A sunny day🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT*- *M*- *S

9.8K 384 8
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR*  *AURENA*🥀🥀🥀



      *NA*

*HAFSAT*- *M*- *S* ✍🏻

*1* ~*2*

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIRRAHIM*
*DA* *SUNAN* *ALLAH* *MAI RAHAMA* *MAI JIN'KAI* *DUKKAN* *YABO* *DA* *GODIYA* *SUN TABBATA* *GA* *UBANGIJI* *WANDA* *YA BANI* *DAMAR* *RUBUTA* *WANNAN* *LITTAFIN* *ALLAH* *KASA* *NA GAMA* *LAFIYA* *AMEEN*

*IDAN* *NAYI* *KUSKURE* *A CIKI* *ALLAH* *KA YAFE* *MIN*

~~~~~~BABIN FARKO

Tuqi take akan titin cikin kwanciyar hankali da nutsuwa motar ta mai qiran passat.   Ahankali take tafiya kamar wacce batason tuqawa.. Duk da kuwa yanda motoci suke kara kaina akan titin hakan bai hanata tafiyar ta ahankali ba..

  " Kanta tadan  kwantar a jikin kujeran motar  tana sauraron karatun al qur'ani mai girma muryan al sudais wanda da dukkan alamu idan kaganta zakasan cewa tanajin daďin karatun,,

  " Matashiyar budurwa ce wacce aqalla shekarunta bazasu wuce 18 ba """ Sanye take  cikin baqar abaya wadda babu wani ado ajiki illa dan stons da aka zagaye hannuntà dashi gyalen abayan tayafa a kanta,

" Kyakkyawar budurwace ta gaske fara Amma bacan ba kuma ba ruwan tarwaďa ba farinta daidai misali wanda kallo daya zakayi mata kasan cewa ruwa biyu taďauko""  Tanada dogon hanci Amma ba sosai ba sai dan qaramin bakinta madaidaici tadan shafa mishi jambaki kadan sai idonta da tasa masa gaxal  sai yaqara mata kyau sosai

   Cigaba tayi da tuqin motar duk ta miķa hankalin ta kan titin tana kallon yanda motoci keta gilmawa  masu mita sunayi masu kallon ta suna kallon ta..

  "   Phone dintane yafara ringing tajuya tamika hannu cikin qaramin jakanta madaidaici taďauka dan duba wake qiran ta ""

" Ya salam tafada tare da dafe kanta sanadiyar sunan wanda tagani a fuskar wayan..

" Daidaita kanta tayi kafin ta amsa wayar,

    Jikin ta na bari tace Hello yaa mahmud tana dan wuri wiri da ido kamar marar gaskiya,,

"  Ji tayi yace mata Dan qaniyarki wayabaki izinin daukar min mota kifita da ita bansani ba ?""

  "Shiru tayi masa batace komiba jikin ta kuwa cigaba yayi da bari dan ita kam harga Allah ta mance motor shi ce ta ďauka'

" Tsawan da taji yadaka mata ne ya sanya har wayan hannun ta yafaďi qasa saura kadan tuqin da takeyi ya kubuce yabar hannun ta.

Saurin daidai tawa tayi akan titin kafin ta   sunkuya taďauki wayar tamayar dashi kunnen ta"" 

  Ji tayi yaqara cewa badake nake magana ba kinyi ma mutane shiru wato  mahaukaci kika mayar dani ?

" Girgiza masa kanta tayi kamar tana gabanshi

" takwabe fuska Tace aiyya yaa mahmud wlh nazo nefa fita da motar mummy sai naga babu dana tambaye ta sai tace min kafita dashi shine tabani naka tace inje dashi..

     Meyasa bazaki qira ki fada min ba,?? Da kike cewa mummy ce tabaki izinin ďauka  Motar tawace ko nata ?' Ya tambaye ta

" Nanma shirun tayi masa batace komai ba

   "Yace  badake nake magana ba kinyi shiru ga dan iska kenan ko ?


" A a tafada tana girgiza kanta..

    "To bari kiji in fada miki wlh wlh kinji na rantse idan kika kuskura kika bari wani abu yasamu mota na  Allah sai nayi mugun saba miki naraba ki da wannan shegen ķafar mai son yawon tsiya kuma kiyi hanzari ki dawo min da mota na tun kafin raina ya gama baci kinji nagaya miki tunda ke halinki ďaukar abun mutane ne basu sani ba Yana kaiwa nan taji ya kashe wayar qit,

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now