🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*70*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*GARIN KATSINA
Misalin k'arfe tara na dare da wasu d'aurin mintuna, tana
kwance bisa gadonta dake shimfid'e a tsakiyar d'akin tayi rufda ciki a sanda wayarta ke hannunta tana latsawa.K'ofar d'akin taji an murd'a ana shirin bu'dewa, jin hakan yasa tayi saurin kashe wayar ta ajiye shi sannan ta rufe idanunta tamkar mai baccin gaske a cewarta k'ofar a bud'e take, ta ma mance da ta kulle k'ofar da makulli hakan yasa take tsimayar shigowarsa.
Jin yana ta murd'a k'ofar game da k'wank'wasawa yasa ta mik'e zaune ta d'auki wayarta ta kunna tana dafe kanta game da jan k'aramin tsaki tace
"Wash! kaina, wallahi na ma mance da na kulle k'ofar ba ta inda zai iya shigowa idan ba nice na bud'e masa ba, bare ma bazan bud'e ba sai dai kayi ka gaji, idan yaso ka hak'ura ka tafi".Ci gaba da latsar wayarta tayi hankali kwance a sanda murmushi ke shimfid'e bisa lausassar fuskarta, shirun da taji na an daina buga k'ofar d'akin yasa ta kuma murmusawa a karo na biyu ta bud'i baki tace
"Himm, ka yita ta k'are amman bazan bud'e k'ofar n..."
Ba ta kai ga iya k'arasa maganar ba ya mak'ale mata a can k'asar mak'oshinta, sanadiyar ganin fuskarsa da tayi yasa ta kawar da kanta gefe taci gaba da latsar wayarta kamar ba ta san mutum ya shigo cikin d'akin ba, sai dai kuma mamaki take a cikin ranta a ina ya samu irin makullin d'akinta har ya bud'e Ya shigo? "ko dan gidansa ne a nan na iske shi". Ta fad'i hakan a cikin zuciyarta tana tab'e baki.
"Yanzu dama kina cikin d'akin nan nazo nayi ta bugawa ina k'iran sunanki ki bud'e min k'ofa amman kika yi banza dani sai yi nake kamar tab'ab'b'e! Da bani da wani makullin da shi ke nan sai dai in hak'ura kenan?". Yayi maganar cikin sigar mamaki a yayin da ya iso gareta yayi tsaye yana kallonta.
Shiru tayi masa tamkar ba taji abunda yace ba, illa ma zama da ta gyara a sanda idanunta ke kan fuskar wayarta sai kayi zato wani abu mai muhimmanci take yi.
Da ke fa nake magana matar!" Ya k'ara fad'a cikin dakiyar murya mai cike da tsantsan mamaki.
Wannan karon ma shiru tayi masa tana ci gaba da latsar wayarta, ganin da gaske ba niyyar kula sa take dashi ba hakan yasa ya zauna a bakin gadon daf da ita yana murmushi ya kalleta daga saman fuskarta har zuwa k'asar k'afar ta, a sanda take cikin tsararran shiri tana sanye da inglish wears wanda ya zauna mata a jikinta yayi mata kyau sosai, a yayin da kuma gashin kanta ke cikin gyara ta mishi tufka d'aya sai shek'i yake mai, ban da haka ga daddad'an k'amshin turaren wuta dake tashi a cikin d'akin, sai ya zo ya had'u da sanyin A C yake fitar da dad'in ni'ima.
Idanunsa ya lumshe sannan ya bud'e su yana jin wani irin tsantsan kewarta a cikin zuciyarsa, zama yayi a bakin gadon daf da ita yana murmushi, a hankali ya d'aura hannunsa kan tausasshiyar k'afarta ya soma murza yatsunta yana mai kallonta yanda tsarinta yake, dan ba k'aramin kyawu yaga tayi masa ba, gani yake taba tab'a yin kyau irin na yau ba,Numfasawa yayi a sanda yake fad'ad'a murmushinsa yace
"Matar, mu je ki bani abincin da zan ci ya toshe min yunwar da ke cin cikina, dan naga alamun yau kina ji da shan k'amshi, ni da nake mijinki ma sai ja min aji kike, dan haka ni dai yanzu muje ki bani abincina inci da sauran hakkina dake kanki, idan yaso sai kina kwana ke kad'ai kullum kina shan k'amshinki, amman fa sai bayan kin gama bani ko wanne irin hakkina gaba d'aya sannan". Ya k'arashe maganar cikin sigar wasa.
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,