Ba tare da bata lokaci ba Dan dolen ta ta bude ido war. Tsaye yake da tulelen tumbinsa yan washe Mata wasu hakawaran sa kamar jeren alkama yace wow hotel dinnan sunyi ashe har budurwa yar kasar masar ake kawo wa.
Daga shiga wanka kawai sai na fito na tsinci yar shila? Cikin bari marakisiyya ta kara kankame gyalenta tana goge hawayen da batasan ya zubo Mata ba tace Dan Allah kayi hakuri kuskuren daki aka samu.
Ajiyan zuciya tayi yana lashe baki ya zauna a gefen ta da sauri ya ja baya yace Ayya daga gani ke sabuwa ce a harkar nan ko? Look innocent prostitute ki saki jikin ki kawai ki kwashi naira.
Ke daliba ce? In ke daliba ce kawai ki fada min jami'ar da kike da ajinku sai MATRIC number dinki shikenan babu ke babu carry over. Dube dube ta fara tana neman abinda zata rotsa masa. Yayinda ya kamo bakin gyalen ta.
Hankade sa tayi tace dalla matsa daga jiki na ni ba yar iska bace amarya ce! Tsayawa yayi cak ya biya da kallo kamar na second biyar kawai ya fashe da dariya yace AMARYA A HOTEL? ke kinga alamun nasha kwaya ne. Yana kaiwa nan ya sake nikita.Kokuwa suka fara yi yasa hannu ya toshe Mata baki yana shirin zube Mata zip din less din dake jikin ta.
.......
M. Ahmad zaune yana aiki a laptop yayinda m. Salis ya kwanta cinyar sa yana masa shagwaba sama sama yake jinsa kawai yana masa murmushi yayinda yake shafa kansa domin shi a kani ya daukesa ba komai ba. Ko ranan ma da aka samu matsala kasa jurewa yayi amma komai ya warware.
Shima m. Salis din a yaya ya daukesa domin tsakanin su akwai shekaru kusan 6 dalilin da yasa kuwa yake Abu kamar mace saboda an Riga da an sabar masa ne Wanda yana kokarinsa wajen danne wa da komawa namiji. Shine in yana magana sai kaga kamar yanga yakeyi.
Wayar m. Ahmad dinne tayi kara ya duba yaga vc ke kiran sa. Da mugun mamaki yake bin wayar da kallo. Vc yana neman level coordinator? Bawai yasa a kirashi ko a turo letter ba? Toh Allah yasa lafiya. Ajiyar zuciayan kwado yayi ya dauka da sallamar sa suka gaisa vc din nasu bashida girman kai.
Nan take sanar dashi yayi bako ne na kunya Dan siyasa ne amma baya gari kuma bakon dama tsayawa yayi na kwana daya su gaisa da vc din kamin ya wuce gaba. Toh shine ya duba yaga a staff dinshi m. Ahmad na daya daga cikin masu gaskiya da kuma hankali dama kuma can akwai Dan sani tsakanin baban m. Ahmad da vc din.
M Ahmad din yace okay sir ba damuwa insha Allah yanzu zanje ko? Vc din yace yeah yanzu zaka je. Kaji ko yana da wani Abu da yake bukata. Zan turo maka address din yanzu.
M. Ahmad yace toh ba matsala sir. Tana kammala wayan m. Salis yace ya akayi? M. Ahmad yace tashi ka shirya zaka rakani anguwa ne. Gyada kai kawai m. Salis yayi ya Mike shima suka shirya suka fita zuwa hotel din. Bayan sunje reception anan aka sanar musu da room number din mutumin tare da yi musu gargadi cewa minti 15 garesu dan 12 na dare yana yi za'a daina kawo ziyara saide kama daki.
A hankali m. Ahmad ke taku yana bin kofar ko wani daki da kallo Dan tun dazu da ya baro marakisiyya gaba daya jikin sa yayi sanyi. Jin kamar ana bige buge a wani daki yasa suka hanzarta domin da alamu ba lafiya ba. Har m. Ahmad zai bude m. Salis yace kul bro ka manta nan hotel ne zasu iya Kira maka yan sanda ayi filing case kayi INVERSION OF PRIVACY.
Juyawa m. Ahmad yayi zai wuce kawai sai ya juyo yace ba nan dakin zamu zo ba? Kalli room number din. Cizo marakisiyya ta gantsara masa hakan yasa ya hanzarta sakin ta yayin da ta fara ihun neman taimako. M. Ahmad najin muryar ta baisan yadda akayi ba kawai ya tsinci kansa ne yana mai kaiwa wannan tulelen banzan naushi ne ta ko ina.
M. Salis kuwa da sauri ya dauko liffayar marakisiyya ya yane Mata jikinta domin zuwa yanzu riganta kamar na mahaukaciya gaba daya a yage yake.
Police m. Salis ya Kira suka taho wiwi bayan sun gama bata lokaci wai a hakan ma sunje ne Dan an turo musu kudin mai. KAI YAN SANDAN KASARNAN KU GYARA HALIN KU. BAZANCE DUK DAYA KUKE BA AMMA YAWANCIN KU BAKWA TSORON ALLAH AKAN NAIRA 100 SAI A KASHE RAYUKA KO SU HALAKA.YA KU MATA YAN UWA NA KUMA IYAYE SANNAN HAJIYA A WAJEN OGA, IN KINSAN MIJIN KI DAN SANDA NE KO SOJA, INA HADAKI DA ALLAH KO WANI LOKACI KI DINGA TUNA MASA GIRMAN AMANA DA HATSARIN CIN TA KIYI MASA WA'AZI DA NASIHA ME TSIMA ZUCIYA YADDA ZAIJI TSORON ALLAH YAYI AIKI BISA AMANA DA BIN DOKA.
ANA YAN DOKA SUNA KARYA DOKA KUGA YADDA SOJOJI KEYI AKAN HANYA SUYI TA KARBAN KUDIN JAMA'A, AKAN NAIRA 20 KO HAMSIN SAI A WUCE DA BOMB KO WASU MIYAGUN ABUBUWA. ALLAH KA KARA SHIRYA MANA YAN UWAN MU KA SAITA AL'AMRAN KASAR MU ME ALBARKA.
Isowar su keda wuya aka sanar dasu Wanda zasu kama nan suka fara kallon juna wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan hakan yasa babu bata lokaci m. Ahmad ya Kira yazeed(na KURUCIYAR MINAL) Yace yayi magana a aiko yara suzo su wuce da Dan iskan nan.
Ana cikin wannan gwaramar lud ya dawo a bige tilif dakinsa yazo zai shiga yaga kofar bata gama ruwa ba yace ji wato mayar nan tara min sauri tayi a daki? Tsaki taja tace au ashe a hotel nake habu sauro. Fadawa yayi yaga empty yace that's good for her ashe tana da hankali yanzu gwaramar mu daya ce. Shine kawai ta sake min kurwa da anyi wannan mun raba jaha.
Jin karan ruwa a bandaki yasa yace sweety, kin dawo ne? Cikin kashe murya sailuba tace wanka nake yace ashe kin dawo. Yatsine fuska tayi tace kar ka cemin a bige kake. Yace na bige kan uw**ki. Kawai yayi tsaki ya sake kwanciya.
Mikewa yayi da kyar Dan yunwa yake ji toh banda shiririta Wanda ya sha giya ga wata ya dauka ya Kira reception mana kawai sai ya fito Wanda yayi dai dai da lokacin Da m. Ahmad ya fito da ita daga dakin bayan ya yankasa hannun yan sojoji Dan yasan mj yazeed bazai taba bari Dan siyasar yasha ba.
Kara bude ido lud yayi Dan ya tabbatar wa kansa abinda yake gani tabbas itace dafe kai yayi yace kai jama'a yanzu maiyar nan wai sa na ganta ko ina ne? Har zai wuce yaji m. Ahmad yace marakisiyya ke da aka daura auren ki me ya kawo ki hotel? Ajiyan zuciya tayi ta sake fashewa da kuka Dan zuwa yanzu muryarta ta dena fita kwata kwata.
Karbar wayan dake hannunsa tayi ta rubuta masa komai tare da karashewa da na gode da ceto na. M. Ahmad yace toh ina ne dakin naku? Da kafada tayi masa alamun itama bata sani ba. Lud suka gani tsaye a gaban su yace sheegiyaaaa karuwar banzaaaa daama bazaaaki Sami ba AI wato da nace ki koma gida shine ke da Dan iskan saurayin naki kuka kama daki ko? Har ma kin manta dakin mijin ki.
Yana kaiwa nan yayi shiru yana maimata kalmar mijinki,mijinki? Itama dai a anata kwakwalwar haka ne domin maganar tazo musu banbarakwai. M. Ahmad ne yace Mr. Lud am sorry to say but ka fahimci maganar nan a baibai. Daga masa hannu lud yayi yace gara ni maganar ce na fahimta a baibai ba tunanina ne baibai ba.
Take m. Ahmad yaji kamar lud yasan me ke faruwa dashi domin maganar tayi daidai da rayuwar m. Ahmad din wani lieutenant ne ya fito yana kiran sunan m Ahmad yace ina yarinyar ana bukatan ganin family dinta don jin dalilin da yasa aka barta tazo hotel.
Lud ne ya kallesu kamar Wanda ba yanzu yake tambele ba ya gyara nutsuwar sa muryarsa tar cikin tsurewa ya kalli sojan yace hey! Yana mikawa officer din hannu musbah sukayi cikin harcen turanci yace ni mijin ta ne kuma yau aka daura mana aure, fita nayi Nemo Mata abubuwan da Mata ke bukata sai aka samu matsalar wuta ita kuma tana tsoron duhu. Kawai sai ta fito wai tana nemana ne.
Da taga bana nan garin komawa daki shine ta shiga wrong room. Rungumeta ta yayi Wanda gaba dayan su sanda sukaji kamar an watsa musu ruwan sanyi yanda suka wani yi vibration. Peck ya Mata a goshi yace na godewa Allah ba abinda ya same ki zo muje in miki tausa.
Baki da hanci m. Ahmad ya saka jin yadda lud yake kwantara karya Wanda da ka gani kasan bawai yana yi bane Dan yana jin tsoron sojojin, ah ah so yake a basa marakisiyya ba tare da an kaita gida ba. Kuma babu shakka bawai Dan yana tausaya Mata bane zai karbeta.
Lud kuwa yana kaiwa nan ya kama hannunta suka shige daki ya rufe kofa harda lock KYAM!
AYYA! AYYA!! TUN KAMIN NA RUBUTA NEXT PAGE NASAN ZAI BADA JUICE ME SUGAR.
KARDAI KU MANTA KU TUNKUDO MIN COMMENTS YAN UWA.TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
16th August,2020.
https://my.w.tt/
YOU ARE READING
YA JI TA MATA
Mystery / ThrillerWannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsi...