🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*25*Dedicated to my besty
*AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sa ike_*Yan zauren Biebie isa gaisuwar wannan shafin gabaki ďaya takuce Aminan juna yan mutunci* 👇
_Shukrah Cute_
_Auntie jamiey_
_Meenarh Parrot_
_Amal BaibiiAna mugun tare iya wiya_🤝🏿Shukura ina miki barka da murna na kammala littafin Ranar suna da kikayi fatan alkhairi Allah yaqara basira na jinjina miki matuqa sai munjiki ana gaba kuma Ranar wanka 😜
*Zan iya cewa taki gaisuwar daban take ďiyata Meela Adeel fatan Allah yabar zaman tare karki samu damuwa autana bazan zauna ina gani wata Neesah takwace miki Adeel ba, kece kaďai kika cancanta da Adeel kinji ďiyata*😁
Ido ya zura mata yana kallon ta gabaki ďaya ya tattara hankalin sa yamar dashi kanta ganin yanda ta harďe hannayen ta duk biyu waje ďaya idon ta na zubar da kwalla alamun nadama qarara a fuskan ta,,,ajiyan zuciya ya sauķe yana cigaba da duban ta sosai kamar mai nazari kafin daga bisani yasa hannayen sa duk biyu ya dafa kafaďun ta tare da ďago da ita ya zaunar ta kusa dashi yana kallon cikin kwayar idanun ta ya buďi bakin sa ya qira sunanta a hankali yana riqe da hannayen ta cikin nashi yace,,"
Maraqishiya, na'am ta amsa masa cikin qasa da murya batare da ta ďago ta kalle shi ba,
kinsan dai inasonki ko? auran soyayya mukayi nida ke ba auran haďi ba, dan ina matukar kaunar kine yasa na auro ki badan komai ba ke kanki kinsan a iya zamana dake ban tabà tauye miki wani hakki naki ba ban kuma tabà nuna miki rashin kyautatawa ko gajiya dake ba ko kin tabà ganin sauyi daga gareni a iya shekarun da mukayi dake?? kai ta girgiza masa alaman A a, yaci gaba da cewa to meyasa kike tunanin auran dana qara kamar nayi ne ďan na daina sonki ne ko kuma nayi tane da wani manufa har yasa kike abu kamar hauka? shiru nan ma tayi tanajin sa yace kibani amsa mana inajinki,,""Kanta ta ďago suka haďa ido dashi tana qara tamqe hannun sa cikin nata tayi qasa da murya kafin tace nidai kayi haquri dan Allah mijina ka mance da duk wani abunda yafaru a baya nagane kuskurena irin haka bazai tabà qara faruwa ba daga yau zan riqeta Amana zamuyi zama tamkar ya da qanwa nidai kayafe min kawai nasan nagaya maka maganganu masu ďaci marasa kan gado wanda ban tabà gaya maka irin makamancin su ba cikin bàcin raine wlh duk sharrin sheďan ne da huďubar sa pls dear nayi alqawari bazan kuma ba, kanta ta kifa kan kafaďun sa idonta na cigaba da zubar da kwalla tana shashsheqar kuka,,,hannayensa duk biyu yasa ya zagayo ta yana lallashin tare da bubbuga bayanta kafin daga bisani ya ďago da kanta yana share mata hawayen fuskan nata yace,,"
kiyi shiru kukan ya isa haka na yafe miki, komai ya wuce fatan bazaki qara maimai makamancin irin hakaba? kai ta girgiza masa tana murmushi,,jin daďi,, shima sakar mata da murmushin yayi cike da kauna ya ďaga kansa ya kalli humaira ya sakar mata da qayaraccan murmushi a ran sa yake faďin ohh kishi kumullon mata ganin yanda tayi kicinkicin da fuska ta zuba musu ido tunda suka fara magana take binsu da kallo ko ķeftawa babu,,saurin kawar da nata idon tayi dan bataso ta haďa da nashi tana wasa da spone ďin hannunta tana jujjuya abincin dake gabanta ji tayi duk abincin ma yafice a ranta, qasa qasa yayi dariya yadawo da duban sa kan Maraqishiya yayi mata nuni da taje ta bata haquri su sasanta junan su tunda duk wani tashin hankalin da tayi ma itane dalilin an auro tane badan komai ba,,"miqewa Maraqishiya tayi tana ďan murmushin dako baki bai iso ba dan dole takeyin wannan abun badan tanaso ba Amma ya zatayi tunda babu tafara isa gareta tayi ta zauna kan kujerun dake kusa da ita,,tana kallon cikin idonta ta kamo hannayenta ta haďe da nata cike da iya magana tafara tacewa,,"

YOU ARE READING
RAYUWAR AURENA
AcciónLabari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,