🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*26*
Dedicated to my besty *AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sai ke tawan_
_Nidai yau najarabtu da abun takaici yafi kusan biyar ina editing yana gogewa bansan meyasaba wlh har nagaji dayi tunjiya nake abu ďaya Amma ina kusan gamawa sai wayar ta mutu dakanta ta kunnu idan nashiga sai naga yagoge min gyran dana yi wlh har nagaji kukane kawai yarage min_🤧🤧
*Gaisuwar wannan page ďin gabaki ďayan sa takice my sister HAUWA SAMASHER keďin daban kike cikin mutane bazan bòye miki ba ina mai farin cikin kasancewata nice mawallafiyar littafin KADDA KO SAKACi nagode sosai SMASHER fatan Allah yaqara hazaqa kina haske akoda yaushe muna tare*🤞🏿
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY BIRTHDAY 2 U MY QAWALLI HANEEFA USMAN FATAN ALLAH YAQARO MIKI SHEKARU MASU TARIN ALBARKA CIKIN ADDININ MUSULUNCI AM SO HAPPY FOR U DEAR*🎂🎂🎂🎂🎂
*HBD again and again is ur time hanefuna ana mugun tare babu rabewa*😘🌲 *YAYI SAKE*🌲
*NA AISHA A'MUHD*
Ban mance dake ba wlh
*JINJINAR BAN GIRMA GAREKI YAR UWA BA SHAKKA KINYI NAMIJIN KOKARI MUNGA SAKON DA KIKA ISAR MANA TABBAS YAYI SAKE YA FAĎAKAR YA NISHAĎANTAR FATAN ALLAH YAQARA BASIRA DA HAZAQA, DUK WANDA YABARI BAI KARANTA BA AYANZU TO BA SHAKKA ZAIYI SAKE KO INCE YAYI SAKE* 😜 *SAI MUN JIKI ASABON LITTAFIN KI NAGABA MADAM AISHU, MAI SHERIFF KE MIKI FATAN ALKHAIRI*🙏🏿Yau tunda asuba bayan ta idar da sallah tayi azkar tare dayin addu'oi sosai tana nan zaune tana tasbihi har garin yasoma hasken rana,,dogon hamma ne yazo mata idonta yana rufewa alaman baccin bai isheta ba, tashi tayi ta haďe sallayan tare da ninke hijabin bayan ta cire ta ajiye su a mazaunin su tana tangal tangal kamar zata faďi taqara hayewa kan gado taja bargo ta rufe duk jikinta idanunta a rufe sabon bacci mai nauyi yasake ďaukanta,,"
Har wajan misalin karfe goma bata farka ba, lokacin tuni har sun kammala da karin safe jin shiru baiga fitowar taba gashi office zai wuce yasa yayi hanyar ďakinta dan ganin ko lfy take, a hankali ya tura ķofar ďakin ya shiga yana sanye cikin farar shadda kaftan kansa sanye da hula ďinkin bama kansa da hula ďinkin bama sai ķàmshi ke fita a ajikin sa, kwance ya hangota dukunkune cikin bargo da alamun sanyin A C yana shiga jikinta sosai tamkar dole aka sata kwanciya cikin sanyi, kai ya girgiza ya qarasa bakin gadon ya zauna bayan ya kashe mata A C lausassar hannun sa yakai bisa gashin kanta wanda ya kwanta mata luf a gaban goshinta ya kawar mata ganin zai iya shige mata duk sanda ta farka, a hankali yakai ďan madaidaicin bakinsa kan nata ya sumbace ta fuskar sa ďauke da murmushi yashafi kanta abu dayawa yake sakawa cikin ran sa shi ďaya yasan me yakeji tattare da ita saida yaqara sunbatan ta a gefen fuskanta kafin daga bisani ya miqe ķàmshin daddaďan turaren jikinsa duk ya gauraye cikin dakin ya fice yaja mata ķofar ya rufe kai tsaye bai tsaya yin komai ba ya fice haraban gidan ya nufi inda motar sa yake ya shiga tare da tasharwa baba mai gadi ya buďe masa get ya yafice,,"
Ba ita ta farkaba sai wajan wuraren karfe goma sha ďaya, a hankali ta buďe idon ta tana murzawa tare dayin miqa bakinta ďauke da salati ita kanta tasan tayi bacci sosai yaukam ba kaďan ba murmushi ne ya bayyana a fuskan ta jin kamshin turaren sa ya gauraye cikin ďakin ko ba'a faďa mata hakan ya tabbatar mata da cewa ya shigo cikin ďakin, ganin yanda lokaci yatafi sosai gashi aiki ne sosai da ita yasa tayi gaggawan tashi tsaye ta shige toilet, wanka tayi tare dayin brosh kafin ta fito ďaure da babban towel ta goge jikinta cikin sauri ta shafa mai kafin tafeshe jikinta da turaruka ta zari dogon riga nashan iska ta saka ta ďaure kanta da ďan kwalin sa, bata tsaya bata lokaci ba ta gyare ko ina na ďakin nata yayi fesfes dashi ta wuce toilet ta gyara abunda yakamata ta gyara da yake jiya ta wanke shi hakan yasa babu datti sai ďan abunda baza'a rasaba,, tana kammalawa ta fice a ďakin tareda jan ķofar ta rufe,,"

YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,