🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*36*Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tareDafa kafaďan ta Nurse ďin tayi gameda da sakar mata da yar murmushi tana duban yanayin ta yanda tabi gabaki ďaya tagama ruďewa tace, Haba dai yar uwa wani abunne idan ance kina ďauke da ciki? ai ni aganina murna zakiyi abun farin ciki nefa,,"
"kinga Nurse ya isa haka dan Allah ni muje ki duba ni kafin ki tabbatar min da cewa cikin ne gareni,,"
"Humaira taji sa ya qira sunanta cikin iriyar murya wanda hakan ya sanya ta ďago da kanta, ta kalle shi da idanunta gameda cewa na am,,"
"Bangane abunda kike nufi ba, cikin ne bakiso ki ďauka ko meye ma'anar ki? Aiyya mana dan Allah, nifa ba cikin bane banason ďaukà kawai dai gani nayi kwatakwata yaushe nema mukayi aure dahar za'a ce na ďauki ciki, banda hakama karatu fa zan koma saura min shekara ďaya in kammala, yanzu idan cikin ne gareni, da rainon ciki zanji ko kuma da faman yin karatu?"Ni shine kawai abunda nake dubawa Amman ba...Amman ba miye ba? me kike nufi da haka humaira so kike kice min bazaki ďauki ciki a yanzu ba sai bayan kingama da karatun ki?,'
"Daga baya kenan idan kinga ba iya rainon cikin sa zakiyi ba, sai ki zubar dashi ingani, cikin nuna bacin ransa yake maganar bayan yasaki hannunta daga nashi batare da ya kalleta yakai dubansa ga Nurse ďin dake tsaye ta saki baki tana kallon abun mamaki,,"
"Yace dan Allah gata nan kije da ita ki dubata yanzun nan inajiran result ďin,"
"Karka samu damuwa yallabe, ba matsala yanzu kuwa za'ayi sai kaje ka yanki katin kafin, cewar Nurse ďin, tana maganar takama hannun humaira tace muje ko? ba musu tabi bayanta tana zunbure zunbure itadai harga Allah bataso ďaukan ciki a wannan lokakin ba, niyar ta sai ta kammala da karatun kafin, ta tamkar tayi kuka takeji,,"
"Cikin zuciyar ta tanata Allah Allah a ranta yasa ba ciki bane da ita, dan batasan ta ina zata soma haďa rainon ciki da karatu ba a lokaci ďaya, tana zancen zuci har aka ďibi jinin ta akaje wajan gwaji nurse ďin ta dawo da ita inda yake zaune yana jiran saka mako banda Maraqishiya dake tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zirga zirga take tsoronta ďaya kardau ace ciki ne ďauke da ita dan babu makawa watan mutuwar tane zai kama a wannan lokakin,,"
"Yana hango tahowar su ya mike tsaye cikin zumuďin jin albishr ďin, yace nurse ya akayi me kikagani cikin ne? insha Allahu cikin ne yallabe, yanzu dai mun ďibi jininta zaku iya komawa gida zuwa gobe sai ka dawo ka karbi sakamakon,,"
"Bazai iyu mujira abamu yanzu ba? a a saidai zuwa gobe,,"
"To ba matsala yace da ita nagode sai nazo gobe ďin, bayan yagama faďan hakan ne yakai dubansa garesu yace sai kuzo mutafi ko?,,"
"Bin bayansa sukayi ko wannan su da abunda yake sakawa cikin ransa kowa yana fatan Allah yasa dai ba ciki bane, haka har suka fito haraban Asibitin humaira kam dan haushi ma ko gigin zaman gaba batayi ba, tashige gidan baya a yayin da Maraqishiya kuma ta shige gidan gaba ya tayar da motar suka bar Asibitin, zuciyar kowa da zancen da yake babu wanda yace da juna koda uffan cikin motar tayi tsit tamkar kace kurmaye ne ke ciki,,"
"Wuraren misalin karfe biyu ya isa dasu gida mai gadi ya buďe masa get ya shiga, ko gama parkin baiyi ba humaira ta buďe nata ķofar ta fice, bayan ya gama daidaita kan motar Maraqishiya ta fito tazo ta buďe musu ķofar parloun batare da takai dubanta gareta ba, dan ji take tamkar ta mangaje ta da hannu, ta zube watse nan wajan, idan yaso koda cikin ne da ita sai yayi sanadiyar zubewar sa, a wannan lokakin zata samu sassauci cikin tsakiyar zuciyar ta,,, shi kuwa yana ganin shigar su ya juyar da kai ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallan azahar,,"
![](https://img.wattpad.com/cover/127963149-288-k884667.jpg)
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
حركة (أكشن)Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,