa".
Tana murmushin k'arfin hali ta k'arashe maganar a yayinda Mummy tayi hamdala a ranta tana godewa Allah da ya kare ma d'iyarta mutuncinta.
Shiru ne ya ratsa cikin parloun na d'an dak'ik'u, babu wanda ya iya fad'in komai sai sautin sauk'ar numfashita dake tashi, ba Abdulmalik kad'ai ba har Abba sai da suka tausaya mata, lallai kuwa ta auna arziki, da ba dan kariyar Allah ba da sai yanda sukayi da ita.
Abban Abdulmalik ne ya katse shirun da cewa
"To d'iyata, munji duk abinda ya faru dake, a gaskiya kin auna arziki, fatan Allah ya kiyaye gaba ya rufa asiri, dan ba k'aramin mugun hannu kika fad'a ba, sai dai kuma mun godewa Allah ubangiji da yasa basu samu damar aiwatar da mummunar nufinsu a kanki ba."Dan haka a yanzu bani da abinda zan iya cewa cikin wannan lamarin, dukda cewa mijinki bashi da laifi sosai a ciki amman kuma hakan ya faru ne a rashin baki yarda da amincewa da baiyi ba, ya biyewa zuciyarsa ya d'auki irin hud'ubar da take basa.
Kinga kuwa yanzu ya rage a tsakaninku, idan kinga zaki iya binsa ku k'ara shimfid'a rayuwar auranku ingattacciya to bisimillah gashi nan sai ku sulhunta tsakaninku, idan kuma kinga baza ki iya ci gaba da zaman aure dashi ba, shi ke nan kina da ikon kanki a cikin wannan lamarin".
Tsantsan tashin hankali ba kad'an ba Abdulmalik ya shiga jin irin furucin da Abbansa yayi ya sanya bai san a sanda ya d'ago da kansa ba cikin muryan tausayi yana duban Abbansa yace
"Haba mana Abba!, dan Allah karka min haka, dan Allah karka cire kanka a cikin wannan maganar, nasan cewa ina da nawa lefin nine silan komai, amman na tuba na gane kuskurena yanzu bazan kuma juya mata baya ba".
Cikin k'asa da murya ya k'arashe maganar a yayinda tausayin sa ya shiga cikin zuciyar Abban Humaira yasa hannunsa ya dafe kafad'un sa yace
"Kayi shiru Abdallah insha Allahu zata dawo gareka kuyi zamanku cikin k'oshin lafiya, ni nayi maka wannan alk'awarin zan dawo maka da ita.
Dan haka kwantar da hankalinka, ka cire damuwa a ranka zata yafe maka, kasan yarinya ce komai sai a hankali".
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcţiuneLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,