🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M_S*✍🏻
*9*~*10*
Har yanzu idon ta a runtse yake takasa buďe su zuciyan ta naci gaba da bugawa yana harbawa kamar zaibar ķirjin ta, bakin ta kuwa har yanzu bai daina Ambaton Allah ba, jira kawai take taji tayi masauķi cikin wannan wangamemen ramin,""
Jin shirun yayi yawa kuma ga wani daddaďan ķàmshi dake bugan hancin ta duk yabi ya addabe ta ji take idan bata mance ba kamar ta tabàjin wannan ķàmshin jikin wani,,hakan yasa tayi karfin halin buďe idon nata dan taga gatan da ubangiji yayi mata dan ita dai tasan fitowar ta daga cikin shopping mould ďin bataga kowa a kusa da wajen ba balle tasamu mai taimaka mata,"
Buďe idanun ta farayi ahankali kamar sabuwar waraka daga makanta," tana gama buďewa caraf suka sauķa cikin ķwayar fararen idanuwan shi wanda yakafe ta dashi kamar zai cinye ta murmushi ďauke a fuskar sa,""
Cikin hanzari tayi ķoķarin kwacewa daga riķon da yayi mata hakan yasa ta qara tafiya baya zata faďi," cikin azama ya qara tamķota, wannan karon kam dan gana tayi,dan in tayi wasa qarasawa zatayi ciki,"Wlh zan iya sakin ki ki faďa ciki idan baki tsaya ba, taji ya faďa yana ďan buďe idon sa kamar da gaske,"baki ta murguďa masa bayan ta kawar da ķwayar idonta daga nashi,"
Tsallaka ramin yayi kafin ya ďagota ta tsaya da ķafar ta," fuskan ta har yanzu a tamķe yake ta juya batace dashi ķala ba ta ta kwashi ledojin ta wanda suka zube qasa ta buďe motar ta dan barin gurin,"
Ji tayi anyiwa hannun ta wani irin riqo,hakan yasa ta jiyo da kanta sukayi ido huďu da shi,cikin sauri ta kawar da nata dan bazata iya juran kallon idon sa ba, fisge hannun ta tayi daga nashi,"kafin tace, meye haka zaka wani riqe min hannu saikace kasamu matar ka,tana maganar ne cikin haďa rai,tamkar bata tabàyin dariya ba,"
" Abun nata ma dariya yaso bashi ganin karfin hali irin nata,"wai ace an taimakawa mutum daga jin ciwo,akan yayi maka godiya saima ya tsaya yi maka rashin kunya," juya kai yayi ya nufi shopping mould ďin batare da yafaďa mata abinda yayi niya ba,"
"Thank u yaji tafaďa can cikin qasan maķoshin ta kamar an maqure mata wuya,"
"Murmushi ya ķubùce masa baice da ita ķala ba yayi gaba a ran shi yace kiyi duk abunda kikaso zaki shiga hannu na watarana ,"Ganin kota kanta baiyi ba gashi tuni har an soma ruwan sama jikin ta yafara jiķewa yasa ta buďe nata motar ta shige jikin ta duk yayi sanyi tabar shopping mould ďin zuciyan ta tunkushe da abubuwa iri iri,"gani take sam bata kyauta masa ba, ji take tamkar ta koma tayi masa godiya sosai, dan ba qaramin taimaka mata yayi ba tayi mamaki matuka ganin wannan karon ya sauya mata kamar bashi kece mata zai rama abinda tayi masa ba, haďuwan su ta farko,"
Ajiyan zuciya ta sauķe tare da yafo gyalen ta da ya warware a kanta lokacin da zata faďi ,"
"Wani daddaďan ķàmshin turaren sa ne taji ya doki hancin ta hakan yasa ta saki yar murmushi ta lumshe ido tare da kaiwan gyalen bisa hancin ta tana sinsinawa kamar kare,"Ajiyan zuciya ta kuma sauķewa a karo na biyu," take cewa inama a ce wannan bawan Allahn zai sota da tafi kowa farin ciki, dan duk wani abu da za'a ce mace taso a jikin namiji to duk ya mallake su saidai kyawun hali ne bata sani ba Amman ga dukkan alamu idan ka dubi ya nayin shi bashida matsala gani take duk abinda yayi mata na rashin kyautata wa itace sila,"
Qara gudun motar tayi kaďan dan ganin garin ya ďauki duhu ga ruwa saman da ake har yanzu kar yayi karfi kafin ta isa gida," murmushi ne sauķe a fuskan ta tana addu'ah a ranta Allah ya kuma haďa ta dashi tayi masa godiya tabashi haquri kafin tabar ķasar,"
**
Ana qiraye qirayen sallah ta isa gida, cikin sauri tayi pakin ta kwashi ledojin ta tabuďe motar ta tafita,"
"Bataga kowa cikin parloun ba hakan ya tabbatar da sun shige yin sallah ne,"ďakin ta tashige kai tsaye toilet ta nufa ta ďauro alwala kafin ta cire kayan jikinta da ya jike,ta zura wani dogon rigan shan iska tare da hijabi ta tada sallan ta cikin nutsuwa,"
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AksiyonLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,