🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻 *Page

1.6K 68 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀



           *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻

 
*Page*

       *31*

Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃



*Gareki Shatuwa na wannan shafin bata kowa bace illah taki ke ďaya AISHA ĎAN SABO LEMO ahaqiqanin gaskiya bazan boye miki ba wlh naji daďin littafin HAMAL sosai wlh yani shaďantar dani ba iyaka duk da nice HAFSAT  muguwar cikin sa bazanyi fishi ba😉 domin ya ilimantar yafaďakar wlh Shatuwa kinyi namijin kokori posting akai akai kullum 2 page gaskiya ba kamar ki Aishu fatan Allah yaqara miki baseera da kaifin idanu da hazaka keďin daban kike kina haskawa akoda yaushe muna nan muna jiranki har zuwa nan da sabuwar shekara fatan Alkhairi agareki Shatutu mugun tare muke wlh*😚

_Maryam Abdool Mai jambaki na ina miki fatan alkhairi ya Allah yabaki lfy da karfin jiki yasa kaffarace Amen ya Allah sorry_😥


*HANEEFA USMAN*
*AMEENA BATURE* wlh harga Allah  banida kamarku😍


_TUNATAR WACE_👌🏿

_Ingantacciyar  hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzon Allah (SAW)_


*Ankarbò Suhaiben ďan sinanirrumiyya_ Allah yaqara masa yarda- yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sutabba tagare shi yace-:  Abun mamaki ga Al amarin mumini, Lallai dukkan al amuran sa Alkhairi ne,  Kuma babu wanda yakeda wannan sai mumuni  Idan abun fariciki yasame shi sai yayi godiya hakan zai zama alkhairi agare shi idan abun bakin ciki yasameshi sai yayi haquri da juriya hakan zai zama alkhairi agare shi".*

*Akhrajahu Musulimu* Allah yasa mudace 🙏🏿









Tashi tsaye tayi cikin sanyi jikin ta yana ďar ďar kanta a qasa ta kasa koda ďago da kai ne suyi ido huďu zuciyar ta sosai yake dukan uku uku jin irin furucin dake fita daga bakinta gashi ba daman tayi magana taqara haurawa kanta hakan yasata jan bakinta tayi shiru tamkar kurma taja gefe guda batace qala ba illah sauraron abunda zata kuma cewa,,"

Cikin magagin bacci tareda yin miqa ta fito daga ďakin ta tana murzan idanunta tare dayin dogon hamma fuskan ta a ďan kumbure irin na masu baccin da bai gama isar suba dan cikin bakin ciki ta kwana jiya, cike da takaici tana taho ta soma faďin wanne tsinannen mahaukacin ne zai shigowa mutane cikin gida da safiyar Allah saikace gidan uban shi yazo yana mana ihu dan iskan.....cak maganar ta makale mata can qasan maķoshin ta ba shiri ta cafke bakinta da hannayen ta biyu tana zare ido da kyau taga dai Umman ce tsaye a gaban ta ba wani mutumin na daban ba hakan yasa cikin tsarkewar murya a hankali tana muzurai da kai tamkar wacce akebi bashin Kuďi bata biya ba tace, au Umma Ashe kece ke tafe war haka ai bansani ba wlh da yake yanzu farkawa ta daga bacci banyin zaton ke bace,,"

dakata tayi mata nuni da hannu  cikin haďe fuska tace qanwar jatimar kice bani ba marasa kunyar banza nufinki nice mahaukaciya tsinanniyar  ko? to ki tabbatar yana kan jatimar  ki,,"

Aiyya mana Umma Sam fa ba haka nake nufi ba kiyi haquri dan Allah tana ďan rusunar da kanta take maganar iyakar bakinta ya tsaya can qasan zuciyar ta ita kaďai tasan mai take aiyyanawa, baki ta buďe da niyar qara wata maganar  sallamar baba mai gadi yakatse ta hakan yasata dakatawa jin da ita yake maganar cikin bada girma kansa aqasa yace Hajiya kinbar mai Adaidaita sahu fa a waje yana jiran kuďin sa, qara haďe fuska tayi tamkar bakin hadari tare da dubansa tace to gulma ce takawo yanzu kasanar da duniya ban biya kuďin mai Adaidaita sahu ba ko kuwa shi ďan marasa haqurin ne ya aiko ka? Allah ya huci zuciyar ki hajiya aiko ni yayi ya bata amsa jikinsa yana rawa bata kuma qara ce masa qala ba ta juyo da kanta tabisu da kallo ďaya bayan ďaya gameda cewa cikin ku wani yabiya sa kuďin sa a takaice tayi maganar cikin bada umarni dan aganin ta kuďin ďanta ne a gidan sa suke zaune idan wanin su yayi gangancin  ce mata bashida kuďi ma to yayi karya aqalla tasan babu makawa dolene duk sanda zai fita yabarwa ko waccen su kuďi a hannun ta dan haka basu da hujjar da zasuce mata basu dashi,,"

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now