🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT M* *Page*

1.3K 55 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀

        *NA*

*HAFSAT_M*

*Page*

        *55*

Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*





koda gari yagama wayewa tun safe ya shirya ya fice yabar gidan batare da yayiwa koda ďayan su magana ba dan a gurin sa baiga amfanin su a gidan."

    "Wuraren wajan karfe goma na safen lokacin ta farka jikinta babu daďi sam takeji kamar zazzabi ne ke shirin rufe ta ga tsantsan ciwon kan dake damunta har yanzu bai daina ba, ji take kamar ana kwala mata guduma, haka ta miqe tsaye dakyar ta shige toilet tayi wanka da ruwan ďumi tareda yin brush ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atumfa yayi mata kyau sosai ajikinta" turare ta ďauka masu ďaďin gaske tafesa a duk jikinta tashafa mai kafin tazo ta ďaura kwalin kayan akanta, bayan ta gama ne ta fice a ďakin dan ďora shayi, breakfast kam bataga amfanin yin ba tunda kullum idan tayi bayaci saita nemeshi a gidan ta rasa shi."

   "Dukda a daran jiya bataji daďin abunda yafaru tsakanin ta dashi ba irin ďacin maganar da ya yagaya mata hakan bai hanata leqa dakinsa ba, Amman kuma sai taga baya nan alamun ma yafita a gidan"

   "Himm tafaďa cikin ranta tana girgiza kai ta fita zuwa kitchen ďinta ta ďora shayi yana tafasa ta juye shi a plas ta dawo ďakin ta zauna a qasa ta jingina bayanta da jikin gado tana fitar da numfashi a hankali tana rufe idanuwan ta tana buďe su tunani iri iri fal a zuciyar ta,"

   "Haka ta wuni zaune a cikin ďakin batareda ta motsa ba daga inda take ko abinci takasa zuwa ta dafa taci tun safe illah shayin dage gabanta kawai da ta iya sha har yaqare, Sallan  azahar ne kawai ya tasheta bayan tayi taci gaba da zama a wajan" Qiran sallan la'asar da tajine yaqara miqar da ita dakyar ta ďauro alwala tagabatar da sallah tana idarwa ta kokwarta ta fice zuwa kitchen ta kunno garwashi ganin tun gyaran safen da tayi yana nan babu inda bàci hakan yasa ta soma saka turaren wuta ta kunna A C da yake akwai wutan nefa sai ya haďe da daddaďan ķàmshin turaren wutan ya mamaye cikin parloun yana fitar da wata irin ni'ima."

   "A gidan su Abdulmalik Umma ce sanye da mayafi ajikinta ta rataya baķar  jaka a kafaďar ta kallo ďaya tak zakayi mata ganewa cewa tana jikin damuwa domin takasa zaune takasa tsaye sai zirgazirga take cikin tsakiyar parloun tana jiran fitowar siyama ta shirya sutafi kafin yan gidan su dawo dan gashi magariba ta kusa" musamman dama ta qira ta daga makaranta ta dawo gida dan ta taya ta aikin da takeson aiwatarwa dan aganin ta yan iskan yaran nan Batula da suwaiba babu abunda zasu tsinana mata face su ruguza mata abunda tayi niyyar yi musamman batula da batason taga an faďi wani ďacin magana akan humaira anan zatafara karanto mata kabili da ba'adi tana qira mata sunan Allah, ita kuwa suwaiba dolancin tama yafi karfin ta ba tuqin ta iya ba bare ta tuqa sutafi, ko a fannan rubutun ma ba iyashi tayi ba wasa tasaka agaba takasa bawa karatu muhimmanci shiyasa gashi har zuwa yanzu takasa ci gaba a karatu sai baya da take komawa."

"ko jiya da Abba  yaga siyama tadawo gida kuma wai kwana zatayi abun yabasa mamaki saida ya sata agaba yana tambayar ta mai yadawo da ita gida ahalin yasan ba hutu suke ba" Tsuru tsuru da idanu tayi ta rasa wanne amsa zata basa, sanin halinsa ne idan batayi hankali ba zai iya cewa ta koma a yanzu dan bayason shashanci ita kuwa harga Allah taďauki alwashin cewa sai tabi Umma sunyi mata taron walaqanci dan lokacin da Umma tasanar da ita lbrn humaira ta zubewar da cikin ta ba qaramin bàcin rai yasata ba tamkar tayi tsuntsuwa tadawo gida takeji, tsanar ta yaqa daďuwa cikin ranta dama ita sam jinin su baizo ďaya ba" kafin Abba yace da ita wani abu tayi saurin qiqiro masa da karyan cewa lfy ce batada shi shiyasa ta dawo Amman jibi zata koma idan tasamu lfy"" Shiru yayi naďan wani lokaci yana magana a zuciyar sa alamun yana tantama da zanceta dan baiga alaman rashin lfy tattare da ita ba, saidai kawai ya tabbatar da takoma jibi kamar yanda tace dan haka yace da ita ta tashi tabar gadansa."

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now