🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M* ✍🏻 *Page*

1.7K 102 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀


        *NA*

*HAFSAT_M* ✍🏻

*Page*

       *17*

*Kafin na wuce inaso nayi amfani da wannan damar wajan yi muku godiya kan yanda kuke nuna min kulawa inafarin cikin kasance wata daku,*👇
   
Babbar yayata sweet Anty fauzy
       
Maman nana

Maman zee
         
Maman khady

Hanee
          
*Ina miqa muku gaisuwa ta fatan Allaha yabar zuminci da kaunar juna Amin*🙏🏿🙏🏿

_Baheera karfa kisa rai aciki_ 😜😜

~Ahankali yake yaye mata lifayar cikin nutsuwa tare da bin surar jikin ta da kallo yanajin wani irin a ran shi,""Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimmussalihat,,, Tabarakallahu masha Allah,,ya furta bayan yagama yaye mayafin, ya rungume ta tsam ajikin shi yanajin wani irin sanyin ni'ima yana sauķa mi shi cikin zuciya, daure wa yayi ya kai hannun sa kan zif ďin riganta yafara zugewa, cak ta riqe hannun sa tare da ķoķarin zame jikin ta a nashi ta buďe baki da muryar ta wanda ya dashe dan kuka tace,, meye haka kake min kabar min kayana,,"dariyane sosai ya ķubùce masa ganin yanda tayi maganar kamar wata yar yaye, ya buďi baki yace,,"

Kinga malama ki kwantar da hankalinki nifa babu wani abunda zan miki kawai dai so nake na taimaka miki,da wannan kayan zafin,"

zamewa tayi gaba ďaya daga jikin shi kanta a qasa takasa ďago da kai ji take idon ta bai iya jure kallon na shi ba," atakaice tace karabu dani bana bukatar taimakon ka,""

"Cak ya ďauke ta fuskan sa ďauke da murmushi yace shikenan gimbiya nabari muje ki kwanta, kinji ? yana murmushi," kawar da kanta tayi gefe taqi haďa ido dashi""a kan gado ya dire ta ya gyara mata pllow tare da kwantar da ita yaja mata bargo ya rufe ta," tsayawa yayi yana kallon yanda ta lumshe idanuwan ta kamar mai bacci,, lumshe idon sa shima yayi tare da buďewa ya sauķe nauyayan Ajiyan zuciya,"

kinyi sallah kuwa? ya tambaye ta, yana kallon ta,"" ďaga masa kai tayi alaman Eh,""To tashi muci abinci kafin kiyi bacci,"

Banajin yunwa tace dashi cikin qasa da murya,

ban yarda ba nidai taso muje muci kinji my angel yana shafan kanta, yana ganin kyawun fuskan ta"""Bazanci abincin ba ni karabu dani dole ne, cike da takaici tayi maganar ji take bata bukatar komai a yanzu duk da irin yunwan da takeji,Amman bazata iya cin komai ba""ďauke hannun sa yayi daga kanta ya tashi tsaye, ganin har yanzu bata huce ba kuma batada niyar hucewa, yace to shikenan na qyale ki kiyi baccin ki saida safe ya juya yabar ďakin, zuciyar sa cike da abu iri iri yana takaicin wannan daran sam beji daďin shiba,, ďakin sa ya nufa ya shige  toilet yayi wanka ya fito tare da goge jikin sa ya shafa mai ya ďauko farar jallabiya mai kyau ya saka tare da feshe jikin da turaruka masu ķàmshi yaja ķofar ďakin ya rufe bayan ya fice, yayi lungun ďakin ta ya tura ķofar ya buďe""

Tsaye ya ganta tana ta jeka ka dawo duk tabi ta tashi hankalin ta bata cikin nutsuwa," duban ta yayi da ido ganin yanda ta birkice kanta ko ďan kwali babu gashin ta yayi cibiri cibiri dashi ita kaďai ta haďa uban zufa ďan tsaban masifa nacin ta kamar mai neman nayi,,""girgiza kan sa yayi ya qarasa shigowa cike da mamakin ta, yake tambayar zuciyar wai yanzu zafin kishi ne ya hanata kwanciyar hankali ko kuma bàtan kai ne ?,"shidai bai tabà sanin ta da irin hakaba saida yayi wannan auran yaga haukanta,""

Mai kuma kazo yi a ďaki na? yaji ta tambaye shi tana kai masa harara,""" kota kanta baiyi ba ya ďauki abinda ya kawo shi ya fice,daga ďakin,"

Harara taqara bin sa dashi tace munafukin mutum kawai ai bakaga tashin hankali ba tukun muje zuwa, tana girgiza kai take maganar cike da masifa," qaran wayar ta taji ta ďauka tasa a kunne,"

Hello qawata yane mai ake ciki da gaskene yayi aure?,"shiwari ta tambaye ta tacikin wayar,"" himm shiwari kenan ai kibari wlh matar nan ba qaramin taimaka min tayi ba maganar ta gaskiya ne naga cin Amana wajan namiji ai ban qyale su saida na nuna musu rashin hankali na kafin nabar ďakin ," tsaf ta zayyane mata irin tashin hankalin da ta musu,"" cike da takaici Shiwari ta shiga mata faďa tare da bata shawarar yanda zata billoma lamarin," saida tagam sauraran ta kafin takashe wayar bayan sunyi sallama zuciyar ta cike da jin daďin shawarar da shiwari ta bata haka ta haura gado ta kwanta ita ďaya tana murmushin mugunta,""

Yana barin ďakin ta ya shige na Humaira," har yanzu tana nan yanda yabar ta Amman da alamun tayi bacci,""kan gadon yahau bayan ya maqala wayar sa a charge,""

A hankali cikin dabara yaye bargon da ya rufe ta dashi, wani irin yarr sokar jikin sa yayi ya lumshe idanun sa ya qara buďe su suka sauķa kan bayan ta wanda yafara zuge mata zif ďin riganta,,hannun sa ďaya yakai yaqarasa zugewa ganin bacci mai nauyi takeyi tana sauķar da nauyayan numfashi, idan ka ganta kasan cewa kuka tasha sosai ba kaďan ba "shafan bayan ta ya soma cikin dabara da nutsuwa yanajin yanda fatar jikinta ke tsantsi da fitar da daddaďar ķàmshi akaro na biyu ya kuma lumshe idanuwan sa ya buďe yanajin wani shauķi a ran sa haka har yayi nasaran cire mata rigan jikin ta ya zubawa surar ta kallo a zuciyar sa yana qara godewa Allah da ya mallaka masa wannan hallitan nashi a matsayin matar sa ta aure,""

Jawo ta jikinsa yayi ya rungume ta sosai a faffaďar ķirjin sa ya gyara kwanciyar sa tare da jawo musu bargo ya rufe su ya lumshe idon sa, zuciyar sa cike da tunani iri iri har bacci yayi nasaran ďaukan sa yana nan rungume da ita....


A dai qara yimin afuwa makaranta nagode🙏🏿🙏🏿




*HaneeSat* ✍🏻📚📚📚

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now