🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*57*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*"Fita sukayi daga cikin tashar suna tafe tana binsu a baya minti minti suke juyowa da kansu suga ko tana binyu idan sun haďa ido sai taga sun sakar mata da shu'umin murmushi wanda take kasa ganewa, Ganin dare sai qarayi mata yakeyi dan gashi har an soma qiran sallan isha'i hakan ya sanya ta dakatar dasu acikin tafiyar tace dasu, dan Allah har yanzu bamuzo shagon bane,?"
"Ama
sa ďayan yabata da Eh tareda qara faďin shagon da yakama mukai ki ďin ne a rufe yake Amman akwai wani mutum mai siyan waya a nan bayan layi na tabbata za'a sameshi" Kanta kawai ta girgiza bata qara cewa komai ba sukaci gaba da tafiya.""Gani tayi sun shiga da ita wani dogon layi mai ďan duhu wanda cikin sa babu hasken wuta sosai, haka zalika baka kallon mutane dayawa sai ďaďďaya hakan shi ya haifar da shiru a layin tamkar babu ďan adam aciki."
"Tsoro ne ya soma mamaye cikin zuciyar ta ganin yanda yanayin layin yake ta soma dana sanin da bata biyo su ba domin gashi sun qara shigar da ita inda batasani ba, Dube dube tafarayi tana rarraba idanu tana shirin komawa baya dan tagama yankewa a ranta bazataci gaba da binsu ba suje suyi mata abunda batayi tsammani ba tunda dama zuciyar ta ba gama gamsuwa tayi da bayanan su ba kawai dai rashin sanin waje ne ya sanya ta binsu."
"Sun iso daidai bakin wani qaramin gida suka tsaya wanda cikin sa kwata kwata idan ka gani bazai wuce ďakuna biyu ba,
"Tattaunawa sukayi a tsakanin suna dariya ganin ta tsaya a baya tana raba idanu yasa sukayi zaton kota gane me suke nufi da ita, hakan yasa suka yanke shawaran ďauke ta su shiga da ita ciki dan karta kawo musu cikas tunda babu mai kallon su."
"Batareda da tace dasu komai ba ta juya baya tayi hanyar da suka biyo da ita ta soma tafiya batare da tasan inda zata nufa ba, Bata ankara ba taji hannun mutum a bakinta an toshe mata shi yanda bazata iya kwakkwaran ihun da mutane zasuji ba" Ďaga ta sukayi ďayan ya riqe jakar kayan ta, tana witsl witsl da ķafafunta tana ķoķarin kwacewa daga riqon da sukayi mata Amman takasa domin ba qaramin riqo sukayi mata ba. yanayin yanda suka toshe mata baki da hanci yasa duk irin ihun da takeyi baya iya fitowa waje ga numfashin ta da takeji yana shirin ďaukewa."
"Cikin wannan gidan suka shiga da ita suka nufi cikin ďaya daga dakuna biyun dake jere a gidan suka kunna wutan ya haska komai na cikin ďakin."
"Madaidaicin ďaki ne irin na samarin zamani babu wani tarkace dayawa acikin sa" Shimfiďe yake da yar kwoďaďďiyar leda a tsakiyar dakin sai katifa dake shimfiďe da pllow akai gefe guda kuma ďan karamin TV ne ajiye da DVD akansa sai tarkacen kwanukan abinci wanda sukaci suka bari da kofinan shayi masu datti"
"Direta sukayi kan lotsats tsiyar katifar kafin suka saki bakinta wanda suka toshe mata shi" Numfashi take saukarwa wahalalle tana haki sosai tamkar wacce tayi mugun gudu, Bayan tadawo daidai tashiga raba idanu ganin inda suka shigo da ita ya sanya ta miqewa tsaye tana waige waige tsoro yagama cika mata zuciya sosai, Cikin dauriya da karfin hali. muryan ta yana harďewa ta soma ce musu, Meye kuke nufi dani, meye nayi muku daga neman taimako zaku kawo ni wannan dakin,?"
"Dariya sosai maganar nata ya sanya su suka shiga yinsa babu kakkautawa."
"Saida sukayi mai isar su kafin suka tsagaita dariyar suna mata kallon sha'awa ďayan yafara takowa gabanta a lokacin da take takawa baya a hankali yana girgiza kai tareda murmushi irin na yan iska" Bayan ya kureta yakai hannunsa zuwa kan fuskan ta da niyar shafan ta, Ganin abunda yake shirin yi mata yasa cikin sauri ta kaucewa hannunsa tana masa mugun kallo, duk da cewa a tsorace take Amman hakan bai yanata yin magana ba."
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AkcjaLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,