🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M_S* ✍🏻
*page*
*14**YA YAN UWA NA MUSULMAI GAWATA YAR GARABÀSA KAĎAN, Watarana manzon Allah (SAW)yafita zagaya gari shida sayyidina Abubabar (R.A), sukazo wucewa kusada wata rijiya sai Annabi (SAW)yacema sayyidina Abubakar "ďauki dutse ďaya kajefa acikin wannan rijiyar" Haka kuwa akayi yaďauuki dutse karami yajefa acikin rijiyar, sai manzon(SAW),yace mutafi sukatafi abunsu sai ranarda dutsen yacika shekara ďaya da jefawa Annabi (SAW),yasake ďaukar sa suka tafi wajan wannan rijiyar bayan sun isa sai sayyidina Abubakar yaji karar faďawar abu acikin rijiyar sai Annabi (SAW) ,yacemaAbubakar kokasan menene yafaďa sai Abubakar yace a'a. sai Annabi (SAW),yace dutsen daka jefa wancan lokacin damu kazo yau shekara ďaya kenan sai yanzu yakai ķarshen rijiyan,kuma wlh babu wanda zaishiga aljannah har sai ladarsa tacika wannan rijiyar, Hankalin Abubakar yayi matukar tashi yazo yasami sauran sahabbai azaune yace mekukeyi azaune ai wlh zama bai samemuba sai yagaya musu yanda Annabi yace Suma hankalin su yatashi sukaje suka tunkari Annabi (SAW) sukace Ya RASULILLAH mukam a ina zamu iya aikin dazai cika wannan rijiyar?Sai Annabi (SAW)"yace ku kwantar da hankalin ku akwai aiki ďaya wanda idan ďayanku ya aika tashi to zai samu lada wacce tafi wannan rijiyar yawa, Annabi (SAW) yace idan ďayan ku ya furta kalmar LAILAHA ILLALLAH a asirce kuma yana mai kaskantarda kansa zuwa ga Allah zai bashi lada wacce taninka zurfin wannan rijiyar sau uku.Yan uwa kuji falalar dake cikin wannan kalmar Ya Allah kabamu ikon faďar wannan kalmar TA LAILAHA ILLALLAH 🙏🏿🙏🏿🙏🏿*
Zaune take a gaban madubin ďakin su tana shafa mai a jikin ta da alama fitowar ta a wanka, doguwar riga ta atamface a jikin ta, sama sama tayi kwalliya bayan tagama shafa man ta mai ķàmshi, tafara feshe jikin ta da turaruka,"
Ganin batada niyar gamawa, gashi lokaci na wucewa yasa Amena ta tashi tsaye taje inda take tace,"
Kinga malama wlh banason walaqanci idan fa bazakije ba zanyi tafiya ta, nagaji tun ďazu nagama shiri nake zaman jiran ki Amman kin tsaya kina kwalliya kamar ance miki wajan gatsar kyau zamuje, indai fa bakida abun siya kifaďa min zanyi tafiya tace da ita tana kakkame fuska dan tagaji da jiran ta,"
Tashi tayi a gaban madubin ta zari mayafin ta kalan atamfar jikin ta da jakar yar qarama, ta juya tace to uwar korafi sai kizo mutafi ai ko?,""
banza tayi mata bace komai ba suka jera suka fita,"" shopping mould dake kusa dasu suka taka suka shiga kowa yafara ďaukan abinda ya kawo shi,""
Tana tsaka da zabàn kaya ta iso gun agoguna masu masifar kyau da tsada, harta wuce sai kuma ta dawo baya, fuskan ta ďauke da murmushi ta zabì agogo guda ďaya mai kyau kalan baki, kafin ta juya tabar wajan,
Gun Amena ta wuce tace idan kin gama mutafi ba? nagama ta bata amsa sukaje gun biya kowa yabiya nashi suka fito dan komawa hostel,"
Suna tafiya suna taďi Humaira tana bama Amena lbrn yanda komai yatafi cikin sauki tsakanin ta da Abdulmalik," cikin jin daďi Amena ta rungume ta tace kai qawata gaskiya na tayaki murna Allah ya sanya alkhairi, yanzu yaushe ne auran naku musha biki ?," dariya tayi tace kefa kinga matsala ta dake kenan kin cika zumuďi, to ba'a dai saka rana ba Abba yace sai na dawo za'a sa,
Yoo meye ya rage ai da an saka yaune fa komawar tamu nifa wlh duk kin gigitani ji nake kamar ace yaune ma auran Amena tafaďa tana mata dariya,"""harara ta kai mata tace to sannu uwata uwar hanzari yanzu ma zaki iya aurar dani ai, tunda na takura miki,"
Kedai kikasani Amarya gidan Abdulmalik",
Himm kawai tace sukaci gaba da tafiya, Amena dai bata fasa ba sai zolayar take,"
YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,