CHAPTER 6

1.9K 138 50
                                    

Kamo hannun sa da sauri tace da gaske kake sweetheart finally zaka aure ni? Yace eh naga ke daya ce kike iya kokari wajen kula dani sauran matan lusarai ne. Tatoon dake jikin sa take bin zancen da yatsan ta tana saurarensa yaci gaba da cewa su iyayen nan nawa sun kasa ganewa nima fa zinar nan da kika ga ina yi ba laifi na bane Allah ne yayi ni a haka.

Toh ya suke so nayi in sunyi min aure matar tamin karama suce na saketa idan na saka kuma sucemin bazanyi zina ta ba toh wai nikam in sha'awar ta taso salatin da iza ja'a zanyi ta koma? Dariya tayi tana dukan kirjinsa tace baby na dama kai mai wa'azi ne zakayi kyau.

Turbune fuska tayi yace ke banason shiririta ke ba'a isa a sako zance na masu hankali ba sai ki sako kin shirme. Tace sorry mine toh na dena. Tureta yayi yace ke ni banason karuwanci matsamin na je na yi wanka.

Yana kaiwa nan ya cilla Mata rigansa ya shige bandaki ya cika bathtub harda saka su turare yayi luf a ciki. Itakuwa sakin baki ma tayi ta ma rasa me zatace wai ita yace ma karuwa? Toh AI in its karuwa ne shi kuma fa?

Kwafa tayi tace nasan maganin ka. Kayan da yafi burgesa tasa tayi Dane Dane a gado tana latsa wayarta wajen 30 min sai gashi ya fito. Zuwa yayi ya kwanta a gefe da niyar ya shareta Dan yaga tana cin magani kar ta kawo masa raini amma kamshin turarenta ya hana shi yin bacci kamar yadda takeson yi Dan shi sallah ba a gabansa yake ba.

Hannunta ya rike tace ka sake ni lud ka sake ni nace. Tashi yayi ya zauna yace ke mahaukaciya me kike nufi? Tace toh me zakayi da karuwa ? AI kai mai tsarki ne mai tsafta sai mai tsafta ce daidai da mai ko ?

Jin jina kai yayi yace wow! wow!! wow!!! Sally congrats kinyi baki it seems like sati dayan da nayi bana nan saboda nayi aure yasa kika manta waye ni ko?
Sauka yayi daga gadon ya dauko wandon daya tube ya zare belt din jiki tana ganin haka tasan ta tabo ma kanta. Hakuri ta fara bashi tana my baby kayi hakuri mana wasa fa nake kai bakasan irin wasan nan na masoya ba? Murmushi yayi yace darling AI nima tawa irin wasan zan nuna miki yana fadin nan ya daureta a gado a kife.

Ya rufe ido ya tsula ta da belt a mazaunanta tana kururuwa tana komai tana hadasa da girman Allah har layi ta Dan Saba ta hadasa da girman iyayensa yace ke baby da kiketa korafi wasan fa bai kare ba Dan wannan wasan karfi ne yanzu zakiji dayan. 😭 haka ya kamata ya murkesheta kuma harda mugunta a lamarin nasa. Wannan shine jimirin duk maven da ta mayar da kanta matar wani babu aure. WULAKANCI DA KASKANCI!

Zama tayi a gefe ta hada kai da guiwa tana kuka shiko baje wa yayi a wajen zaiyi bacci yace ke kin cika min kunne. Tace Allah ya isa na. Mikewa ya fara shirin yi yana fadin dama ban koshi ba zo nan Dan...... ki

Washe gari marakisiyya tayi shirin makaranta tsaf amma ta rasa ta ina zata hada ido da m. Ahmad toh tace masa me ? Yanzu wani irin kallo zai dinga yi Mata? Parlourn mahaifinta tayi sallama ya amsa ta shiga ta tsuguna tace dad good morning.

Shafa kanta yayi yace morning my daughter anyi shirin makaranta ne? Tace eh daddy yace toh masha Allah a dawo Lafiya Allah ya bada sa'a. Cigaba da karanta jaridarsa yayi shiru shiru bata Mike ba yace daughter kinason wani Abu me ko bakida kudi ne?

Sauke kai tayi kasa tana wasa da yatsarta tama rasa ta ina zata fara tace umm dama.... dama nace Dan alkah kuyi hakuri da abinda ya... ya faru jiya na biye ma yaya lud mukayi muku tashin hankali a gida. Ajiyan zuciya tayi yace babu komai daughter nasan ba halinki bane kina da tarbiyya da ladabi kuma laifin mu tafi yawa a cikin lamarin nan especially ni da nake kareshi bana bari a gwaba tun yana yaro sannan kuma duk sanda muka samu rashin ji ruwa bama boye wa.

Yanzu ki duba abinda mukayi jiya har kunyan tunawa nake muma kuyi hakuri ku yafemu yar albarka.

Shiru tayi yace ko akwai wani maganan ne? Tace uhmm dama... nace maganar da kikayi da umma ne dad a Dan dubamin Dan Allah ka tausaya min. Sarai ya gano inda ta dosa amma sai yace wace magana kenan?

Tace batun nan da kace... sai...sai na gama makaranta yace kinzo da magana mai girma marakisiyya amma insha Allah zan duba ba gani an Jima ko zuwa gobe zan neme ki. Murmushin jin kunya tayi ta Mike a guje tana fadin daddy na gode Allah yabar min kai.
Shima dariyar yayi ya kurbi coffee dinsa kamin yaci gaba da karatun sa.

Tana isa makaranta kamin ta shiga gate su mansura suka tare ta shiga motar sukayi suka rufe kofa kirif sa shike tinted ne Dan haka basuda damuwa Dan babu me ganin abinda suke.
Beeba tace babe skill dinki na acting a secondary zakiyi using Dan wallahi da kyar muka ceto ki.

Mansura tace beeba baki iya bada labari ba ni zan bada wannan. Kinga... ta fada tana dafa kafadar marakis tace muna zuwa office din HOD muka samu class rep sun hada miki bomb wai biniyar wannan yaron kike shi kuma yace Sam bazai aminta da ke ba. Shine wai saboda kinyi zuciya kikace in bazaki anfana da ita ba toh babu mai anfana wai shine kika hankadesa da gangan kika taka masa girmansa.

Marakisiyya ta kasa rufe bakin ma tace amma wannan anyi Dan munafuka toh ku me kuka ce? Beeba tace nuna masa mukayi cewa mi Mata ne mun fisa kisa tun kamin mu shiga office din muka saka su bandage abin mu gashi kina kallo sai next week zamu cire.

Mansura tace muna shiga muka jira ya gama tsarinsa sai muka fara namu cewa nayi shine yasa miki ido tun muna 100L har gida yake abinki yana kofar miki samari amma tausayinsa yada baki fadawa dad dinki ba. Kuma ace mace kyakkyawa irinki ki rasa miji ko saurayi? Toh shine muka ce AI shine ya toshe miki baki ya kaiki empty class zaiyi lalata dake mu kuma muka yi kokarin cetonki amma sauran yan clique dinsu suna gadi sune suka dake mu shi kuma ya dakeki saboda kinji bashi hadin kai.

Toh da kika samu dama shine kika take abin nasa hakan yasa abokansa sukayi mak mugun duka Wanda ya janyo bazaki iya zuwa school ba. Shine HOD yace zaiji daga bakinki amma dukda haka ya tsige class rep idan harda hadin bakinsa akayi kuma indai gaskiya ne labarin mu toh kin zama class rep.

Dariya ta kyalkyale dashi suka tafa tace kai tazo mu jira irin Wanda jarya haka Anya kuwa mala'iku zasu barku? Mansura tace banison wulakanci fa yanzu dai daure miki kan da hannu zamuyi da kin isa gida sai ki dinga cirewa bayan kamar sati haka toh zamu daina sawa minsan na iya makeup zan mana tabon karya. EVERYTHING IS FSIR IN WAR AND LOVE inji bature.

Marakisiyya tace gara da kika ce inju bature fa. Toh amma kinsan dole department din zasu rubuta apology letter to my residence ya zanyi kenan a gida za'a gane kuma kashin my ya bushe Dan korar my za'ayi na sani. Mansura tace eh zakisan yadda zamuyi tackling wannan din yanzu dai mu shiga

..........

Lud ne tsaye a kofar hotel din yana ta kallon agogo wayarsa ya dauko ya daddanna yace hello ! Baby ki dmfito da wuri mana kinsan ina kiranki fa. Tace dear sorry ganinan saukowa kasan jiya kamin mugunta. Murmushi yayi yace sorry AI in banyi muguntar ba ban cika ni din ba. Tace wannan haka yake gwarzo na. Bayan minti daya sai gata da tshirt da Jean ta daura kimono akai Rana shiga ya kalleta yace toh menene na daura wannan buhun akan kayan ki? Zaro ido tayi tace buhu kuma? Yace wannan fafalos din Rigan saman mana cireshi don Allah tace haba dearie wajen sirikai fa zani.

Shiru yayi yana kallon gabansa Wanda daga yayi hakan toh tasan gara tayi abinda yace cirewa tayi ya fincike turban din ma dake kanta ya kalleta da kyau yace perfect sannan ya kunna motar sai gidansu.

KAI JAMA'A A DUNIYA ANA KARYA,KO SHIN KUNGA LAIFIN SU MANSURA DA SUKAYI KARYA? ME ZAKU IYA CEWA GAME DA ZANCEN DAD DA MARAKISIYYA? SHIN KUNA GANIN WAHALAR TA YA KARE KO DA SAURA?

MAI ZAKU IYA CEWA GAME DA YADDA SAILUBA DA LUD KE ZAMANTAKEWA? YAYA SU UMMA ZASUYI REACTING IDAN SUN GA MATAR DA YA KAWO MUSU? ZASU HANA KO ZASU YARDA? IDAN SUN HANA MAI LUD ZAIYI?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

25th July,2020.

YA JI TA MATAWhere stories live. Discover now