🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAPHSAH_M*
(HaneeSat)*Page*
*66*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*Tsaye yake dai-dai k'ofar d'akin ya hard'e hannayensa duk biyu bisa k'irjin sa, a yayin da idanuwansa ke kan su yana binsu da wani irin mugun kallo na nuna b'acin rai.
Zuciyarsa ce ta shiga tsananin mamaki da a binda kunnuwansa suka jiye masa.Tambayar cikin ransa yakeyi. "Shin mafarki nakeyi ko kuwa a zahiri ne?"
Ganin ya kasa amsa tambayar da yake yiwa zuciyarsa hakan ya sanya shi takowa cikin d'akin ya k'araso zuwa garesu inda sukayi tsuru tsuru da idanuwansu a sanda kansu ke sunkuye sun gagara d'agowa bare harsu had'a ido da nasa.
Bud'an baki yayi da niyyar magana sai kuma yayi shiru, a takaice yace
"Ku same ni a mota".
Yana kaiwa nan ya fice daga cikin d'akin, har zuwa lokacin ransa a jagule yake.Dum! dum! zuciyar ko waccensu ke mugun buguwa, tsoro da fargaba ya sanya su rud'ewa, jiki na rawa suka bar d'akin bayan sun d'auki mayafinsu da wayoyinsu.
A haraban gidan suka iske shi zaune cikin motarsa yana jiran dawowarsu, a sanda yake sak'e sak'e a ransa na shi kad'ai yasan irin hukuncin da zai yanke musu, dan sun cuce sa a rayuwa sun gama dashi matuk'a.
Tada motar yayi bayan sun shiga baba mai gadi ya bud'e masa gate ya fice, bai zarce ko ina ba sai gidansu.
A wajan gidan yayi parking motar kafin ya nufi ciki a yayin da suke biye dashi a baya jiki a sab'ule tamkar suyi tsuntsuwa su b'ace sukeji, haka ya nufi b'angaran Abba a bakin k'ofar parloun sukaci karo dashi cikin shirin sa da alamun fita zaiyi."A'a Babana kane tafe war haka bakaje wajan aiki bane!?" Cike da mamaki yayi masa tambayar ganin su Marak'ishiya tafe a bayansa.
Kansa kawai ya girgiza masa tareda fad'in "Abba pls inaso inyi magana dakai mai muhimmanci".
"To mu k'arasa ciki babana, fatan dai komai lafiya?""Lafiya". Ya fad'a a takaice, a yayin da ya k'arasa shigewa cikin parloun.
Dawowa cikin parloun Abba yayi bayan ya amsa gaisuwar da su Shiwari sukeyi masa."Abba, zanyi magana ne yanzu a gaban ka in ai watar da a binda nake shirin ai watarwa badan komai ba face dan ka zame min shaida wani lokacin, ko kuma karkaji lbr daga baya kace me yasa ban sanar maka ba, duk da kuwa nasan akwai a binda na b'oye maka shi kusan watanni baka san dashi ba, amman insha Allahu yanzu zakaji komai da ya dad'e yana faruwa a cikin gidana ba tareda kasani ba".
Tun a sanda ya soma maganar cikin su babu wanda ya iya cewa uffan, illah Abba da ya tattaro da hankalin sa zuwa kansa.
A yayin da yazo k'arshe a zancen sa yakai dubansa kan Marak'ishiya gameda k'iran sunanta cikin iriyar murya yace
"Kije na sake ki saki biyu daga baya zan cikata miki d'ayan, ke kuma! yayi nuni da Shiwari murya a d'age yace
"Ki k'ira min mijinki yanzu a waya kiyi masa kwatancen inda kike yazo ya same mu".Cikin sanyin jiki kamar yanda ya umurce ta dashi hakan ta ai watar ba tareda yin musu ba.
A lokacin da zuciyar Marak'ishiya ya tsananta buguwa jin kalmar saki daga bakin sa bama d'aya ba har biyu, gashi yana ik'irarin cewa daga baya zai cikata mata d'ayan wanda da zaran yayi shi ke nan tsakanin ta dashi babu ko wanne irin aure face idan ba wani auran tayi aka saketa ba.
Hakan da ta tuna ne ya shigar da ita cikin tsananin tashin hankali da nadamar a binda ta aikata a sanda idanuwanta suka cika da kwalla ta d'ago dasu tana kallonsa murya a raunane ta soma cewa.
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
ActionLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,