🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*24*Dedicated to my besty
*AISHA GENTLE LADY*💃*Sister Lieey,*
*Sister Lieey*
*Sister Lieey*
Karkiga naqira sunanki haka kin cancanta ne shiyasa ina miqa miki gaisuwa ta matuka ako ina kike da akwai hali dana mallaka miki wannan page, Amma Karki samu damuwa insha Allahu nest time😁Allah yabar zuminci da kaunar juna ana tare🙏🏿🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂 *Sister Smasher karkiga naqara miki HBD badan komai bane illah dan kin cancanta ne keďin daban ne lokacin ki bai qure ba kina cikin watan haifuwar ki bazan daina miki fatan alkhairi ba Allah ya albarkaci rayuwar ki yasa kigama da duniya lfy wannan kirkin naki kiqara riqe shi dakyau karki bari shine jigon rayuwa HBD Sister Smasher 🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂 again and again am wishing u a long life*😘
*My Safiyya musa huguma Ana tare a riqe zuminci da kyau banda rabewa ina miqa miki gaisuwata sai kin ganni Safiyyu na*😜😜
Cikin sakin fuska ba yabo ba fallasa ta amsa mata gaisuwar tace, ya nashigo banganki ba ina kikayi?,,,,Eh wlh umma ina kitchen ina haďa mana abinci,,"
Kallon rashin fahimta tayi mata kafin tace bangane kina haďa muku abinci ba, ita wannan ďin fa tayi nuni da humaira meye amfanin ta a gidan da bazata dafa muku ba sai ke ba itace qasa dake??,,Himm kawai tace ai bata fara girki ba tukunna umma,"
"Tun yaushe aka auro ta zakice bata soma girki ba, dan taci mai daďi tasha mai daďi taje banďaki ta zazzagar aka kawo ta gidan kenan ko? ta tambaye ta tana mata wani irin kallo,,,,,zata fara ai umma duk mun zama ďaya fa yanzu, idan nice nadafa ma ai ba matsala bace itama watarana zatayi mana zaman tare ne ai,,"
Hannu ta ďaga mata tace kinga dakata uwar bayani yaushe kika sauķo haka bansani ba, harda wani kun zama ďaya?faďa min inajinki,,"Umma dan Allah kibar wannan zancan komai ya wuce ni a wajena,"
To shikenan Maraqishiya naji nabari damuwar kice batawa ba nasan dama dole za'ayi haka duk zuriyar ku ďaya mota ďaya ta kwaso ku dan haka kuje ku qarata, kuma duk abinda yabàci miki akan wannan shegiyar yarinyan kiyi kuka da kanki zakice nagaya miki,,,kai kuma kanajina ko? aure kaida suwaiba dole ne ba makawa har indai ina numfashi a duniya to sai anyi shi,,,tana kaiwa nan ta miqe tsaye tace ke tashi mutafi nagama abinda yakawo ni sai gobe kuma,,,tashi suwaiba tayi babu musu zuciyar ta fayau takeji kamar ta daka tsalle dan murna itama nan da kwanaki kaďan zata zama hajiya sai abinda taso zatayi waiyyo Allah nuna min wannan lokakin,,"
Umma ku tsaya muci abinci mana ya nuna fa,,harara ta watsa mata tace karki kuma ce min umma munafuka kawai kina nan kamar zakiyi wani abun arziki ashe ba hakaba sai kuje ku cinye abincin ku inadashi a gida na,,"
Shiru tayi bata qara magana ba saida taga sun fice daga parlon, kafin ta tashi da sauri tana faďin bari naje naba Umma haquri naga ranta yabàci sosai ina zuwa, daga Abdulmalik ďin har humaira babu wanda ya tanka mata illah mamakin canzawan ta da sukaga tayi ba zato ba tsammani,,"
Baba mai gadi ya buďe musu ķofar get ďin zasu fice kenan ta fito da gudun ta har tana tuntubè taďaga murya tace Umma dan Allah tsaya kiji abinda zancan mana,,,tsayawa tayi tare da jiyo da kai tana mata kallon bàcin rai tace, lfy zaki tsayar dani?,,,,tana sauke numfashi alamun ďan gudun da tayi ya shige mata jiki tace,,"
Umma karfa kice zakiyi fishi da abunda kikaji yanzu nafaďa wlh siyasa nayi musu cikin dabara zan aiwatar da duk wani shirin dana kulla mata batare da yagano bakin zaran ba kinga kenan suwaiba na shigowa ita kuma tana fita koya kikace da wannan shirin??,,,jinjina kai tayi tana washe baki tayi dariya tace ba shakka na gamsu da shirinki Maraqishiya wani lokacin kinada kaifin kwakwalwa har kike iya haďa munafurcin da koni bazan iyaba, sai yanzu naji wasai a raina kinga kafin nan idan itama suwaibar ta shigo sai ta tayaki kuyi tare,, ni natafi sai gobe idan nashigo kuma ma qarasa sauran,,"
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
БоевикLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,