🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*35*Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare_TUNATAR WACE_👌🏿
_Ingantacciyar Hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzo Allah (SAW)_
*Ankarbò daga Abdullahi ďan Amru ďan As Allah yaqara musu yarda yace: Manzon Allah (S.A.W) yace:" hakika mafificin Azumi a wajan Allah shine Azumin Dawud, mafificiyar sallah a wajan Allah: sallar Dawud ya kasance yana yin barci rabin dare, sai ya tashi a ďaya bisa ukunsa, sai yayi barci a ďaya bisa shida, ya kasance yana yin Azumi yau ya ci gobe""*
_Allah kasa mu dace Ameen_🙏🏿🙏🏿
Ďago da kanta tayi gameda miqewa tsaye wanda har i zuwa lokacin hannun ta yana kan kirjinta tana riqe dashi sanadin zafin da takeji yana qaruwa mata tamkar ta balle shi takeji cikin bàcin rai ta ďago da idanunta,,"
""wanda suka soma canza launi tareda sauķar dashi bisa kansa ganin fuskan sa ba qaramin mugun bàcin rai ya kuma jefata ba gameda qara murtuke fuska tana masa mugun kallo,,"
"Ta buďi baki dakyar da niyar masa magana tanajin tamkar Aman fitowa waje zayi hakan ya sanya ta fasa abunda tayi niyar faďa,"
"Tasa ķafar ta zata koma cikin motar taji yace,,"
"Kiyi magana masa sarkin rashin kunya idan yau ďinma kinada baki,hakan da taji ya faďa ne yaqara tunzura ta bataso tanka masa cike da bàcin rai ta dawo da baya zuwa inda yake tsaye yana harďe da hannayen kan ķirjin sa gameda zuba mata na mujiya yana jiran yaji mai zatace, idanunta tar akansa ta danne abunda takeji,,"
"cikin zuciyar ta tare da qara haďe fuska ta ďago hannunta tayi setin fuskan sa da yatsan ta kafin tace,,"
"Gaga malam wlh tallahi kafita a harkata banason iskancin banza kanaji na ko? wlh ko tafiya nake ka ganni to ka canza hanya ko kayi kwanan layi ko kuma ka juya baya dan wlh banida kyau bana ďaukan zancen banza da wofi irin naku na yan tasha masu zaman kashe wando bakuda wani aiki inbanda saka idanunku kan matan mutane bakusan komai ba duk wacce tazo wucewa da ruwanku, to nidai inaso kasan wani abu tamkar yanda kasan nayi maka gargaďi abaya wannan karon ma shi zanyi maka kafita harkata karka kuma bi takai na dan ni ba tsarar ka bace kaji nagaya maka,,""Idan kunne yaji to ba shakka gangan jiki ya tsira..keee ya dakatar da ita da hannun sa cikin jin zafin kalaman ta yace, wlh kibar ganina haka ni ba'a takani da ķafa kai tsaye a wuce inaso kisan cewa billahillazi la'ilaha'illahuwa kinji da sunan rabbi na rantse miki ba iblis ba wlh na ďauki alwashin sai kinyi dana sanin wannan munanan qazaman kalaman naki a kaina ki tabbatar da cewa bake ba zaman lfy ko ina kike zan nema nasani,,"
"Mitsee taja dogon tsaki tace in kafasa kaqi Allah a niyar ka tabika wlh nafi karfin ka, tana kaiwa nan ta juya zata shige mota tayi kicibus da shi ba shiri ta dawo baya yana mata kallon tuhuma,,""A takaice ya tambaye ta yace keda waye wannan kuke magana??
"Nima bansan shiba kawai ganina yayi ya tsaya yana gaya min zancen banza,,au baki sanni bako zakice? badamuwa ya rinya akwai lokaci nan gaba kaďan zakisan koni waye, yana gama faďin haka ya kaďa kansa gameda da shigewa cikin super market ďin ransa in yayi dubu ya bàci,,"""A yayin da itama ta shiga motar ranta a jagule har ta zauna sai kuma Aman data danne shi ya taro mata cikin baki batasan lokacin da ta fito daga cikin motar ba ta soma kwara Aman sosai babu kakkautawa wanda ganin hakan ba qaramin mugun hankali ya tashar masa ba,,"
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
ActionLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,